CHAPTER 12

114 6 0
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

*MASU MIN SHARING ƊIN WANNAN LITTAFIN WAƳANDA NA SANI DA WAƳANDA MA BAN SANI BA UBANGIJI YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA DON ALFARMAR MUHAMMADURRASULILLAH🤲 NGDE SOSAI 👏*

Banyi Editing ba

Page: 12

____Wani irin kuka takeyi wanda sanadinsa ya haifar mata da wani irin Rawar jiki, ƙara ƙanƙameshi tayi tamkar zata koma cikinsa ba tareda ta iya magana ba. Gabaki ɗaya ta gama sarewa da lamarin wanda da ace tasan haɗarin dake tattare da wannan binkicen nata to da tun farko bata farashi ba.

A hankali yake saurara bugun zuciyarta wanda ya ninka nasa kusan so goma, a hankali yaji jikinsa yay masa wani irin sanyi wanda hakan yay tasiri a gangar jikinsa wajen saukar masa da tsananin tausayinta wanda kaso tamanin na zuciyarsa yaywa hakan mubaya'a.

Hannunsa yasa a saitin kanta ba tareda ya iya cewa komai ba illa kafe ƙofar dayay da dara-daran idanunsa waƴanda suke ɗauke da abubuwa da suka zarta fahimtarsa, gabaki ɗaya ji yake kansa duk ya gama kullewa cikin yanayi na rashin sanin makama da abinyi ya zarota daga jikinsa tareda riƙe kafaɗunta sabida yanda yaga dukta rikice yace "ke kwarkwar ɗin likita ki dakatar da wannan shirman kukan naki muyi amfani da tunanin mu wajen samun mafita...... Hannunsa ta damƙe cikin nata tana ƙoƙarin komawa jikinsa yay saurin dakatar da ita, ganin bata cikin haiyacinta yasashi saurin girgizata a lokacin da aka turo ƙofar, da wani irin sauri ya bizgeta suka lafe a bayan wani baƙin glass wanda ya sensor ɗin wutar ɗakin yasa ya ɗauke gabaɗaya sabida kyaucewar da sukai daga saitin ƙwan fitilar.

Buɗe baki tayi da nufin ta ƙwalla ƙara yay saurin toshe mata baki da hannunsa wanda babu ciwo a jiki, rintse idanunsa yay gam sabida Azabar da hannunsa mai cowon ke mishi gabaɗayan nauyinta ya ta'allaka ne akan hannun don haka wata irin zufar Azaba ta fara tsatsafo masa.

Wasu kita-kitan ƙarti ne majiya ƙarfi suka shigo ɗakin nan take hasken ƙwan fitilar ya sake gauraye ɗakin, dube dube suka farayi cikin hanzari amma kuma basuga komai ba har zun juya zasu fita Noor ta dunguri glass ɗin dake gefansu nan take kuwa ya faɗi ƙasa ya tarwatse, a wannan lokacin daga ita har shi babu wanda be razana ba a lokacin da ƙartin suka nufi gurin gadan-gadan don su duba suka abinda ya haifar da fashewar Glass ɗin.

Suman tsaye Noor tai sabida tsabar Razana a lokacin da ɗaya yakai hannu ze buɗe labulan, yana shirin lega bayan glass ɗin da suke a ɓoye ne sukaji muryar Dr. Bashir Bala cikin yanayi na kyaushi yace "maza ku fito ba'a nan akafi buƙatarƙu ba, ko wace ko wace ƙofar ku datseta karku bar kowa ya shigo kuma karkubar kowa ya fita, zan kira wayar Securitys ɗin dake tsaron get ɗin farko dana ƙarshar akan kar subar kowa ya fita har se mun gaba waƴanda sukai mana kutse tukuna."

Juyawa sukai da suri don su cika Umarni cikin yanayi irin na zallar biyayya ga Dr. Bashir ɗin. Wata nannauyar Ajiyar zuciya Abou Hateem ya saki lokaci guda kuma ya zare Noor daga jikinsa yana buga kumatunta kaɗan, nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke har seda abin yaso bashi tsoro

Kallon tsaf ya shiga yi mata sabida tsabar yanda yaga tana neman fita daga haiyacinta safa da marwa ya farayi a ɗakin maganganun mutumin ɗazu suna dawo masa a tsakiyar kansa na a rufe ko wace ƙofa kar abar wani ya fita.

Idonsa ne ya sauka akan Babban Window ɗin dake ɗakin don haka ya isa gurin cikin hanzari yasa hannunsa da ƙarfin tsiya ya ɓalle net ɗin dake jiki sannan ta fara ƙoƙarin cire slide glass ɗin dake jiki.

Sosai hannunsa ke zubar da jini wanda hakan ya ƙara ɗagawa Noor hankali, ƙasan farar rigar dake jikinta tasa hannu ta yaga ba tareda ya lura da ita ba se kawai jin saukar hannunta yay a saman nasa tana ƙoƙarin ɗaure masa ciwon, a sanyaye ya ɗaga gajiyayyun idanunsa ya saukesu akan kyakkyawar fuskarsa wadda hawaye suka gama wankewa. Lumshe idanunsa yay da sauri tareda da barin kallonta yaci gabada ƙoƙarin ɓalle glass ɗin, ganin dayay wankin hula na ƙoƙarin kaishi ga dare ne yasa ya daki glass ɗin da lafiyayyen hannunsa tayanda bazeyi ƙara ba ya fashe.

MURADIN RAI! (complete) Où les histoires vivent. Découvrez maintenant