Divorce

92 11 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                    (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..*

   

                               02

#Divorce

                 Salati fadawan gurin duka  suka ɗauka,duk da sun fahimci cewar Mysha ta rasu tun farkon da aka buɗe motar,amma babu wanda ya iya yin wani abu har sai da ya basu umarni,ganin ana ta diri²n abunda za'a ɗauketa yasa ya cire babban rigarsa yace asata ciki,fadawa suka karɓa aka ɗaukota jikinta har ya kumbura aka rufe,banda masifaffen wari babu abunda gurin keyi,haka suka keta cikin gida Abba na gaba suna biye da shi sukai ɓangaren Daada,dai² lokacin Daada na amsa kiran da akai mata a waya tace "Mamman! Direban ya taho nake ga tun ɗazu,na aika an kirasa kuma na sanar masa,ka ɗan yi haƙuri yana tahowa" sallamar Abba Waziri da hayaniyar fadawa yasa ta amsawa tana kallon ƙofar shigowa,warin da ya fara iso mata yasa tai saurin toshe hanci jin amai na shirin ƙwace mata tana faɗin "um'um! Wannan warin na mene ne ni Sa'adatu? Naman kai ne wannan ɗin ya ɗume gurin da wari? Jummai! Mero!!!" Ta shiga ƙwalawa bayinta kira,Abba Waziri da ya shigo yana kallonta ya girgiza kanshi cike da jimami yace "ba naman kai bane,naman mutum ne.. Jikarki da aketa nema ce muka gano" saurin miƙewa Daada tayi tana kallonsa a tsorace tace "jikata!? Mysha!? Sa'adatu!? Me suna na?" Abba Waziri ya zauna yana gyaɗa kanshi yace "Allah yai mata rasuwa" salati Daada ta ɗauka tana faɗin "a ina aka ganta? Me ya sameta? Me taci? Waye ya ɗauketa?" Abba Waziri yace "yanzun nan Isiyaku ya ganota a cikin motar Babanta" jikin Daada banda rawa babu abunda yake saboda kaɗuwa da tashin hankali tace "duk neman da akaita mata a garin nan dama tana cikin gidan nan? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Ta yaya? Waye ya kaita mota kuma?" Abba Waziri dai yai shiru ya riƙe kanshi,kuka Daada ta saki tana girgiza kai tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Wannan wane irin baƙin labari ne? Yaya iyayen yarinyar nan za suji ni ƴasu idan suka samu labarin nan?" Da sauri² kuma sai ta ɗaga wayarta ƙirar Nokia ta shiga duba number Hamood,bugu ɗaya ya ɗauka ranshi a ɓace bai jira yaji me za tace ba yace "Daada! Ni bazan iya ci gaba da jira ba,na taho a taxi kawai" Daada dake tsayar da kukanta tace "toh³! Mamman,sai ka iso" daga haka ta ajiye wayar tana rufe bakinta saboda kukan dake cin zuciyarta,Abba Waziri ya kalleta jikinsa yai sanyi yace "Sa'adatu! Kuka ba naki bane yanzu,ya kamata ki ƙwarara kanki kuma ina so zancen nan ya tsaya iya mu kaɗai,shi Muhammadu tunda ya taho kin san hanyar da ya biyo yazo,yana buƙatar hutu duk da hankalinsa a tashe yake,kada mu ƙara masa wani damuwa,mu barsu har zuwa wayewar gari idan Allah ya kaimu,yanzu kafin shigowata na kira Isma'il,duk inda yake yana hanyar zuwa,na sanar masa abunda ke faruwa,in sha Allahu da ya iso za mu tafi akai gawar asibiti ai checking,saboda mu san abunda yai silar mutuwarta" Daada ta gyaɗa kanta tace "toh shi kenan" Abba ya tashi yana kiran bafadensa dake waje,yana shigowa Abba Waziri ya kalleshi yace "ɗauki gawar muje asibiti yanzun nan" respectfully bafaden ya amsa tare da ɗaukan gawar Mysha dake naɗe cikin babbar rigar Abban suka fita,Abba Waziri na fita yake cewa Daada "sai mun dawo" Daada ta amsa tana binsu da kallo har suka fita gidan. Few minutes