CHAPTER 14

102 7 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

*MASU MIN SHARING ƊIN WANNAN LITTAFIN  WAƳANDA NA SANI DA WAƳANDA MA BAN SANI BA UBANGIJI YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA DON ALFARMAR MUHAMMADURRASULILLAHI🤲*

banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 14

____Tsayar da Motar yay lokaci guda kuma ya kifa kansa a saman sitiyarin motar yana sauke Numfashi lokaci guda kuma idanunsa suka ciko da wata daskararriyan ƙwalla

Kasa ɗagowa yay sabida zafin da zuciyarsa ke masa hakan yasa itama ta maida hankalinta kacokan ga Saleym ɗin sabida Sauyin data gani a tareda shi lokaci guda.  Lumshe idanunta tai ta kuma beɗesu a kanshi sannan ta maida nutsuwarta ga abinda tai niyar yi tun farko wato bama Abou Hateem mouth respiration.

Jikinsa a mace ya ɗago da kansa daya mugun masa nauyi daga saman sitiyarin motar yana sauke numfashi akai-akai yama motan key sukaci gaba da tafiya batareda ya iya furta koda kalma guda ba,.

Se wajen 2:00am na dare suka shigo cikin Kaduna Direct Asibitin datake aiki ya nufa kai tsaye guri ya nema yay perking batareda ya mata magana ba, Sosai ta fahimci sauyin dake taredashi sakamakon shirun dataji yay mata tafi kowa sanin halinsa  sabida shaƙuwar dake tsakaninsu, sedai har yanzu ta kasa  gano ainihin maƙasudin canzawar nashi a lokaci guda, buɗe motar tayi ta fito tareda zagayawa saitin inda Saleym ɗin yake tace "har yanzu banace ga dalilin Sauyawar da Saleym Mahmoud Bakori yayi ba dukda cewar duk duniyar nan idan aka cire iyayen mu baka da Aminiyar data wuceni haka nima banida wanda yafika, wannan sauyawar taka na lokaci guda tasa naji ina Zargin kaina haka kuma zan iya jurar komai a Rayuwata amma banda wannan baƙon Sauyin da idanuna suka gane min a tareda kai Saleym!!"

Noor tayi maganar a matiƙar raunane tana kallon gefan kyakkyawar fuskarsa wadda kwantaccen sajensa ya ƙara masa haiba ta musamman.

Numfashi kawai yake saukewa sabida tsabar yanda zuciyarsa ke wani irin racing  ya kasa mata magana  hakan yasa ta buɗe murfin motar tareda kamo hannayensa cikin nata tanaɗan matsawa kaɗan alamar rarrashi tun kafin tayi magana yay saurin sakkowa yay hugging ɗinta very tight lokaci guda kuma ya sakin mata kuka kamar wani ƙaramin yaro, shiru tai tana sauraron yanda hawayensa ke sauka a saman doron wuyanta sosai jikinta yay wani irin sanyi wanda ta rasa dalilin faruwan hakan.

Bakajin sautin komai sena bukun zujiyarsa gamida shashsheƙan kukansa daƙyar ya iya buɗe bakinsa lips ɗinsa na wani irin rawa yace "why Noor meyasa se a gabana zakiyi hakan?  Shin kinsa yanda nakeji a game dake kuwa? Koda wasa kin taɓa saurarar zuciyar wannan saleym ɗin da kuma dalilin dayasa kullum zuciyarsa ke bugawa samada so ɗari da saba'in a Rana?"

Yay mtaTambayar yana ƙara ƙanƙameta a jikinsa kamar wanda ake ƙoƙarin ƙwace masa ita,  girgiza masa kai tayi cikin irin yanayi irin na wanda keson tabbatar da abinda yakeson tabbatarwa.

Wani marayan kuka ya sake sakar mata a wuyanta hucin dake fitowa daga bakinsa yana sauka a saman fatar wuyanta, hkanne ya haifar mata da wani baƙon yanayi wanda yay tasiri sosai a gangar jikinta harya haifar mata tasowar tsigar jikinta.

A zahiri so take ta janye jikinta daga nasa amma sam yaƙi bata damar hakan yace "Noor ni kaina bansan ainihin tartibin yanda nakeji akanki ba amma tabbas zuciyata tana azalzalata akan duk wani motsi naki, har yanzu ban gama sanin ma'anar abinda kebin jijiyoyin jini na akanki ba amma inaso ki sani ko wace daƙiƙa ta rayuwata yana ta'allake ne da son ƙara samun kusanci dake Noor!!"

Gabanta ne yay wata irin bugawa a lokacin dataji bugun zuciyarsa yana ƙaruwa fiyeda na farko tabbas tasan anything bad can happen to him at this time  muddin bata lallaɓashi ba,  bataso ta Rasashi a ko kaɗan haka kuma bataso Ciwonsa ya tashi a sanadinta  Saleym yanada kima a idanunta data zarta zaton duk wani me zato, bayan hkaa kuma sonda take masa na daban ne tayanda harshenta bashida isassun kalmomin daza tayi

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now