Decision maker

73 11 4
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..*


                               08

#Decision maker

*MUNIBA*

        Daga zoo road gidansu Baniynah suka kama hanyar komawa,a hanya Baniynah na kallon Muniba softly tace "ehm! Sweetheart wane kalar takalmi za muyi amfani da shi ne? Ni fa i don't think zan iya sa hill shoe for the hole kwanakin bikin nan,kada nazo bayan biki ina fama da kaina,amarya na can gidanta ni a barni da jinya" ɗan murmushi Muniba dake driving tayi tana gyaɗa kanta tace "ok! Nima dama na so tambayarki,da kince shi za musa ma,haƙuri kawai zan baki" Safwa dake back seat dai bata ce komai ba,sai da Baniynah tace "and Safwa?" Tana girgiza kanta hankalinta akan wayarta tace "same here" Muniba tai sanyayyan murmushi,kai baza kace wani abu ya faru tsakaninsu ba,tace "at last dai mun tsaya a same ra'ayi,ina gudun arthritis,bayan haka ai da bazan sa plat ba" Baniynah tace "yeah! I see.. Kuna amare,i mean wedding breast,ai dole ku nemi masalaha" Muniba ta buɗe ido tanaa ƴar dariya tace "Allah ya shiryaki Sweet,ji wani iskanci wai wedding breast,dama haka ake cewa?" Baniynah da tai maganar tace "to kuna ƙirjin biki ba dole a faɗa ba" Muniba tace "a fassara me ƴanci,me kike nufi da abunda kikace?" Baniynah ta fashe da dariya tace "ke dai tunda kin gane ai shi kenan" Muniba tace "babu wani tunda na gane,wannan dai cin mutuncin grammar ne,i wish gaban Mami kikai maganar nan" Baniynah ta buɗe manyan idanunta tace "taɓɓɓ! Ai duk abuna kuma bazan yi a gabanta ba" suna ta hira da dariya,Safwa dai was busy a gurin,hankalinta na kan wayarta gaba ɗaya,suna isowa get ɗin gidan Muniba tai horn,get keeper ɗinsu Baniynah wani dattijo ya fito ya buɗe mata da saurinsa,tana dariya ta sauke glasses ɗin gefenta a hankali ta ɗan tsaya tana faɗin "sannu Baba.. Ina yini?" Ganinta yasa dattijon tahowa yana washe baki yana cewa "a'ahh! Hjy kece a gidan namu haka? Ai kuwa mutanen naki sun fita ɗazu,ince kou baku yi waya dasu bane kafin kizo?" Murmushi ta saki tace "na sani Baba,ai tare muka fita da su,ban shigo gidan bane" yace "toh² Allah sarki,an dawo lafiya?" Tace "lafiya lau Baba,ya aiki?" Yace "aiki alhmdllhi,ya mutanen gidan naku?" Tace "kowa lafiya lau Baba.. Sannu da aiki" Baniynah ta kwantar da kai kamar marainiya tana kallon Muniba tana ɗan murmushi,ita fa haka halinta yake duk sanda za tazo gidansu sai ta tsaya get sun gaisa da megadin,ita take ce masa Baba shi yasa kowa ma ya ɗauka,akansa suna yara ansha yin faɗa da ita,idan taji an faɗi sunansa gatsal ko ance masa Malam Ahmadu,akan rashin ce masa Baba ba har kuka take,sai da suka gama gaisawa kafin ta ƙarasa ciki,ƙasan tent dake ɗauke da cars sama da 5 ta tai parking sannan suka sauka dukansu zuwa entrance,Muniba dake gaba ta danna bell,basu yi minti 2 ba tsaye wata kyakkyawar budurwa dake tsananin kama da Baniynah ta buɗe ƙofa,sai dai ta fi Baniynah hasken fata,ita fara ce tas,tana saki murmushi take faɗin "Oyoyo ƙanwata.." Rungume juna sukai ita da Muniba dake dariya tana cewa "Yaa Khalidah kina gida abunki bakya fita,ku dai amaren nan kunji daɗinku" Khalidah tace "tou kou dai za ki fito