da barinsu Abba Waziri gida,taxi ya tsaya ƙofar gidan,saukowa kyakkyawan matashin mutumin yayi fuskarshi ɗaure,duka a shekaru bazai wuce 38 yrs ba,wallet ya ciro a aljihun wandon suite ɗinsa ya zaro kuɗi ya bawa driver daya ciro masa jakarshi dake booth,ya karɓa tare da yi masa godiya sannan ya nufi babban ƙofar gidan,yau ya yi mamaki da yaga zauren gidan babu mutane,Abbansu da ya san idan yana nan sai ya kai 10pm,baya shiga gida har sai ya tabbatar kowa ya shiga gida cikin ƴaƴansa,sannan zaisa a rufe ƙofa shima ya shiga gidansa,amma yau 9pm ma baiba ya tarar ba ya nan,tou kou dai duk akan ɓatan Mysha ne? Ya ɗan taɓe baki sannan ya shiga ciki,kai tsaye ɓangaren mahaifiyarsu wanda suke kira Daada ya nufa,tunda ya shigo bai haɗu da kowa ba har ya iso daf da ɓangaren na Daada,sai ga wani bafaden Abba nan yana fitowa zai wuce,da sauri bafaden ya nufoshi yana faɗin "ranka shi daɗe Barka da zuwa.. An zo lafiya? Ya ƙarin haƙurinmu?" Gabanshi ne ya faɗi,yana kallon bafaden kamar bai gane me yake nufi ba yace "waye ya rasu Shu'aibu?" Bafaden ya kama bakinsa da sauri ganin kamar bai sani ba,da sauri yace "a'a babu kowa bari naje ana jirana ne" da sauri ya wuce ya bar gurin,da wani irin kallo ya bishi ya kasa buɗe baki yai magana saboda gabanshi dake tsananta faɗuwa,tunanin Mysha da aka sanar masa ta ɓata tun jiya ya ƙara sashi shiga cikin damuwa,wucewa yayi cikin ɓangaren Daada,jikinshi na bashi tabbaci akan maganar Shu'aibu,zai yi wahala ba ƴarshi Mysha ce ta rasu ba,shi yasa daga zuwansa Shu'aibu yake masa ta'aziyya? Ya tambayi kanshi,da sallama ya shiga parlon yana janye da jakarshi na kaya,Daada dake zaune ita kaɗai shiru tana tunani ta ɗago da sauri,tana kallonsa wasu irin hawaye suka kawo idanunta,da sauri ta kauda kai gefe tana gogewa a ɓoye tace "Mamman! Sannu da hanya" zaunawa yayi kusa da ita yana kallonta ƙur gabansa na tsinkewa yana faɗuwa,a hankali yace "Daada! Wani abu ya samu Mysha ne da kuka kasa sanar min?" Da sauri Daada ta girgiza masa kai a ɗan ruɗe tace "a'a Mamman babu komai,bamu ɓoye maka komai ba" yana mata kallon tsanaki yace "idan babu abunda ya faru me yasa Shu'aibu da ya ganni yai min gaisuwa? Waye ya rasu Daada? Ƴata Mysha? Mamana ce ta rasu?" Kasa kallonsa Daada tayi saboda kukan da ya zo mata,yace "Daada please ki sanar min,Mysha ta rasu?" Gyaɗa kanta Daada da kuka ke cinta tayi tace "Allah yai mata rasuwa,yanzun nan babu jimawa aka ganota,amma Abbanku sun tafi asibiti da gawar" kallon Daada ya tsaya ya dunga yi kamar bai gane me take cewa ba,lokaci ɗaya ya sauke numfashi me nauyi ya furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Sai kuma yai shiru damuwa me girma na rufeshi,his little girl Mysha ta rasu? How? And a ina? Ya tambayi kanshi,lokaci ɗaya ya kalli Daada yace "Daada a ina aka ganota?" Labarin da Abba Waziri ya bata ta sanar masa,ya dunga kallonta kafin da sauri ya miƙe ranshi a ɓace yace "Hoor tana ina? Ta san cewa anga Mysha? Why ban ganta a nan ba?" Daada ta riƙo hannunsa da sauri tace "tana can gidan,zauna Mamman" yana kallon Daada ranshi a ɓace yace "how can i sit Daada? Ƴata fa ce ta rasu,shigowata kenan nasamu labarin nan,kuma ace ita tana can hankalinta a kwance? Garin wane sakacin ta bar yarinyan da take just 3 yrs har ta tafi garage ta shiga mota ta kulle kanta? How? Wace irin uwace wannan? Wane irin sakaci ne haka?" Da sauri ya