MURADIN RAI chapter 3

160 13 0
                                    

🧊🧊🧊 🧊🧊🧊
🧊🧊🧊
*MURADIN RAI*
*(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : CHUBAƊO (the chosen one)✍️_*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page:3

____✍️A firgice ta farka duk ta haɗa uban Gumi  tamkar wadda aka sheqawa ruwa a jikinta, sosai ƙirjinta ke wani irin beating Kamar xuciyarta zata tsaga qirjin ta fito, babu abinda take saukewa se numfashi akai-akai Tamkar wadda ta fafata tsere da lafiyayyen  ingarman doki maji ƙarfi.

Dafe kanta tayi da dika hannayenta biyu  mafarkin datai yana dawo mata  tsaf  a rsakiyar kanta,   tamkar a lokacin abin ke faruwa, rintse idanunta tayi daƙarfin gaske kanta na wani irin bugawa tamkar wanda ke shirin farai mata ciwo, Jiki a saliɓe ta buɗe idanunta sannan ta sakko da dogayen ƙafafunta ƙasa daga saman makeken gadon, tareda sanya ƙafarta cikin wani lallausan takalmi irin na mutanan yankik  Ƙasar Toukey.

bata dire ko ina ba Se a gaban  madedaicin Firinjin dake ɗakin tsayawa taiyi cak tareda folding hannunta bisa ƙirjinta, ta jima a tsaye  tana aikin fafutukar son gano wani abu ƙwaƙƙwara akan mafarkin da take yawanyi amma sam abin ya faskara, Ajiyar zuciya ta sauke me ɗan ƙarfi tareda firzar da iska daga bakinta me cikeda huci, sannan ta buɗe firinjin tareda ɗauko ruwa me ɗan iskan  sanyin  ta kafa a bakinta.

Seda tasha sosai sannan ta sauke goran ruwan tana maida numfashi, ta jima a tsaye kamar bazata motsa ba sannan ta fara zagaye dakin cikin yanayi irina Safa da Marwa tamkar wadda ke cikin gagarumin zullumi, tabbas ya zama wajibi a gareta ta nemawa kanta mafita akan wannan yawan mafarkin da takeyi, "shin meyasa ta kasa manta Fuskar wannan yaron har izuwa wannan lokacin ?."  Noor ta jefawa kanta wannan tambayar da har yau ta gaza samun Amsarta.

Ajiyar zuciya ta sauke me nauyin gaske a karo na barkatai,  Abubuwan da suka gabata suna dawo mata tamkar a lokacin abubuwan ke faruwa a kan idanunta, har yanzu Fuskar yaron ce takeyi mata yawo a tsakiyar kwayar idanunta, abu ɗaya take iya tunawa shine  lokacin da yaron ya  riƙe gefan rigarta cikin yanayi irin na wanda ke tsakanin rayuwa da  mutuwa, gam ya riƙe rigar da hannayensa kamar his life depends on ya riƙe rigan dake jikin nata karya saki, cikin wani irin muryar mai fuzgar zuciya  yace, " pls help me miss I don't want to die!,  I'm the only son my mother have,  pls  try to save my life Don Alla...."   duk yanda yaso ya ƙarasa maganar kasawa yayi sabida yanda numfashinsa ke sarƙewa yana barazanar ɗaukewa gabaɗaya, cikin wani irin yanayi wanda yafi kamada na fitar Haiyaci Noor ta fara ƙoƙarin girgizashi.

idan hankalinta yay dubu a wannan lokacin babu wanda bai tashi ba, haka kuma duk yanda taso ta ceto Rayuwarsa  abin yaƙi yuwuwa. Tanaji tana gani ubangiji ya saukar da ikonsa a kanshi Rai  yay Halinsa,  yaron ya mutu batareda ta iyayin komai ba, haƙiƙa al'amarin Ubangiji seshi, haka kuma idan ya zartar da hukuncinsa akan mutum babu yadda ya iya dole ne musulmi ya karɓi hakan kuma yayi godiya, wannan shine cikar imani  idan wa'adi yayi babu makawa sai rai ya ɗanɗani azabar mutuwa.  A lokacin da labarin Mutuwar yaron ta isa ga Mahaifiyarsa tayi kuka tamkar bazata dena ba,  amma kuma daga bisani haka tayi haƙuri da jarrabawar da Allah yayi mata tayi tawakkali bisa mutuwar ɗanta ƙwaya ɗaya tilo a duniya.

hannu Noor tasa ta share hawayen daya zubo mata na tsananin tausayin yaron da kuma Mahaifiyarsa batareda ta shiryawa hakan ba, iska ta furzar me ƙarfin gaske tareda   ƙudurtawa zuciyarta cewar lallai seta ganowa kanta dalilin Mutuwar Yusuf. Sabida a lokacin da aka kawoshi Asbitin itace ke kula dashi, "to amma menene maƙasudin rikicewar jikinsa haka?" tayiwa kanta wannan tambayar a zuciyarta

Hawayen dake kwaranyowa daga idanunta tasa hannu ta ƙara sharewa, sosai takejin yaron a kusa da zuciyarta sabida yanda yake da shiga Rai, wasu lokutan har mamaki mahaifiyarsa keyi yanda Yusuf ya ke sakin jiki da Dr. Noor ɗin, a iya Rayuwarta tasan ɗanta miskili ne,  kuma sam baya sakin jiki da kowa musamman ma malaman Asbiti, amma kuma se gashi a ɗan taki kaɗan shaƙuwa mara misali ta samu nasarar wanzuwa a tsakaninsu.

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now