Wedding bell!

78 6 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2024.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*TIKTOK:ASLISMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*


                               29

#Wedding bell!

*WAZEER*

        Tunda yazo duniya ko yace ya girma ya mallaki hankalin kansa,wani abu bai taɓa haɗa shi da wani ba,zagi ko cin mutunci ba'a taɓa masa ba saboda tsananin takatsan² da kamewa,yau da Safwa ta zageshi ta gaggaya masa magana gani yake kamar wani mummunan zunubi ya aikata,da ƙyar bayan ya tabbatar ta tafi and she'll never came back ya buɗe motarsa ya shiga tare da barin GRA ɗin. A hanya yana driving yana tunanin kalamanta da suke masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa,idan yace bai shiga damuwa da ruɗewa a sababin maganganunta ba,tabbas sai dai ya zama ya faɗi son ransa,kalamanta sun dakeshi da gasken²,tuhumar kansa yake me yasa yayi haka? Me yasa bai sanar da Safwa komai ba? Me yasa da Dad yace masa a'a ya yarda aka tafi a a'a? Me yasa bai sanar da Abba ba his granfa,ko yayi maganar da Mimi ya nemi shawararta? Wata zuciyar tace "wait Wazeer.. Ta ina za ka iya tunkarar wani da wannan al'amarin,bayan ba kowa ya san waye kai ba? In fact ba da kowa kake mu'amala ba.." Numfashi me zafi ya sauke,zuciyarsa na sake tuhumarsa abubuwa da dama da suka shafi rayuwarsa,maimakon ya wuce Galadanci haka kawai yaji bazai iya ba ya ɗauke hanya ya nufi Jambulo,Mimi yake son zuwa ya gani,ko da bazai ce mata komai ba,ko da kuma ba zai iya sharing damuwarsa da ita ba,yana ganin zuwan nasa kawai ya ganta zai sanyaya masa rai. Sanda ya iso line a waje yayi parking tare da sauka motar ya nufi masallacin unguwar,sallar ishaa da bai samu yi ba kasancewar yana hanya akai kira ya fara gabatarwa,bayan ya idar ya fito masjid ɗin ya wuce gidan da ƙafa,a bakin entrance ya tsaya yayi knocking,Kubra tazo ta buɗe tana tambayar "waye?" Bai ce mata ƙala ba sai fuskarsa da ya sake ɗaurewa,ganin wanda ke tsaye yasa ta bashi hanya tana faɗin "sannu da zuwa" a hankali kamar ba zai amsa ba yace "thanks!" Tare da wucewa ciki yana furta "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Jin muryarsa yasa Mimi dake aiki idanunta akan MacBook saurin ɗagowa tana zare glass dake kan fuskarta,Mama dake zaune tana kallon labarai wani lokaci suna hira da Mimi ta saki fuskarta tana faɗin "wa'alaikas salaam warahmatullah wabarkatuh.. A'ahh! Me gidana yau ka tuna da wannan matar taka ne?" Ɗan gyara yanayin fuskarsa yayi ya durƙusa kusa da ƙafar Mama zai zauna saman rug,da sauri Mama tace "tashi² ka zauna kusa da ni Abuu Turab" cikin girmamawa yace "Mama ki barni na zauna nan na gaji ne,ƙasan zai fi min daɗi" Mama tace "tohh shi kenan zauna tunda ka fi son nan ɗin" yayi ɗan murmushi me ciwo kafin ya shiga gaisheta "barka da dare Mama" Mama tace "barkanmu dai Abuu Turab,ya aiki da mutanen gidan naku?" Yace "alhamdulillah!" Mama tace "kamar ka san kwana biyun nan ina cigiyarka" yayi ɗan gajeran murmushi yace "aiki ya min yawa ne shi yasa ban samu zuwa ba" Mama tace "Allah sarki.. Toh Allah ya taimaka yayi kyakkyawan jagoranci" yace "ameen.." Idanunsa na kaiwa kan Mimi dake sauraron hirarsu,a hankali yace "Mimi barka da dare" Mimi da tun kallon farko da tayi masa ta fahimci yana da damuwa ta gyaɗa masa kai tace "barka dai,ya aiki da su Daada?" Yace "lafiya lau alhmdllh" tace "maa sha Allah" tana rufe MacBook dake gabanta. Tunda ya zauna bayan sun gaisa bai sake cewa komai ba yayi shiru yana ƴan tunane²,Mimi ta tashi da kanta ta tafi kitchen ta haɗo masa abinci ta kawo tare da ajiyewa gabansa tana faɗin "ci abinci" ɗaga idanunsa da suke cike da damuwa yayi ya kalleta,kafin yayi magana tace "ci maza u look somehow.. Daga ina kake ne ma?" A hankali ya sauke kansa ƙasa yace "na je wani unguwa ne" tace "Mmmm! Eat first to" ba don yana jin zai iya ci ba,sai don kada Mimi tayi saurin fahimtar akwai wani abu dake damunsa ya gyara zama tare da ɗaukan spoon yayi bismillah,bai wani ci da yawa can ba saboda har yanzun ba komai yake iya ci ba a abincin gargajiya ya ajiye ya sha ruwa. Jifa² da Mama suke hira ita da Mimi sosai ya ɗebe masa kewa,kuma ya rage masa damuwa da zafin da zuciyarsa ke yi,aƙalla ya samu good 2 hours a gidan kafin ya fara haramar tafiya,yana ɗaukan key ɗinsa da ya ajiye ƙasa tun shigowarsa yace "Mama zan tafi" Mama tace "toh Abuu Turab.. Mun gode sosai da zumunci,Allah ya mayar da kai gida lafiya,a gaida su Daadan naku da mutanen gidan" yace "za su ji in sha Allah.. Sai da safe" tace "Allah ya tashemu da alkhairi" ya amsa yana miƙewa tsaye,tashi Mimi tayi ta ɗauki hijab ɗinta tasa,suka jera tare zuwa waje,a balcony suna sauka take cewa "Zaki!" Yanda ta kirashi sai da sunan ya keta ƙirjinsa,a hankali tasa hannu ta riƙo nasa suka tsaya a gurin,tana masa kallon tsanaki tace "meke faruwa?" Shiru yayi da farko kafin ya girgiza mata kai yace "nothing.." Tayi shiru itama tana kallonsa da sake karantar yanayin dake kan fuskarsa,a hankali tana kwantar da murya irin na me rarrashi tace "ko dai baza ka iya sanar min ba?" Da sauri yace "Mimi babu fa" tace "are u sure babu komai?" Ya gyaɗa mata kai da sauri yace "absolutely" tace "ok! Allah yasa" yace "ameen.. Sai da safe" tace "uhumn! Allah ya tashemu lafiya.. Ka gaida gida" yace "na gode" cikin ɗan sauri ya wuce ya sauka yana tafiya,Mimi tayi tsaye tana kallonsa,tunani da yawa suna zuwa ƙwaƙwalwarta game da rayuwarta da ta ɗanta har ya fice gidan.

WAZEER!Where stories live. Discover now