Proposalist

157 10 4
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               27

#Proposalist

          Tace "yanzu Mamman ka fi so ka auri wata matar daban akan ka dawo da uwar ƴaƴanka? Shin mene ne laifin Hooriyah ne? Me Hooriyah ta rasa? Shi kenan kai baza'a maka ba dai² ba ka haƙura? Naga Ubangiji ma da ya haliccemu haƙuri yake da mu,duk laifin da muka masa da zaran mun roƙe shi yake yafe mana.. Kai ne baza ka iya yafewa wani ba? To ta ina Allah zai yafe laifukanka kai? Shin baka karanta bane? Baka sani bane? Ko kuwa ina ka kai iliminka da duk ka manta da wannan? Wallahi yau na sake tabbatar da kalar mugun halinka,ace shekaru ɗai² har 20,amma kana riƙe da baiwar Allah a rai,shin ma wai ita ta kashe Sa'adatu ne? Ka faɗa min.. Nace wuƙa ko igiya tasa ta zarge wuyanta ta kasheta?" Hamood ya ɗan kalli Daada,kafin yace komai Daada tace "ina sake faɗa maka wallahi² muddin baka dawo da matarka ba,kayi saken da wani ya aureta,ina tabbatar maka sai ka zo nan gaba kana da ka sani.. Ina cewa ranar da incident ɗin ya faru yarinyar nan ba ta gidan nan,kai fa na kira muka yi magana da kai ka tabbatar min mahaifiyarta aka kira aka sanar mata ba ta da lafiya,unconscious aka kaita asibiti kuma duk cikin gidan nan babu wanda yayi karar ya bi bayanta a ranar,in fact ko bayan nan bamu je mun mata sannu da jiki ba,to ta ina za mu iya zuwa ka yi wannan aika²r.. Shi kenan saboda baka yarda da ƙaddarar data sameka ba,sai ka ɗorawa baiwar Allah laifin mutuwar ƴarta? Kalar na ka adalcin kenan Mamman? In taƙamarka kai uba ne,ita kuma ai naga uwa ce,ta fika sanin raɗaɗi da zafin ciwon data sha,tun daga sanda ta samu cikinta har zuwa haihuwarta da raino.. Saboda son kanka da zuciyarka baka barta da zafin rasa ƴarta da tayi ba,ka rabata da ɗanta again,ka ɗauke shi without sanin kowa har mu iyayenka kai tafiyarka uwa duniya da shi,kamar wani mara mafaɗi kai zamanka can saboda babu wanda yai maka magana ko yace don me.. Shi kenan ka kyauta ka ji Mamman,kayi duk yanda zucuyarka ta raya maka,Allah ya taimaka,mu namu dama ido ne tunda bamu isa mu faɗa kaji ba,Allah ya bada sa'a,aure kuma Allah ya sanya alkhairi,ga kanan ai ga wacce za ka auro,Allah ya baku zaman lafiya.." Fuskarsa ɗaure tamau kamar wanda aka cewa ga mutuwa nan a gabansa ko kuma dai Hooriyah ɗin da bai son gani ko jin zancenta,ƙasa² yace "Daada! Ni fa ba wai yafe mata ne ban yi ba,kawai ni ba na son zancenta,ba na so ana min maganarta da duk abunda ya shafe ta,abunda ya haɗa mu ya raba,don Allah ki daina cewa wai na dawo da ita,ni da ita ko a lahira muka haɗu baza mu taɓa mutunci ba,taje tayi rayuwarta yanda take so nima nayi nawa,Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi.." Daada dake masa wani kallo tace "auu! To ai shi kenan tunda haka kace,Allah ya haɗa ta da wanda zai so ta ya mutunta ta fiye da kai.. Ba don kada nai maka baki ba Mamman,a matsayina na uwa na san muni da illar yin haka,da sai nace duk macen da za ka auro wallahi baza ta taɓa kaiwa Hooriyah ba,mace me haƙuri da son naka,iyayenka da kowa naka mutunta shi take,amma baka duba haka ba.. Babu laifi,Allah ya taimaka" sakin baki Hamood yayi yana kallon Daada with suspicion kafin yayi ƙwafa tare da miƙewa tsaye,rai ɓace yana duban Daada yace "tunda ita kika haifa ba ni ba ai shi kenan.. Sai da safe" wata irin harara ta wurga masa,har ya juya zai tafi kuma sai taga yai turus a gurin yana kallon ƙofa,kallon gurin ta juya kanta tayi don ganin abunda ya tsayar da shi,Wazeer dake tsaye gurin yana kallonsu kawai hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗinsa ya shigo da sallama a