Chapter 2:Thriller

57 2 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2024.
*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*






                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*TIKTOK:ASLISMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.* 

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

*THRILLER..*
*BOOK 2.*

      •••Cikin wani irin ƙaraji Hamood yace "Wazeer! Ok² gani nan a hanya yanzun nan" bai jira me wanda ya kira zai sake faɗa masa ba ya kalli driver ɗinsa yace "yi maza ka shiga mota ka kaini gida" yanda Hamood yayi magana yasa da sauri driver ya amsa tare da zagayawa ya shiga mota,Hamood na kallon Safwa a ƙagauce yace "i'm sorry wife wani uzurin gaggawa ya sameni zanje gida,sai mun yi waya anjima kafin lokacin dinner" Safwa da wannan karon shi ne na biyu da ta taɓa jin sunan Wazeer kuma ta gane abunda yake nufi ta gyaɗa masa kai,a hankali tace "ok!" Yana shirin rufe motar ta ɗan yi dum da sauri tace "arghm.. baka ji ba" Hamood dake cike da gaggawa ya kalleta yana karya kai kamar maraya yace "wife please.. Later za muyi magana,i'm in hurry yanzun nan" tace "ok! But magana nake so muyi dama,ko nace tambaya gare ni da nake neman amsarta" Hamood yace "idan na dawo anjima sai muyi,yanzu dai ayi min haƙuri na tafi" ta gyaɗa masa kai kaɗan tace "shi kenan" yace "alright! Bye²" tace "bye.. Ka kula min da kanka" ya gyaɗa mata kai yana ɗan murmusawa yace "thank u.." Suna barin GRA da wani irin gaggawa Hamood ke yiwa driver ɗinsa magana ya ƙara gudu²,kamar za su tashi sama gudu kawai driver da Hamood ya gigita yake,cikin abunda bai wuce mintuna 5 ba suka iso Tudun wuzirci,kafin driver ya daidaita parking tuni Hamood ya buɗe mota ya sauko tare da nufar cikin gida,yanda yake tafiya zai tabbatar maka akwai wani abu,yana isowa apartment ɗinsu ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya shigo. Tsaiwa yayi yana kallon Wazeer daya juyo ya kalleshi,lokaci ɗaya muryarsa a karye ya furta "Son!" Tahowa Wazeer yayi zai fita,da sauri Hamood yasha gansa,yana masa wani kallo cike da damuwa yace "where have you been kwana biyun nan da suka wuce? Ina kaje daka bar gida? Mene ne na duk wannan Son?"


