THRILLER

421 38 8
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.

*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.* 

*It's all about:*#Masturbate,#Porn,#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lust.

*THRILLER*


      •••Kallon mahaifinsa yake a bit scared da idanunsa da suke cikin fari tar ɗin eye glasses da suke ƙarawa idanunsa ƙarfin gani yace "Dad! She's my girlfriend.. Ita nake son aure,please Dad i'm begging u ba na son rasa ta,kai wani abu akai Dad i'm matured enough,zan iya riƙe mata ta,amma Dad bazan iya riƙe kaina ba anymore.. Aure nake so.." Wani kallo mahaifin nasa ke masa yace "WAZEER u're not,har yanzu kai yaro ne,baka kai ka iya riƙe mace ba,baka kai ka riƙe gida ba,and the worst part of it har yanzu u're dependant.." Numfashi WAZEER ke saukewa da sauri² yace "Dad i'm not dependant,zan iya riƙe mata ta" Dad yace "baza ka iya ba,ka tashi ka bani guri kada na ɓata maka rai,u're still young baka wuce kaima a raineka ba" Wazeer yace "Dad i'm not a kid anymore,kai min aure ka gani idan ban bawa Mata ta ciki ta haihu ba,ni aure nake so kai min,i'm tired of everything,na gaji da karatu and whatever da kake sawa ina yi,aure nake so.." A fusace Dad yai masa tsawa "WAZEER! Enough da wannan shirmen da kake faɗa min,i'm ur father ka san irin maganar da za ka furta a gaba na,na ce ka tashi ka bani guri kafin na saɓa maka.. Bazan maka aure ba yanzu,saboda baka kai ka iya riƙe gida ba,so get out of my sight" a fusace ya miƙe heading to entrance ya fice da gidan zuciyarsa na wani irin ƙuna.

*

   "Did u know who WAZEER is? Anya Safwa kin ma san wane ne mahaifinsa kuwa? Kin san me kike shirin aikatawa?" Radhiya ta faɗa looking at Safwa dake zaune in front of her,a hankali Safwa ta girgiza mata kai tana taɓe baki tace "i don't care whom son is,kawai ni na amincewa Alh Muhammad Aliyu Waziri,ni na masa izini ya turo akayi maganar aurenmu,wallahi na gaji da tarin samarin nan Radhiya,duk da kike ganinsu taron tsintsiya babu shara ne,duk ciki dai kin gansu ƴaƴan manya ne,samari masu jini a jika,amma shi kaɗai yazo min da maganar aure.. So i just sit and think kawai shi ɗin ne dai² da ni,kawai na masa izini ya aiko akayi maganar aurenmu,yanzu ba ga shi nan zan yi aure ba in the next couple days?" Wani irin mahaukacin dariya Radhiya ta fashe da shi,kallon u're crazy take yiwa Safwa,har hakan yasa Safwa fara zargin kanta da maganar da tayi,a hankali kamar za ta yi kuka tace "stop laughing at me Radhiya.. Kina ji ina miki magana mai muhimmanci za ki sa ni gaba kina dariya,idan akwai wani abu ki sanar min please,kafin nayi gaggawa gara na sani.." Radhiya na girgiza mata kai tace "u're extremely late Safwa.. Lokaci ya ƙure miki,kin yi kuskure da kika yarda za ki auri Alh Muhammad Aliyu Waziri,domin kuwa he's a biological father of WAZEER.. Let me explain da kyau,ALIYOS! ALEY!! Ur boyfriend,shi nake nufin ɗan Alh Muhammad Aliyu Waziri ne na cikinsa,and shi kaɗai ya haifa.." Wani dum Safwa taji tun daga cikin kunnenta har ƙwaƙwalwar kanta,kamar dodon kunnenta bai jikinta ta daina jin komai,idanunta sukai wani dishi² ganinta ya ragu saboda tsabar ruɗewan da tayi,tambayar kanta ta fara yi "ALEY! ALIYOS! What does that mean? Alh Muhammad Aliyu Waziri shi ne mahaifinsa? Biological father!? How?"

*

     Cards ɗin yake kallo idanunsa suna sake kaɗawa jajir,jijiyoyin jikinshi da na kansa banda wani irin harbawa babu abunda suke,a guje kamar wanda aka koro ya shigo yana ƙwala kiran "Dad! Dad!! Dad!!! Where are u,come out.." Yayi maganar cikin ɗagawar sauti,Dad dake waya cikin farin ciki yace "sorry! I'll get back to u.. Ok! Bye" dai² nan Wazeer ya banko ƙofar bedroom ɗin tare da watso tarin invitation cards ɗin hannunsa suka watse a saman floor,so pissed off yana yiwa Dad wani kallo yace "what am i seeing Dad? What am i looking? My girlfriend and u? Dad budurwata da nazo nace ka aura min kaje za ka aure? What a shame.. Ohh! Wow! My Dad zai auri budurwata?" Sai kuma ya fara ɓaɓɓaka dariya irin wanda tunda ya tashi bai taɓa yi ba,yana nuna kanshi yace "Dad! Aure da budurwata? This is shameful.. Abun kunya ne Dad,kace min mafarki nake,kace min ba gaskiya idanuna suke gani ba.." Yai maganar da amo me girma kuma cikin tsawar da sai da gidan ya amsa amon muryarshi,Dad ya kalli tarin IV ɗin da ya zubar ƙasa kafin ya ɗaga kanshi ya kalli Wazeer dake wani irin huci kamar mayunwacin zaki,ɗauke kanshi yayi tare da juyawa zai bar gurin,da sauri Wazeer dake ta kallon reaction ɗinsa yace "so is that all true? Da gaske ne kenan abunda na gani?" Dad ya juyo a ɗan fusace yace "Wazeer!" Da ihu shima yace "don't call my name,just explain it to me,nace da gaske ne?" Dad bai san sanda bakinsa ya suɓuce ya furta "yeah! It's true" clapping hannayensa Wazeer ya shiga yi,yayi baya² yana sake kallon Dad daga inda yake,a hankali ya zare glasses ɗin idonsa yana kuma kallon Dad,yanda yai da idanuwa za ka rantse da bai ganinsa da kyau glass ɗin ya tare masa wani abu yace "wow! Dad and his son's girlfriend are getting married,i'm happy for u,Allah ya bada zaman lafiya.." Daga haka ya jefi Dad da wani kallo kafin ya juya ya bar gurin da sauri..