ciki²,ransa sosai yake ɓace don babu abunda bai ji ba a maganarsu,amma dake ɗan duniya ne fuskewa yayi yai kamar bai ji komai ba,yanda yayi ɗin nan duk ƙwaƙwar mutum bai isa yace ga wani yanayi da ya shimfiɗa a fuskarsa ba bayan wanda ya saba ajiyewa yau da kullum. Daada ta fara sauke ajiyar zuciya tana barin maganar da tayi niyyar yi tace "Zainul-abideen! Yaushe ka shigo?" Yana zama saman armchair yace "yanzu.. Barka da dare" Daada tace "barka dai.. Ka dawo lafiya? Ya aikin?" Yace "alhmdllh!" Lokaci ɗaya kuma ya miƙe kamar wanda aka tsikara yana faɗin "sai da safe" bai jira Daada tace wani abu ba,haka nan bai kalli inda Dad ɗinsa yake ba ya wuce yayi ficewarsa. Daada dake ta kallon Hamood da ya kasa tafiya,ya yi tsaye kamar wanda aka sassaƙa,tace "ka fasa tafiya ne ko akwai wani abu da ka mance baka faɗa min ba?" Saurin juyawa Hamood yayi yana kallon Daada,yana ɓata fuska yace "Daada please.." Ƙwafa Daada tayi kawai ta ɗauke kai,jin bata ce komai ba Hamood ya wuce yana faɗin "sai da safe?" Ko ci kanka Daada bata ce masa ba har ya fita. Daga nan ɓangaren mahaifiyarsa ko da ya fita zaure ya wuce inda Abba yake,sam bai son maganar ya jima,ya fi son ayı komai wuta² a gama,shi bai ƙi ma ace idan an tashi yanke bikin asa 2 weeks ba,ya yi nisa dai kawai dai duka akai maganar 1 month,sallama yayi tare da ƙarasawa gaban Abba ya zauna,dattijon mahaifin nasa ya ɗan kalleshi tare da faɗin "Muhammad.. Lafiya dai ko?" Hamood da kansa ke ƙasa yace "Abba dama wata magana ce ta kawo ni" Abba na gyaɗa kansa yace "toh! Ba ka bari har na shigo cikin gidan? Yanzu a nan za muyi magana?" Hamood yace "ayi haƙuri Abba" Abba yace "ai ba cewa nayi ka yi laifi ba.." Yana kallon mutanen da suke tare yace "ku ɗan bamu guri za muyi magana" cikin girmamawa duka suka fita,sanda zauren ya rage su biyu kawai Abba yace ",wace magana ce Muhammad?" Kan Hamood har sannan a ƙasa yace "Abba dama ina neman aure ne,to mahaifin yarinyar ya buƙaci na tura magabata na" Abba yana masa wani kallo yace "tou a ina take? Ƴar waye kuma?" Hamood ya shiga bawa Abba bayanin Safwa da iyayenta,duk Abba yana saurarensa bai katse shi ba,sanda ya kai aya kafin yace "yanzu Muhammad ba ka yi haƙuri ka mayar da tsohuwar matarka ba mahaifiyar yaranka? Ka fi so ka je ka auro wacce baka san halayenta ba,itama bata san naka ba?" Ɓata rai Hamood yayi ya ƙi cewa komai,Abba duk yana kula da shi kawai ya gyaɗa kansa yace "shi kenan.. Tunda haka ka zaɓawa kanka,mu a matsayin iyaye namu addu'ah ne,Allah ya sanya alkhairi.. Yanzu sai ka jira na sanar da Yaya,ka san dole zai sa ayi binciken gidan su yarinyar da iyayenta,duk abunda ya faru daga nan kuma zan sanar maka.. Tashi ka tafi" Hamood ya gyaɗa kansa yace "toh Abba.. Allah ya ƙara girma,a tashi lafiya" da kallon tausayi Abba ya bi shi,har ransa yake son zaman ɗan nasa da Hooriyah,amma tunda haka ya zaɓarwa kansa ya ɗauki rayuwa da ɗabi'un turawa,zai barshi yayi yanda yake so,don idan sun takura basu san me zai faru ba,kuma baza suyi shisshigi a lamarin Ubangiji ba,la'alla zaman nasu ne ya ƙare,in kuma da saura za suyi addu'ah Allah ya kawo dalilin da za ta dawo,addu'ah kam dama kullum yana yiwa yaransa duka,hatta su Isma'il da duk matansu suke rashin mutuncinsu bai ware ko mutum ɗaya ba,su gidan sarauta ne komai suka yi idanun mutane kusan duka yana kansu,banda haka a zafin rai irin na Yaa Abdulkarim ma da tuni ya sallami matarsa,su suka tsawatar masa,amma har gobe tayi masa wani abun yana faɗa mata haƙuri yake kuma ta ci darajar su Abba ne,idan ta kai shi bango wallahi sai ta tafi gidansu.

WAZEER!Kde žijí příběhy. Začni objevovat