ƙwace hannunsa ya nufi ƙofar fita ɓangaren,Daada na kiransa bai saurareta ba yai gaba zuciyarsa na bala'in raɗaɗi,sanda ya iso apartment ɗinsa buga ƙofar ya dunga yi da azababben ƙarfi,bai damu da cewar dare yayi ba kuma mutane za su iya fitowa saboda gidan ba iya su kaɗai bane,akwai Yayyunsa sannan da ɓangaren bayin gidan kuma,Suwaiba ce ta taho ta buɗe ƙofar gabanta na faɗuwa saboda ba'a taɓa musu irin bugun nan ba,tana buɗewa da sauri ta matsa tana faɗin "Dad sannu da dawowa" bai ko kalleta ba yai ciki yana tambayarta "ina Hoor?" Tace "yanzun nan ta shiga ciki ta ɗan kwanta ba ta jin daɗi" bai sake bi ta kanta ba ya wuce corridor yana tafiya da ƙarfinsa,yana zuwa ya buɗe bedroom ɗinta ya shiga babu kou sallama,Hoor dake kwance idanunta da suke zafi lumshe saboda kumburi da tsananin ciwon da kanta ke yi,buɗe ido tayi saurin yi dama ba bacci take ba,kawai dai ta kwanta ɗin ne ta samu hutu,dishi² take ganin mutum saboda babu haske ɗakin sai hasken corridor da ya hasko har cikin ɗakin,daga yanayin ƙamshin daya ziyarceta ta gane kou waye,buɗe baki tayi da iya ƙarfinta tace "Hamood!" Yana sauke numfashi ya mayar da ƙofar ya rufe tare da kai hannunsa kan switch ya kunna bulbs,hasken da ya gauraye ɗakin yaiwa idanunta ƙarfi yasa ta runtse idonta,takowa ya dunga yi har ya iso gaban gadon da take kwance,Abuu-Turab da ya gama kukan ɓatan Mysha yai bacci da ƙyar a jikinta,kallonsu yake kamar yau ya fara ganinsu,bai zauna ba yana daga tsaye yace "Hoor! Me yasa kike nan? Baki san abunda ke faruwa bane?" Idanunta a kulle cike da ƙarfin hali tace "Babana yana ta rigima ne tun safe saboda ɓatan Mysha,duk da suna faɗa sosai,amma ka san yanda suka shaƙu da ita,yanzun nan bai jimaba dana samu yai bacci" yana mata wani kallo a ƙasa² yace "Mysha ta ɓata kou dai sakacinki yasa ta rasu a cikin mota!?" Da ƙarfi ƙirjinta ya wani bada ras har bata san sanda ta miƙe zaune tana kallonsa ba,tace "me kace Hamood? Mysha ta me?" Wani banzan kallo ya dunga sakar mata daga tsayen da yake,lokaci ɗaya ya juya ya fita daga ɗakin,manta wani ciwo dake damunta tayi,da sauri ta sauka gadon ta biyo bayanshi kamar wanda ƙwaƙwalwarta ya taɓu tace "Hamood! Stop please,ka tsaya kai min bayani yanda zan gane,wace Myshan kake cewa ta rasu? Ba dai ƴata ba?" Bai saurareta ba ya nufi ƙofar fita daga part ɗin gaba ɗaya,biyoshi tayi a haukace tana kuka tana faɗin "Hamood! Ka sanar min don Allah" ɓangaren Daada suka nufa dukansu yaƙi tsaiwa ya saurareta,suna shigowa suka samu Daada na sa Jummai ta ɗauke jakarshi daya bari ta kai ɗakinta,surutan da Hoor take wanda ke biye da shi da gudu² yasa Daada saurin waigawa tana kallonsu,da sauri Hoor ta nufi Daada ta zube a ƙasa tana risgar kuka tace "Daada don Allah kice ya faɗa min,ina yaji labarin Mysha ta rasu? A ina ya samu wannan labarin da ni ban sani ba ni da nake garin?" Alama Daada tai mata da hannu tazo,da sauri ta rarrafo ta matso tana wani irin kuka me ban tausayi,duk wanda ya kalleta dole zuciyarsa tai rauni,amma kou ɗis Hamood bai ji ta bashi tausayi ba,yana kallon Daada yace "Daada zan tafi asibitin gurinsu Abba" Daada da jikinta yai sanyi tana shafa kan Hoor dake jikinta tace "tou kuma daga zuwanka za ka fita Mamman? Ai da ka zauna ka huta kou dan tafiyar da kai" fuskarsa a ɗaure yana girgiza kai yace "babu komai Daada bari naje,na fi so nasan abunda yai causing mutuwarta" Daada