MURADIN RAI CHAPTER 11

96 6 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba

Page: 11

______Wani irin bugawa ƙirjinsa keyi cikin yanayi irin na wanda ke neman mafita ya nufi bayan wani dogon glass ya lafe a gurin yana  Karanto duk addu'ar datazo mashi a ransa,  rintse idanunsa yay da ƙarfi a lokacin dayaji takun takalman mutane sama da biyar wanda ya gama yanke ƙauna akan shi suka fito nema.

Securitys ne suka shigo ɗakin a ƙarƙashin jagorancin Dr. Arfat   Feruz, nuni ya farari musu da gadon farko sannan yace "daga kan wancen gadon zuwa kan wannan yaron dake dabda gado na ƙarshe zaku kwashe ku mai dasu zuwa wancan ɗakin wanda ke maƙotaka da office ɗin Dr. Bashir Bala, lallai kuyi aikin cikin hanzari sam karkubar koda ƙaramar alamace dazata sa ƴan leqen Asirin da sukai mana kutse su samu wata hujja akanmu.

Da sauri suka amsa da "ok sir" sannan suka fara tura gadajen suna fita dasu  zuwa waje  shidai Abou Hateem har ya wannan lokacin yana maƙale a jikin glass ɗin dayay masa shamaki dasu, a lokacin dayaga ana fita da yaran zuwa wani ɗakin daban idan hankalinsa yay dubu to babu wanda be digunzuma ba, don haka ya ƙudurtawa kansa cewar daya bari a gaban idonsa ɗansa ya shiga Halaka gwara ya fito kawai a yita ta ƙare.

Tas suka gama ficewa da yaran ya rage daga Dr. Feruz sai Hateem wanda ke kwance samɓal a saman gadon  Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfin gaske lokaci guda kuma yakai hannunsa saman goshin Hateem wanda keta fitar da gumi, na'urar Oxcigyn ɗin dake lilo a jikin gadon ya ɗauka tareda saƙala masa ita bisa hancinsa, na'urar dake gefan gadon wadda ke kamada Tv ce ta fara ƙara  Alamar numfashin dake jikin Hateem ɗin yana gabda ya ɗauke gabaɗaya.  Yakai hannu kenan ze taɓa Abou Hateem ya shaƙeshi cikin yanayin na zallar fusata gamida wutar ɓacin rai.

Gabaɗaya ya manta da ciwon dake jikin hannunsa har seda yaga jini na zuba daga jikinsa zuwa kan farin Uniform ɗin dake jikin Dr. Feruz ɗin, kakari ya fara cikin wani irin yanayi na fitar haiyaci ya fuzge hannunsa daga wuyansa tareda zubewa ƙasa yana maida numfashi.

Nanfa aka fara kallon-kallo a tsakaninsu kasancewar akwai wannan kayan a jikin Abou Hateem ne yasa Dr. Feruz bai samu zarafin ganin Fuskarsa ba yace "waye kai kodai kana ɗaya daga cikin ƴan leƙen Asirin da sukai mana kutse ne sannan  me namaka kake ƙoƙarin kasheni?" 

Dr. Arfat Feruz ya jefawa Abou Hateem tambayoyin duk a lokaci guda

Kobi takansa Abou Hateem beyi ba balle ya samu zarafin Amsa masa tambayoyin dayake jifansa dasu waƴanda yakema wani  kallo na daban  a tasa fahimtar,  jefar da akwatin dake hannunsa yayi a lokacin dayaga  numfashin hateem dake fita ta cikin Oxcigyn ɗin yana janyewa gabaɗaya, da wani irin sauri ya nufi gadon wanda be taɓa zaton yana dashi ba ya fara  jijjigashi cikin yanayi irin na wanda ke cikin zallar tashin hankali mara misali.

duk dauriya irinta Abou Hateem a wannan lokacin seda ya gaza sabida rigar tashin hankali. dake ƙoƙarin maye gangar jikinsa, zubewa yay a ƙasa bisa gwiwoyinsa ya fashe da wani irin kuka wanda ke baiyana irin ciwukan da rayuwarsa take ɗauke dasu.

Kafeshi da dara-daran idanunsa Dr. Feruz yayi kansa a matiƙar ɗaure a gamedashi idanunsa ya sauke akan akwatim dake  yashe a ƙasa lokaci guda kuma ya maida kallonsa ga Abou Hateem wanda keta gurzar kuka kamar ƙaramin yaro  yace " ada ina tantama akanka tareda tararradin kai wanene a raina amma kuma dana kalli waccen akwatin na fahimci cewar kaine wannan ɗan leƙen Asirin daya shigo wannan ma'aikatar har ya samu nasarar sace abu mafi daraja a kasuwar duniya,  mene alaƙarka da wannan yaron da har kake zubar da hawaye akansa irin haka?"

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now