da miji ne,su Abba su shiga ayi komai a wuce wajen,kema ki shiga sahun amaren?" Kama baki Muniba tayi tana zaro ido tace "nahh! Ai ban isa aure ba,so kike Yaa Khalifa ya hayayyaƙo min yace me na sani? Mmmm.. Mama fa?" Khalidah dake dariya tace "alright! She's upstairs" da sauri Muniba ta wuce tana cewa "bari naje mu gaisa" daga haka tabi stairs tai sama,a upstairs parlour Muniba ta tarar da Mama,kana kallonta za ka gano kamar da suke da yaranta biyu mata,zaune take tana waya da kaya tsibi² a gabanta manyan laces tsadaddu iri²,kana gani kasan kayan fitar biki ne na ankon iyaye,tai sallama a hankali kafin ta zauna,Mama data juyo tana ganinta ta saki murmushi tana faɗin "ameen wa'alaikis salaam.. Ok we will talk later,na gode,sai kin jini kuma" tana ajiye wayar tace "a'a daughter kin iso? Ai nan sukaita jiranki kafin su fita balcony,Safwa na cewa su jiraki can kina zuwa sai ku tafi" Muniba ta ɗan zamo daga kujeran da take tana faɗin "ina yini Mama?" Mama tace "lafiya lau.. Ya gida da su Mami?" Muniba tace "suna nan lafiya suna gaisheku" Mama tace "muna amsawa.. Hope saƙona ya isa gurinta?" Muniba tace "saƙo kika aika mata bana nan? Abun ci ne?" Mama na girgiza kai tace "a'a na zubarwa ne.." Dariya Muniba tayi tace "wallahi ban sani ba sai dai in na koma na tambayeta" Mama tace "it's ok! Nima zan kirata da kaina idan na natsu" kamar wasu friends Mama suke hira har Muniba na tayata ware laces ɗin da suke zube na mutane,can bayan ɗan lokaci sannan sai ga su Khalidah sun yo saman ita da Baniynah,Muniba ta kalli Baniynah tace "a'ahh! Ina Safwa? Ba dai har ta wuce ba?" Baniynah tace "yeah! She's gone,wai tana da appointment ne" Muniba ta gyaɗa kai tace "ohh! Allah sarki" daga haka sai bata sake cewa komai ba,Mama na kallon Baniynah data zauna ta riƙe waya a hannunta tace "tohh! Ai kin samu owness corner za ki fara sana'ar naki kou? Tou sauko maza kisa hannu mu gama cirewa mutane kayansu,daɗin Muniba kenan babu yanda za'ayi taga kana aiki ta samu guri ta zauna,ku kuwa sai ance kuyi" Baniynah tace "Mama! Ɗan hutawa fa nake yi" Mama tace "ai ita dake baiwar gidanku ce,ina jin kuna meeting za kuce ta fito da mota,ta kaiku ta dawo da ku,shi ne za kice min wani hutawa kike,da me ya kawoki nan? Ai da kinyi zamanki can downstairs kin huta" Muniba dai aikinta take bata ce komai ba,Baniynah ta sauko tana kallon Khalidah dake mata dariya,tace "Mama kinga Yaa Khalidah tana min dariya kou?" Mama tace "ohoo! Kuka sani kuma,ni kawai aiki nace azo ayi min,kema Khalidah sauko baza kizo ki samu gaba kina kallo ba,maza² taso ayi hannu da yawa ayi a gama" da sauri Khalidah ta zaro ido tace "Mama har ni kuma?" Mama tace "haka nace.. Kou baza kiyi ba? Ai tunda kika samu damar tsokana,haka za ki sauko kisa hannu,babu ruwana da bikinki za'ayi,tunda ba'a fara ba bazan zuba ido aƙi yi min aiki ba" dariyar ƙeta Baniynah ta fashe da shi tana cewa "Allah shi ƙara,ai kinga daɗin tsokana yau" Mama ta kalleta da sauri tace "tou azagwai,kika sa tsiya tas zance tai zamanta" da sauri Baniynah ta zaro ido tace "Mama itafa ta fara min dariya wallahi" Khalidah ta marairaice tace "dan Allah Mama kice nai zamana,ni yaushe