za tai magana ya juya yana cewa "Daada please ki barni don Allah" daga haka ya bar musu parlon,Hoor na ƙoƙarin tashi ta bishi Daada ta riƙo hannunta,da sauri ta waigo tana kuka tace "Daada zan bishi ne" Daada tace "dawo ki zauna Hoor,kin san halin Mamman da baƙin taurin kai da kafiya,kina ganin yanda yai fushi bazai taɓa bari ki bishi ba yanzu,ni banma ga dalilin da yasa yaje ya sanar miki ba,ke da ba lafiya ne da ke ba yau duka,ga Zainul-abideen yana ta kukan rashin ƴar uwarsa,zauna mu jira har su dawo muji daga bakinsu" ba'a son ranta ba Hoor ta koma ta zauna,haka nan dai sai share hawaye take akai² hankalinta ya mugun tashi,she blame no one akan mutuwar Mysha bayan kanta,me yasa kafin ta tafi bata nemo ƴarta da kanta ta damƙata a hannun Suwaiba kou wani a cikin gidan ba? Kuma kou gurin Daada za ta iya kawota saboda ta saba da ita sosai,me yasa ma bata tafi da yaranta ba? Tasa su gaba su tafi tunda weekend ne babu school. Daren ranar nan kusan za'a iya cewa har ya fi daren jiya na ɓatan Mysha,babu irin maganar da ba'a faɗa ba a gidan yinin yau,har fa da masu cewa akan ɓatan nan nata da ba'a san inda take ba,ai gara ace mutuwa tayi kowa yaga gawarta ya tabbatar ta rasu,sama da ace ɓata tayi irin wanda shi kenan baza'a sake ganinta ba,ganin yanda Hoor take kuka nasiha sosai Daada tasa ta gaba tana mata akan tawakkali,ita dai bata fahimtar komai sam,haka kawai zuciyarta ta shiga saƙa mata idan bata koma ba wani abu zai iya samun Abuu-Turab,da ƙyar bayan wani lokaci taiwa Daada sallama ta fito da niyyar komawa can part ɗinsu,ba don tana jin bacci ba kou idan ta kwanta za ta iya runtsawa,sai saboda ta bar Abuu-Turab dake kwance yana bacci,sannan Suwaiba bata san ta fito ba sun bar ƙofar a buɗe,tunda ta nufo part ɗin sai tsoro duk ya sake kamata,irin tsoron rasa wani makusancinka,tunda ta shigo ta ganshi yanda ta barshi sai kuma ta shiga kukan rashin ƴarta,ranan yanda taga rana haka darenma bata iya runtsawa ba,damuwa da tashin hankali sosai suka rufeta har wani zazzaɓi² ta dunga ji yana saukar mata. Da ƙyar ta iya kaiwa asubah a wannan yanayin,kiran farko ta sauka gadon tana tafiya da ƙyar² kanta kamar zai faɗo saboda tsananin ciwon da yake mata,a daddafe ta shiga bathroom tai wanka ta ɗauro alwala,tana fitowa tasa babban hijab har ƙasa ta shimfiɗa darduma,a zaune tai nafila tana ta addu'ah hawaye na mata zuba,a zaunen kuma dai ta sallaci sallar asubah,tana nan zaune inda tai sallah saman sallaya tana addu'o'inta har gari yayi haske,jikinta a sanyaye ta tashi tana kallon Abuu-Turab dake bacci innocently ta nufi ƙofa ta fita tana riƙe da wayarta,layin Yaa Abuye ta kira muryarta a dashe sosai suka gaisa yana tambayarta babu labarin Mysha har yanzu? A hankali hawaye suka sauko idonta tace "Yaa Abuye! Mysha is dead an ganta jiya,tun da dare su Hamood da Abba Waziri suna hospital da gawarta" salati ya shiga jerawa yana faɗin "bari nai waya da su Mansoor na sanar musu,in sha Allah gamu nan a hanyar zuwa.. Allah ya bamu haƙurin rashinta" katse wayar tayi saurin yi,bitterly wani kukan ya sake ƙwace mata. A parlour lokacin data fito ta samu Suwaiba na mopping,tana ganin fitowarta ta tsaya da aikin da take,har ƙasa ta tsuguna tana faɗin "Mimi! Barka da fitowa.. Ina kwana?" Da dasasshen muryarta Hoor tace "yawwa Suwaiba,sannu da aiki" Suwaiba na kallonta da tausayawa,har Hoor ta kai ƙofa za ta