Auren sirri 01

1.6K 47 2
                                    

🔐 Auren sirri 🔐 1⃣

Mamy ce ta shigo dakin Ayisha ta tayar da ita zuwa skul kamar yanda ta saba kullum,tana nade saman gado tana baccin ta cikin kwanciyar hankali.
Mamy ta girgiza kai hade dayin murmushi ta zauna gefen gadon Ayisha tana shafa fuskar ta
a hankali kuma tana sosa mata kafa,cikin bacci ayisha taji kamar ana mata susa hakan ya mata dadi shiyasa ta kara rungume karamin pillow dake kusa da ita me yanayin Heart,ganin haka yasa mamy ta dan bubbuga bayan ta gami da kiran sunan ta Ayisha...Ayisha ki tashi mana ki shirya school ko kina so ki makara ne? Ayisha tadan kunburo baki cikin shagwaba da alamun bacci tace mamy please ba yanzu ba se anjima idan na tashi bacci na shirya inje,mamy ta zaro ido kadan gami da cewa lallai Ayisha kina so kiyi missing test da zakui kenan? Cikin sauri Ayisha ta mike gami da cewa OMG! Lokaci daya tana mai aza hannu aka da sauri kuma ta zura santala santalan kafafun ta kasa ta zura silifas ta shige toilet.
Mamy tai murmushi gami da mikewa a ranta tana jin tsananin kaunar diyar ta,kai tsaye dinning ta wuce dan duba ma Ayisha abinda zata ci kasancewar tasan bata son abinci mai nauyi musanman lokutan safiya. Batafi mintuna talatin ba ta jiyo tashin kamshin Ayisha ta daga kanta sama ta zuba mata ido tamkar bata taba ganin ta ba har Ayisha ta karaso gun mamy,hure mata ido tayi mamy tai ajiyar zucia gami da murmushi tace an shirya ko swthrt? Ayisha tace yes mamy taja kujera ta zauna gami da riko hannun mamyn tace gud mornin mamy? mornin swthrt,how was ur nyt? Ayisha tace fine mamy,taci gaba da cewa mamy kiman addu'a Allah ya bani sa'a kan test dinnan,mamy tai murmushi gami da cewa ameen swthrt gami da bude food flask zata zuba ma Ayisha breakfast ganin haka Ayisha ta bata fuska ta kauda kai,mamy ta debo mash potatoe takai bakin Ayisha gami da cewa oya open ur mouth swthrt,cikin shagwaba ta bude baki ta zuba mata,kusan minti biyar mamy na ciyar da ayisha kafin ta mike gami da cewa mamy yau kina so cikina ya fashe ko? mamy tai daria gami da mikewa ta kama hannun ayisha sukai waje gun parkin motoci,mamy kejan motar har suka karasa skul dinsu ayisha oxford university dake birnin na England,ayisha ta zagayo ta side din mamy gami dayi mata peck tace i will miss u mamy,mamy tai murmushi tace i will miss you too swthrt,ayisha ta juya zuwa class,mamy kuma taja motar ta cikin farin ciki tayi wajen aikin ta.

Mrs sS ❤️ ✨

AUREN SIRRIWhere stories live. Discover now