*

    Dafa kafaɗarta tayi a hankali idanunta sun yi jajir sun kumbura da raunanniyar sanyayyar muryarta tace "take heart MUNIBA! Kullu nafsin zha'iƙatul maut.. Dukanmu nan jiranta muke,yanda muka zo da ɗai² haka za mu koma,daga Allah muke kuma gareshi za mu koma kin san haka.. Allah yaiwa Abuu-Turab rasuwa,ya tafi inda bazai sake dawowa ba,a yanzu addu'ah yafi buƙata daga garemu baki ɗaya,Allah ya kai rahama kabarinsa,ya yafe masa laifukansa,ya haskaka makwancinsa.." A hankali idanunta na tsiyayar da hawaye masu zafi ta gyaɗa kanta,wani irin zafi take ji yana taso mata irin na rashin masoyi,zafin rashin abunda zuciyarka take so take muradin kasancewa da shi tsayin rayuwa,muryarta a dashe bai fita da kyau hawaye na ci gaba da sauka daga cikin kwarmin idanunta ta furta "ameen Mama" occupants ɗin gurin duka kallonta suke da tausayawa,a hankali mutane suke tai masa addu'ah,Muniba dake kuka mara sauti tana amsawa da ameen²,Mama ta juya ta kalli ɗayar budurwar da kanta ke ƙasa tana kuka tace "BANIYNAH! Ba kuka za ku masa ba,haƙuri za muyi saboda dukanmu nan muma wata rana na haka ne,Allah yasa yaje a sa'a,halayensa na gari su bishi" Muniba ta kasa daina kuka,ta kuma kasa mantawa da fuskarsa me cike da fara'a,a ko da yaushe gizo yake mata a idanu,ba iya bacci ba hatta a ido biyu sai ta dunga ganinsa yana zuwar mata,idan ta kalli fuskar mutane sai ya dunga rikiɗewa yana koma mata sak Abuu-Turab ɗinta,masoyinta da takewa wani irin zazzafan so,ashe ba me tsayin rayuwa bane,ashe tafiya zai ya barta. A hankali tana lumshe idanu ta furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajirniiy fii musibatiiy wa'akufniiy khairan minha.." Daga lokacin da saƙon mutuwarsa ya risketa zuwa yanzu ta maimaita addu'ar nan bata san adadi ba,tabbas addu'ah makamin mumini,in banda haka mutuwar nan da ya yi sanadiyyar da a yanzu sai dai ace wani zancen ake ba wannan ba,mutuwar ya girgiza zuciyarta,ya jijjiga ji da ganinta,ta kaɗu iya kaɗuwa,ta tsorata da lamarin duniya,imani ya ƙara shigarta,ta sake yarda Allah shi ke da ikon tasarrufi da komai,tabbas mutuwa gaskiya ce,domin kuwa ta gani kuma ta shaida,lallai ɗan Adam ba a bakin komai yake ba,yanzu za ku dunga hira da dariya,anjima ace babu wane. Ta yi kuka da zuciyarta,ta yi da idanunta,duk wanda ya kalleta daga ranar jumu'ah zuwa yau da akai sadakar 3 zai san lallai mutuwar nan ya shigeta fiye da tunani,kou mahaifiyar Abuu-Turab da ƴan uwansa basu kaita shiga tashin hankalin rashinsa ba,a hankali idanunta suka lumshe ta zame tare da kwantar da kanta saman cinyar Baniynah dake kusa da ita tana kuka,bakinta har sannan na motsawa tana tasbihi tare da tsarkake Ubangiji (SWT)..

    

       '''#Wannan shi ake kira ana bikin duniya.. Yayin da wasu ke farin ciki,da yawa wasu lokacin suke kuka da baƙin cikin rashin wani makusancinsu.. Shin yaya wannan al'amari yake ne? Anya Dad bai so kanshi ba? Me zai sa ya aure budurwar ɗansa? Budurwar zuciya? Son kai? Ko kuwa son zuciya? Waye Abuu-Turab da ya rasu? Mene ne alaƙar dake tsakaninsa da Muniba? Miji ko kuma saurayin da take tsananin so? Me Safwa ta aikata haka? Shin da can bata san WAZEER ɗan Alh Muhammad Aliyu Waziri bane har sai da ƙawarta ta sanar mata? Data sani wane mataki za ta ɗauka a yanzu? Just follow this fairy tale of love,jealousy and ultimate betrayal that leads someone to the lost end.. For group request chat me up https://wa.me/+2348165726609'''



#Allah ka gafartawa iyayenmu!
#Follow
#Comment
#Vote
#Share
#WATTPAD:@REAL-SMASHER
#AREWABOOKS:@REALSMASHER
#THREAD:@ASLISMASHER
#Whatsapp:@https://wa.me/+2348165726609
#ASLI-SMASHER.

WAZEER!Where stories live. Discover now