fita,sai kuma ta juyo tana faɗin "Abuu-Turab na nan yana bacci a ɗakina,ki kula da shi idan ya tashi kizo ki sanar min" Suwaiba ta amsa respectfully tana bin uwar ɗakinta da kallo cike da tausayawa na irin halin data tsinci kanta a ciki kwanakin har ta fita,dai² Hoor na isowa ɓangaren Daada,ta hango tahowar su Abba shi da Hamood dake ɗauke da wani jakar leda da hannu bibbiyu,saurin shiga ciki tayi saboda ba su kaɗai bane akwai ƴan uwan mijinta maza su 4. Hamood su 8 iyayensu suka haifa,babbar yayarsu mace ce Khadijah,ta rasu tun tana da 5 months a duniya,bayan ita sai Yaa Isma'il,Yaa Abdulkarim,Yaa Ibrahim da Yaa Yusuf me sunan mahaifinsu Abba Waziri wanda Hamood yake bi,sai mata biyu ƙannensa Hafsah sannan Amina itace autarsu,duka cikinsu kuma babu ɗan kishiya cikinsu ɗaya,Daada Sa'adatu ita kaɗai ce matar Abba Waziri,aurensu tun sakun lalle,a yanzu wanda suke raye a duniya su 7 ne,dukansu sunyi aure matan kam basa ƙasar. Da sallama ta shiga parlon Daada,nan ta tarar da matan Yayyun Hamood sun shigo,suna ganinta suka fara kallonta da wani irin emotion a fuskokinsu,a hankali ta ƙarasa ta durƙusa gaban Daada,tun batai magana ba fuskarta kawai ya isa bayyana maka how sad she's,Daada tace "sannu Hoor" muryarta a dashe saboda kuka tace "barka da safiya Daada" Daada ta amsa tana dafa kanta tace "Barka dai Hoor,ya muka ji da wannan al'amari kuma? Ya ƙarin haƙurinmu?" Hoor da hawaye har sun fara zuba idonta ta amsa,sannan suka shiga gaisawa da facalolinta,sai ga sallamar su Abba sun shigo,kallo ɗaya za kai musu ka tabbatar suna cikin damuwa musamman Hamood,sannu da shigowa aka dunga yi musu,Hamood ya wuce hanyar ɗakin Daada idanunsa sun kaɗa sun yi mugun jaa,kana kallonsa za ka san bai yi bacci ba throughout the night,Abba ne ya zauna saman kujera,Daada tai masa barka da dawowa,haka surukanshi matan ƴaƴansa sai gaisheshi suke suna masa ta'aziyya yana amsawa idanunsa akan Hoor da tai zuru²,ba idanunta kawai ba hatta fuskarta ta mugun kumbura sun yi jaa,da hannu ya yafitota yai mata alamar tazo kusa da shi,rarrafowa ta dunga yi tana kuka mara sauti,Abba ya dafa kanta yana kallonta sympathetically yace "haƙuri za muyi ƴata,Allah ya rubuta iya kar kwanakinta kenan a duniya tare da mu,Allah shi bamu ita kuma ya tsara ba mai nisan kwana bace,shi ya ƙaddara ta wannan hanyar za ta mutu,ki bar yi mata kuka ki mata addu'ah,domin yarinya ce ita ƙarama,bata da laifin komai a kanta,sai dai muyi fatan Allah yasa ta zama cikin masu cetonmu ranar lahira,Allah ya bamu haƙuri da juriyar rashinta.." Nasiha sosai Abba ya dunga yi mata da ya sanyaya mata jiki,ba'a jima ba sai ga sallamar Mama da su Aunty Zainab dukansu har da su Yaa Abuye,su Daada suka amsa ana masu sannu da zuwa,idanun Mama akan ƴarta ta zauna suka shiga gaisawa da su Abba tare da yiwa juna ta'aziyya. Guraren 8am Hamood ya fito bedroom ɗin Daada,ganin su Mama yasa ya tsaya suka gaisa yai mata sannu da jiki,ita da su Yaa Abuye sukai masa ta'aziyya,daga haka ya wuce ya fita bai ko kalli inda Hoor take ba,tunda ya fito ita kam idanunta na kansa,bala'in damuwa take ji idan ta tuna rasuwar Mysha da yazo mata bagatatan,bai jima da fita ba ya dawo da yadin likafani ya wuce,shi ya shirya Mysha da hannunsa sannan ya ɗaukota ya fito da ita,ya ƙarasa gabansu Abba ya ajiye musu gawarta,daga haka bai ce komai ba ya juya ya fita,a yanda ta dunga wari jiya kai