CHAPTER 15

108 6 0
                                    

🧊🧊🧊    🧊🧊🧊
          🧊🧊🧊
   *MURADIN RAI*
   *(Abou hateem)*
🧊🧊🧊🧊🧊🧊

*_WRITING BY : ZAINAB MHMD CHUBAƊO✍️_*

*MASU MIN SHARING ƊIN WANNAN LITTAFIN  WAƳANDA NA SANI DA WAƳANDA MA BAN SANI BA UBANGIJI YA BIYAKU DA GIDAN ALJANNA DON ALFARMAR MUHAMMADURRASULILLAHI🤲*

Banyi Editing ba🙅‍♀️

Page: 15

____Cikin fushi da ɓacin rai Mom ta nunata da yatsa tace "daga gidan ubanwa kike at this time? dake nake mgana don kutumar ubanki!!"  mom tai maganar a matiƙar harziƙe

Kuka ta fashe  dashi  sakamakon ɓarin makauniyar da mom tai mata wanda yasa taga wasu jajayen taurari suna mata shawagi a tsakiyar kanta,

"bazaki bani Amsa ba sekinja abinda zan miki illa a nan gurin kome!!?"  mom ta sake daka mata wata sabuwar tsawar data zarta na farko.

"kafin ki illata ta ni nan zan ɗauki mataki akan Aisha!!!" Dadyn Noor daya shigo falon ya faɗi hakan yayinda ya janyo Noor ɗin jikinsa yana bin Mom da wani irin kallo wanda yafi kamada na zallar ɓacin rai.

Harɗe hannunta Mom tai bisa ƙirjinta a hankali ta fara takowa daga inda take a tsaye zuwa gaban Dad ɗin sannan tace "Ada Nayi zaton cewa wani Abun nayiwa Ubangiji shiyasa ya haɗani dakai a matsayin Mijin dazan zauna dashi don kawai laifin danayi masa ya zame min kaffara, Amma kuma daga baya sena fahimci cewar Auren ka bashida maraba da Auren Ƙaddara!!"     mom ta faɗi hakan tana kallon tsakiyar idanun Dad cikeda fishin dayaci ƙaniyar na farko.

Ba ƙaramar Kaduwa Dad yayi da kalaman Mom ba don haka ma beyi gigin sake firta  wata kalma ba sabida ya lura muddin ya tanka mata tofa Allura ce zata tono Garma shiyasa ya tsuke bakinsa yay shiru yana binta da idi.

Juyawa Mom tai fuuuuu zata bar falon harta kai jikin ƙofar se kuma ta dawo da baya tana binsa da wani fisataccen kallo wanda yasa yaji ya muzanta, kallonta ta mayar ga Noor wadda ke rizgar kuka  sannan ta saki wani ƙayataccen murmushi wanda ke baiyana zafinda zuciyar ta keyi   tace " ke kuma ki jira lokaci tabbas wata Rana sekin yi  dana sanin Fitowa daga tsatson wannan mutumin da kikewa kallo a matsayin mutum mafi soyuwa  a Zuci......."Aisha!!!"    Dad ya katseta ta hanyar kiran sunan ta cikin wata mahaukaciyar tsawar data sa falon ya amsa.

Murmushi kawai mom ta sakar masa sannan ta juya tabar falon cikin wani irin sauri wanda ke ɗauke da zallar ɓacin ran dake cin zuciyar ta.

A wannan lokacin abubuwa da dama ne suka cika zuciyar Noor musamman dataji kalaman kaushin da Mom ke jifan Dad dasu a gabanta ba tareda shakka ba, tunda take a Rayuwar ta bata taɓa ji Mom ɗinta tayi musayar yawu da Dady ba duk irin ɓacin da ranta zeyi kuwa "amma meyasa tayi dashi a yau?"   wani ɓangare na zuciyarta ya gaya mata hakan.

Ɗagowa tai da kumburarriyar fuskarta wadda ke ɗauke da shatin yatsun mom zatayi magana yay sauri dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu yace "not now daughter kibari mu samu lokacin daya dace tukunna zan sanar dake komai."

Be jira cewar ta ba ya juya yabar falon jikinsa a mugun sanyaye.

Koda yabar ɓangaren Noor Direct falon Mom ya nufa kansa tsaye zuciyarsa na rawa tamkar ba tasa ba, cikin sauran ƙarfin daya rage masa ya ɗag hannunsa ya ɗora a saman handle ɗin ƙofar ya shiga falon da Sallama ɗauke a samn Harshen,  turu yayi sabida ganin bata falon  dama can beyi tsammanin ganin ta a nan ɗin ba don haka ya haura upstairs don yasan tana can

Tun kafin yakai ga shiga ɗakin yakejin saukin shashsheƙar kukanta jikinsa a mugun saluɓe ya tura ƙofar, tsayawa Dad yay yanajin zuciyarsa na masa wani irin Zafi wanda hakan ke faruwa a sanadin kukan datakeyi

MURADIN RAI! (complete) Where stories live. Discover now