New decision

79 10 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..*


                               04

#New decision

                   Zazzaro idanunta Hoor tayi tana dafe ƙirji tace "na shiga uku.. Hamood please don't do this to me.. Ka tsaya ka bani yarona" wani matsiyacin kallo ya sakar mata ya rufe motar ya tayar zai tafi,da gudu Hoor ta isa gefen da Abuu Turab yake yana kallonta idanunsa na ciccikowa da ƙwalla ya kasa magana,kana kallonsa za ka san ba ya son tafiya ko'ina tare da mahaifinsa,amma kuma bazai iya fitowa ya faɗa ba,tsoron yai magana yake a gaban Hamood,bai so yai masa faɗa yai masa irin ihun da yake yiwa Mimi,Hoor ta buɗe motar hawaye na zuba idonta tace "Hamood please ka tsaya ka bani yarona.. Ina za ka kaishi? I've my right over him,zan iya riƙeshi na bashi tarbiyya a matsayin mahaifiyarsa,kada kace za ka rabani da ɗana by force" ƙoƙarin jan motar ya dunga yi,ita kuma ta riƙe murfin motar tana son ɗaukan ɗanta,a zuciye yace "Hooriyah get out of my way,kada kija nabi ta kanki na wuce" cikin ihun itama tace "kabi ta kan nawa ka wuce Hamood,shi ne zan san ka tsaneni ba ka son sake ganina,ka kasheni kawai ka huta.. Ai babu me maka komai tunda ku kuke da garin Kano,ba taƙamarka kai jinin sarauta ba? Ka kasheni nace maka,amma wallahi babu inda za kaje min da yaro.. Saboda selfishness irin naka na rasa ƴata 6 days yau,sannan yanzu kazo za ka rabani da wanda nake gani naji sanyi.. Shin kai kaɗai ka rasa ƴarka ne? Ai nima ƴata ce kamar yanda take taka" yanda take kuka haka Abuu Turab yake kuka yana kallonta,a hankali cikin tsoro ya kalli Hamood yace "Dad ni a gurin Mimi zan zauna,ba zan bika ba ka ƙyaleni naje gurinta,she's crying because of me" gigitaccen tsawa Hamood yai masa cikin ihu yace "Wazeer! Keep ur mouth shut kafin na mammareka.. Baza ka zauna gurinta ba,yau ɗin nan za mu tafi ni da kai,bazan taɓa barinka a gurinta ba,muguwa ce ita,tana da son kanta,me kisan kai ce,mutane take kashewa,idan na barka a gurinta za ta kasheka kamar yanda ta kashe Lil Mysha.." Abuu Turab na kuka yace "Dad ba ta kashe mutane,ni na fi son Mimi,a gurinta zan zauna" cikin faɗa idanun Hamood sun rufe tsabar ɓacin rai ya fizgi motar,sauran kaɗan ya taka mata ƙafa da mota,Allah ya kawo Yaa Umar da ya fito parlour amsa waya,jiyo kamar hayaniya da ihunsu ne yasa ya fasa ɗaukan wayar,ƙwalawa su Yaa Abuye kira yayi yana cewa "ku fito ina ga rigima suke" da hanzarinsa kafin su fito tuni har ya rigasu isa waje,yanda yaga Hamood ya fizgi motar yasa da wani irin ƙarfi ya fizgo ƙanwarsa ta faɗa jikinsa,wani irin kuka me cin rai Hoor ta fashe da shi,tana ƙoƙarin ƙwacewa tabi motar Hamood da gudu,Yaa Abuye da suka fito gidan yai mata tsawa yana faɗin "what's happening? Meke damunki Hoor? Kukan me kike?" Cikin gushewar hankali tace "Yaa Abuye ya tafi min da ɗana,ya rabani da Abuu Turab ɗina" Yaa Abuye ya dunga kallonta yana faɗin "kamar yaya ya tafi da shi? Ina zai kaishi?" Yaa Umar yace "Allah dai ya rufa asiri na fito,amma da tuni ya bigeta da mota" Yaa Abuye yace "hauka yake zai bigeta? Kou shaye² ya fara?" Yaa Umar ya taɓe baki yace "tou Yaya wallahi nima dai na kasa gane komai,kou maganar da Abbansa yai masa ne yasa yazo ya ɗauke shi?" Yaa Abuye yana kallon can titi da zuwa lokacin babu alamar motar Hamood ya ɓace tuni yace "Umar kamota ku shigo cikin gida" da sauri ya juya zuwa ciki Yaa Umar na riƙe da ita suka bi bayansa,banda kuka babu Hoor take tana waige² kou za taga Hamood ya dawo mata da ɗanta,amma har suka shiga gidan kou ƙurarsa basu gani ba bare shi kou me kama da shi,suna shigowa cikin parlour Mama da Yaa Mansoor suka bisu da kallo,da gudu Hoor ta ƙwace jikinta ta tafi ta faɗa jikin Mama ta sake rushewa da sabon kuka,hankalin Mama a tashe tana kallon Yaa Abuye tace "tou wai dama zuwan nasa na ya karɓe ɗansa ne? Ba tafiya yazo yai dasu kamar yanda kace Abban nasa ya ce muku ba?" Yaa Abuye yace "tou nima dai Mama na yi zaton haka,amma ban san me haka yake nufi ba kuma" kamar gidan da akai mutuwa haka duka sukai shiru kowa da tunanin da yake,sai kuma kukan Hoor da ya cika gurin,Yaa Abuye yana girgiza kanshi yace "Mama ina ganin mu bar maganar nan iya mu kaɗai,mu bashi lokaci muga kou zai dawo da kansa ya nemi ta dawo,i think yana kan dokin fushi yanzu,bazai saurari kowa ba tunda har ya kasa sauraron iyayensa.. Hoor kiyi haƙuri,in sha Allah zai dawo miki da ɗanki,ki bar kukan haka nan kada damuwa yasa wani ciwon ya kamaki" Mama na sauke ajiyar zuciya tace "maganarka haka ne Abuye.. Mu bashi lokacin,Allah ya ganar da shi gaskiya" Yaa Mansoor da ya kasa cewa komai yace "ameen.." Yaa Umar dai ba haka yaso ba,dan shi kaɗai yaga abunda ya gani sanda ya fita,ba don Allah ya kaishi ba da yanzu wani maganar ake yifa ba wannan ba,amma ganin Mama tace a bashi lokaci yasa kawai yai shiru,tunda shi ne ƙarami a ciki bazai so ya kawo nashi maganar ba,kou kiran can gidan babu wanda Mama tasa yayi,duka sukai shiru da niyyar su zuba ido suga kou wani zai biyo ba'asi idan an kwana biyu.

WAZEER!Where stories live. Discover now