baza kace itace yanzu a gabansu ba,kamar abun tsafi suna kaita asibiti aka fesa mata magunguna bayan an gama binciken da za'ayi akasata cikin locker ta kwana,gawar ta daina wannan azababben warin,kuzo kuga yanda ake kukan mutuwa,duka matan da suke parlon kasa daurewa sukai,saboda yanda Mysha take da shiga rai,yarinya ce ƙarama amma duk wanda ta sani a cikin gidan kou ta taɓa ganinsa a wani gurin,indai ta fito ta ganka kou baka kula da ita ba sai ta biyoka ta riƙe maka riga tana dariya,she's just 3 amma idan tana abu kamar babba,she's smart and beautiful,tana da saurin sakewa da mutane kamar itace babba akan Abuu-Turab,sam shi bai sakewa da mutane,idan ba Abba Waziri ba sai kou parents ɗinsa su ɗinma Mimi,kou Daada da take Grandma ɗinsa bai son shiga gurinta,duk wasan da take masa tana cewa mijinta kou tace Waziri me jiran gado ba zaisa ya taɓa tankata ba,shi haka nan Allah ya yishi miskilin gaske,idan kaga murmushinsa tare da Mimi ne,sai kou little sis ɗinsa Mysha,shima sai in tsokanarsa take kou ta takurashi shi ne zai mata ɗan murmushin yaƙe,not deep murmushi da zaisa kaga kamar tana dariya,daga haka zai ɗauke kanshi,baza ka taɓa ganinsa yana ƙyaƙyata dariya ba. Hoor kallon ƴarta kawai take tana kuka me taɓa zuciya,sallamar ɗaya cikin fadawan Abba Waziri yasa Yaa Isma'il tashi ya nufi ƙofa,yana kallonsa yace "ya akai Salisu?" Bafaden yace "mai martaba ne ya iso yana zaure,ya ce ai masa iso zuwa cikin gida gurinsu Daada" da sauri Yaa Isma'il yace "ok! Bari na sanar da Abba" da sauri ya juya ciki gurin Abba,ɗan sunkuyawa yayi dai² kunnensa yace "Abba Uncle Abduljalal ne yazo yana waje,ya ce ai masa iso zai shigo yaiwa su Daada ta'aziyya" da sauri Abba ya tashi yana gyara babbar rigarsa yace "toh! Muje sai mu shigo tare" daga haka suka nufi waje Abba na sanar da Daada Mai martaba ya zo zai je za su shigo tare,ta amsa underneath tana maimaita faɗin "Mai martaba!? Shi ne yazo da kansa? Su da ake zuwa yiwa gaisuwa yau shi ne yazo nan da kansa?" (Ɗabi'ar sarakai ne idan akai mutuwa wani makusanci kou bawansu ya mutu sai dai aje a musu gaisuwa),mamaki duk ya cika Daada,Abba suna fita babu jimawa sai gasu nan shigowa fadawa na tafe suna zabga kirari,har suka shigo cikin parlon da sallama,Daada da su Mama sai barka da shigowa suke masa,Mai martaba ya zauna saman kujera aka shiga gaisawa da yiwa juna ta'aziyya,Mysha jika ce a gurinsa shima,saboda shi da Abba Waziri wa da ƙani suke,sarki Abduljalal sai kallon Hoor yake yana mata sannu,sun ɗan jima a nan kafin su Yaa Abuye suka tashi za su tafi jana'iza,wanda za'a gudanar a harabar gidan sarki tunda babu nisa daga gidan zuwa can,duka mazan suka fita tare da su Abba,Hamood da ya fita tunda ya ajiye gawar Mysha ya shigo sanye da jallabiya hoodie,fuskarshi tai fayau idanunsa har sannan a rine,Hoor na zaune sai kallon ƴarta take hawaye suna sauka fuskarta,a hankali ya ƙarasa yana kallon agogon dake ɗaure wrist ɗinsa yace "i think it's almost time yanzu,Daada zan tafi kada mu ɓatawa mutane lokaci" Daada ta gyaɗa masa kai tace "tou Mamman.. Ɗauketa kuje,Allah yasa me ceto ce" ya amsa tare da sunkuyawa ya ɗauki gawar dake rufe da zanin Daada,buzun da yasa aka shigo masa da shi ya isa ya ɗauketa yasa ta ciki ya nannaɗe,duk abunda yake su Aunty Zainab suna kallonshi har ya fita,Mama sai haƙuri suke bawa Hoor data sa kanta tsakanin thighs tana kuka mara