nai mata dariya in ba sharri irin na Baniynah ba?" Mama tace "ai da dai ban san halinku ba dukanku sai kice min haka,maza sauko Hjy kisa hannu ayi a gama min aiki na,ina da ku idan ban sa kunyi min ba wa zan sa?" Khalidah tace "Mama fa wallahi baki da gwani" Mama tace "bazan yishi ba kuma,aiki ne dai sai kinzo kin yi min,gara ni dana haifeki na moreki,kafin wasu su fara gwada sunma fini iko dake.. Maza² get down ai min aiki,bari naji da sa Laminu ya kai kayan nan nima na huta" Muniba dake lissafin wanda suka ware tana ƴar dariya a ciki² tace "Mama kiyi zamanki a gefe kawai kisa ido,yanzu za mu gama miki komai" Mama tace "Allah yai miki albarka daughter,ya kawo miji na gari na aurar dake,ai tunda kika ce na huta hutawar zan yi,idan ba ke da kike tausayina ba,in dan su o'o ne sai na kwana nan zaune ina aiki,baza a dubi uwa ace na bari na huta ba,shi yasa nake faɗen alkhairinki a gidan nan.. Har haushina ake ji kuma baza'a fasa ba" Khalidah tace "kai Mama" Mama tace "tou na faɗi abunda ba dai² bane uwata?" Muniba tace "Mama ki rabu dasu kawai" Mama tace "na barsu da halinsu daughter.. Amma idan ba'ayi a gidan iyaye ance Allah yayi albarka ba,a je gidan miji da kou sannu bazai ce ba" Baniynah ta fashe da dariya tace "kai Mama" Mama tace "attoh! Ai gaskiya na faɗa kou na yi ƙarya?" Muniba tace "wane mutum yace kin faɗi ba dai²ba Mamanmu" Mama tai murmushi ta ɗauki remote tana canja channel,Baniynah ta kalli Muniba tace "wallahi duk makircinki ne ya janyo" Muniba tai mata gwalo tace "yiiii! Ai kin manta mace fa nake,kou shaiɗan yanzu sai yaji tsoron zama nan gurin" Khalidah tace "ni dai duk ku ajiye hiran nan naku muyi mu gama tunda kun janyo mana aiki" Baniynah tace "a'a Yaa Khalidah ga wanda ta janyo mana nan,ki dena yin jam'u" Muniba tai murmushi,Mama dake kallon Arewa24 tace "kada ki kulasu daughter.. Idan kuka sa tsiya wallahi zance ta bar muku mu ƙarasa,ai dama tare muke yi da ita kuka zo kuka tarar da mu" Baniynah ta gwalo ido tace "aahhhh! Yaa Khalidah dan Allah ki shiru kawai muyi mu gama" hira suka ci gaba da yi,har suka gama aikin suka kwashe kayan suka zubesu can angle na parlour,Mama ta kallesu tana sakin murmushi tace "sannuku tou Allah yayi albarka" Baniynah da Khalidah suka amsa can ƙasar throat,Muniba ta tafi kusa da Mama ta zauna tace "ameen Mamanmu" Mama ta kalli su Baniynah tace "auu! Haushi kuke ji na saku aiki shi yasa baza ku amsa ba?" Baniynah ta turo baki tace "mun amsa fa" Mama tai murmushi tace "kada ma mutum ya amsa mana,ni dai tunda an gama min aiki na ai shi kenan" dariya Muniba ta fara,Khalidah ta tashi da sauri ta ɗauki wayarta tace "sai an jimanku" Mama tace "Allah ya nuna mana,ai idan mutum bai zauna anyi hira dashi a gidansu ba,gidan miji dai in yaje ba hutu aiki zaita yi,idan ba'a saba yi tun a gida ba sai anje a fara kiran Mama a waya ana mata kuka" dariya dukansu suka kwashe da shi,Khalidah ta dawo da sauri ta zauna tana cewa "Mama dan Allah ki dena cewa haka,komai akayi sai kice in anje gidan miji kaza" Mama dake murmushi tace "attohh! Me zance in ba wannan ba?" Nan sukai ta hira kuma Muniba na dariya.

WAZEER!Where stories live. Discover now