sauti. Abuu Turab ne ya shigo yana wara idanunsa dake cike da bacci yana kiranta "Mimi! Mimi!!" Saurin ɗago kanta tayi hawaye shaɓe² a fuskarta,da dasasshen muryarta tace "here i'm Babana,come here" tsaiwa yai yana kallon mutanen dake parlon one by one kamar bai ganesu ba,fuskarsa a tsume ganin yanda kowa ke kallonsa ya sake cewa "Mimi!" Da sauri ta miƙe tsaye lokacin Daada na cewa "zo Zainul-aabideen.. Ga Mimin naka a nan" kallon inda ta nuna masa yayi sai ya ganta tsaye tana kallonsa da kumburarrun idanunta,da sauri ya nufeta ya shige jikinta yana cewa "Mimi! Are they found her? An ga lil Mysha?" Gyaɗa masa kai tayi tana ta ƙoƙarin mayar da hawaye,yace "where is she Mimi?" Kasa amsa masa tayi ta sunkuya ta ɗaukeshi duk girmansa ta nufi ƙofa za ta fita,Daada tace "Hoor! Za ki iya yi masa wankan nan kuwa? Ki kawoshi zan masa ki samu ki huta" ɗan dakatawa Hoor tayi kamar tana yiwa wani raɗa tace "zan iya Daada" daga haka ta fita,can part ɗinsu ta tafi a hanya duk rashin maganarsa sai tambayarta yake "Mimi Ina Lil Mysha? Me yasa ban ganta ba? Ba kin ce an ganta ba?" Ta gyaɗa masa kai tace "ehh! But" sai kuma tai shiru ta kasa cewa komai hawaye suna saukowa idonta,hannu bibbiyu yakai fuskarta yana share mata hawaye,kamar zai yi kuka yace "Mimi! Why are u crying?" Girgiza masa kai tayi tana ƙoƙarin tsayar da kukanta tace "nothing my dear.. I'm fine" a hankali ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta yana sauke ajiyar zuciya. Sosai babban filin gidan Sarki ya cika da mutane ƴan zuwa ta'aziyya,kou babba ne ya rasu ya samu mutanen da Mysha ta samu lallai za ai masa tsammanin ya dace da rahamar Allah,daga nan bayan an idar da sallah,gidan sarki na Nassarawa aka wuce da gawarta bisa umarnin Mai martaba Sarki Abduljalal,can aka binneta a gidanta na gaskiya,tunda akai jana'iza su Abba Waziri suka dawo gida suke karɓar ta'aziyya,babu wanda ya sake ganin fuskar Hamood sai dare guraren 10pm,lokacin gidan ya yi shiru saboda baƙi duka sun tafi babu me kwana sai ƴan uwan Hamood mata biyu Hafsah da Amina da ba ƙasar suke aure ba da suka zo. A hankali yake tafiya ya nufi ɓangaren Daada,ya ɗan jima suna magana kafin ya fito ya wuce gidanshi,kou da ya shigo ya tarar da gidan shiru bai iya neman Hoor ba ya isa master bedroom ɗinsa,cikin ƙarfin hali ya isa bakin gadonshi ya zauna ya riƙe kanshi,duk wannan abun da ya faru hawaye sili ɗaya bai zubar ba,duk yanda mutuwar Mysha ya girgiza shi,kusan zai iya cewa tsakaninsa da Hoor raba dai² sukai,Abuu Turab yafi sakewa da ita duk da Mysha ta kowa ce,amma tana sakewa da shi sosai duk da bai cika zama ƙasar ba saboda ba nan yake aiki ba,wani lokaci idan tana jin rigima sai tace a gurin Dad za tai bacci,sai dai Hoor ta haƙura ta bar musu ɗakin ta tafi ta kwanta ita kaɗai kou kuma ta kwana rungume da Abuu Turab,wannan shi ne abunda ya ƙara mata shaƙuwa da shi sosai² kuma yasa ta fahimceshi fiye da kowa. Wasa² tun ranar da Hoor taga Hamood a ɓangaren Daada lokacin da zai ɗauki gawar Mysha,da kuskure bata sake sashi a idonta ba,kullum gida ɗaya suke kwana su tashi,kawai dai idan ya fita sallah tun asubah bai dawowa gidan sai can dare ya tabbatar ta yi bacci,a fakaice ga duk me hankali zai gane wasan ɓuya Hamood ke yi da Hoor,idan ta tambayi Abuu Turab Dad zai ce mata ya ganshi a gurin Abba Waziri saboda yana fita yaje gurin Abba ya zauna,sai dai bai jimawa saboda mutanen da yake gani za kaganshi ya dawo yana neman Mimi,kamar maraya haka zai shigo mata da fuskar damuwa ya kafa mata tambayoyi akan inda aka kai Mysha ba ya ganinta,gidan duka an rasa me bashi amsa,kowa tausayinsa yake ji saboda kusancinsa da ƴar uwarsa,kusan babu wanda bai san yanda Mysha ke tsokanarsa ba. Shigowar Hamood kenan cikin gidan yana tafiya saɗaf² babu alamar footsteps ɗinsa kamar dai wani mara gaskiya,Hoor data rame sosai saboda damuwa da yawan kuka ta ɗaga kanta ta bishi da kallo,dama zaman jiran ganin shigowasa take kou da zai kai sulusin dare a waje,yau ta ƙudurce za ta jirashi,ita bata fahimci wannan sabon attitude ɗin nasa da ya tsiro mata ba tunda ya sauka garin,ajiyar zuciya ta sauke me nauyi kafin ta buɗe baki da muryarta da bai gama komawa dai² ba ta furta "barka da shigowa" kamar ba da shi take ba ya kama hanya yai wucewarsa,bata ji haushin rashin amsawar da baiba duk da ta san ya jita ta tashi ta tafi kitchen,abinci ta haɗo masa da duk abunda ta san zai buƙata ta wuce ta nufi hanyar bedroom ɗinsa,sai da ta fara yin knocking door ɗin kafin ta tura ƙofar ta shiga da ƴar sallama a bakinta,bata sameshi ba a ciki da alama ya shiga toilet,ajiye tray ɗin ta ƙarasa tayi tana ƙoƙarin tashi ya fito ɗaure da towel alamun da suka tabbatar mata wanka yayo,da kallo ta bishi ganin yanda ya ɗauke kai kamar bai san da kasancewarta a ɗakin ba,sosai jikinta yai sanyi kafin a hankali ta tashi ta nufeshi tana rausayar da kai muryarta a karye tana cewa "duk kwanakin nan ina kake shiga ba na ganinka?" Kamar ba da mutum take ba yai mata shiru ya ƙi tankata,batai fushi ba duk da haka ta kai hannu za ta karɓi towel ɗin hannunsa da yake goge jiki,da wani kakkausar murya yace "stay away from me please.. I'll do it myself,i don't need ur help.. In fact i need my own place" tsaye tayi tana kallonsa da shock,har ya wuce ya gama abunda zai yi tana inda ya barta,ko da ya gama saka night wears ɗinsa gadonshi ya nufa ya hau ya kwanta tare da jan duvet ya juya mata baya babu magana,ya dai yi mata irin maganar kurame ma'ana idan kin gaji da tsaiwa ki kashe min haske ki fita,mamakinsa sosai ya cikata ta dunga tausar kanta tana danne kukan daya tsaya mata a wuya,jiki babu ƙwari ta wuce dai² inda kanshi yake da sanyayyar muryarta tace "Hamood! Ga abinci na kawo maka baka ci ba kuma ka kwanta" idanunsa a kulle yace "i don't want anything now.." Tana gyaɗa masa kai tace "but.. I want to talk to u" a ƙagauce yace "speak up i'm all ears" muryarta na shaking tace "did i made a mistake? Shin na maka wani laifi ne da ba ka son yi min magana kou even kallona? Please tell me,what have i done to u da ya zama laifi?" Kamar me jira ya buɗe ido tare da tashi ya zauna ya jingina bayanshi da bed frame ya wani rungume hannayensa a ƙirji yana kallonta da soyayyun idanunsa,cike da isgilanci yace "ohh! Sai yanzu kikai tunanin kin yi wani abu? Shin har kin gaji?" Hawaye na ciccikowa idanunta tace "yes of course.. Na gaji ina son sanin abunda nai maka" yana kallonta right in the eyes yace "ok! Tunda kin gaji u can leave.. Kije gidanku na sakeki..."

       #A'ah! Me kuma yai zafi da ya kawo batun saki a nan? For business advert chat me up 08165726609..

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*


#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

WAZEER!Where stories live. Discover now