*

       Kallonsa Wazeer ya tsaya yi kamar bai gane me yake cewa ba,Dad yace "please Son.. Let's talk" cikin jin zafinsa Wazeer ya girgiza masa kai,wani irin ɓacin rai yana bijiro masa ya buɗe baki yace "me za kace min? Me kake da shi da zan tsaya naji?" Dad yace "amma yana da kyau ka saurareni kaji bayanin da zan yi maka,abunda ya faru wasn't intentional,sam ban san kana son yarinyar nan ba,ban san komai dake faruwa tsakaninku ba,ban san ya akai haka ta faru ba,amma ka yarda da ni wallahil'aziim.." Kafin ya kai ƙarshe Wazeer yayi ƙwafa ya wuce fuuu zai fita,saurin riƙo rigarsa Dad yayi yace "wait Son.." Cikin ihu da zafin rai Wazeer yace "don't call me ur Son.. I'm not ur Son,u better find ur Son somewhere,in ni ɗanka ne da gaske baza ka min abunda kayi ba.. Hummm! Wai ur Son,ain't u ashame of urself? Wait.. Da kace min mata mugaye ne azzalumai,masu son kansu,and what about u? Mene ne bambanci tsakaninka da su?" Ihu Dad da maganganun Wazeer sukaiwa zafi kuma ya ji su a bazata yayi tare da ɗaga hannu zai mareshi yace "Wazeer enough" Wazeer dake kallonsa idanunsa da jijiyoyin kansa sunyi raɗa² yace "ka barni na faɗi abunda ke raina mana.. Ko ba gaskiya na faɗa ba? Ain't ready to hear? Ba kai ka sanar min duk wannan ba? Don kawai kana jin haushin mahaifiyata sai laifinta ya shafeni? Shin mene ne Mimi ta aikata maka? Abunda kayi mata hukunci ne ko ɗaukar fansa? U took me ka bar Nigeria for good 20 years,ka taɓa tunanin ya kamata ka kawoni na ganta? Ka taɓa tunanin bai dace ka raba uwa da ɗanta ba? Ka taɓa tunanin cewa abunda ka aikata zai iya janyo min wani ciwon? Ka taɓa tunanin sanadin da yaja na samu depression? Ka taɓa zama kaji mene ne matsalata me nake so? I have been crying through this years saboda kewar Mimi,ina kuka saboda rashin Mysha,a kullum ina kewarsu ina yin kuka,through this years babu abunda zan ɗorar bayan kewa da damuwa,idan nayi maka maganar Mimi sai ka kawo min maganar da zaisa na tsani mahaifiyata,haka na shafe shekarun yarinta bani da single friend,u stole every bit of shekarun ƙuruciyata,sam ban san daɗinsa ba,ban san ya yake ba,ba ni da kowa dake so na,babu wanda yake zama da ni,babu wanda zan yi sharing farin ciki ko damuwata da shi,why? Me nayi maka?" Cikin kaɗuwa Hamood yace "but i loved u Son.." Da sauri Wazeer dake cike taf da ƙunci yace "u never loved me Mr Hamood Waziri.. This is kind of wickedness,baka san komai ba bayan son kai,da cika buri a rayuwarka.." Dad da ya zazzaro idanunsa yace "Wazeer! Ko ka yarda ko kada kayi ni mahaifinka ina sonka,idan babu soyayya me zai sa na tsaya maka a rayuwa? Na baka ingantaccen ilimi,na baka gatan uwa da uba,na maka kaza³" Wazeer na girgiza kansa yace "duk abunda kayi min ba don kana sona kayi ba,ka yi ne saboda ka cutar da zuciyar da taso ka da amana,zuciyar da ta yarda da kai ta baka amana,zuciyar da har gobe take shirye ta karɓeka,zuciyar dake da adalci,zuciyar da bata san komai ba face alkhairi.. Why are u so selfish Mr Hamood? Me yasa baka san kowa ba sai kanka?" Wannan karon Dad couldn't help it sanda ya ɗauke fuskar Wazeer da mari ji kake tass,Wazeer da al'amarin ya zowa a bazata yayi still yana kallon Dad bakinsa ya kasa rufuwa,cikin damuwa da ɓacin rai Hamood da bai so ya mareshi ba,in fact bazai iya cewa ga abunda ya janyo ya ɗaga hannunsa ya daki ɗan nasa ba,yana nuna shi cikin dakewar zuciya yace "don't dare dare call her name a gabana,i hate that woman.. Na tsaneta da gaske.. I hate her saboda ita taja na rasa ƴata" gyaɗa kansa Wazeer ya dunga yi yana kallon Dad,lokaci ɗaya yayi murmushi me ciwo yace "u slapped me yau saboda ƙiyayyar Mimi,ko kuma saboda cewar na faɗa maka gaskiya ne?" Dad yace "i slapped u saboda kana ƙoƙarin nuna min ban isa ba" Wazeer yace "this is not the truth,kace ka mareni ne saboda ƙiyayyar da kake yiwa mahaifiyata.. Ohh wow! I'm not surprise don ka yi haka,because dama can na san baka taɓa so na ba" cikin hargagi Dad yace "take it duk yanda kaso,amma ka sani duk duniya ni ne gatanka.. Ba ka da kamarni,kuma baza ka taɓa canja haka ba,baza ka taɓa canja ni da wani ba Wazeer,u are dependant,a ƙarƙashina kake,ni ne komai naka a duniyar nan,in kuma kana jin ka isa kace ba haka bane,sai na tabbatar maka da furucin da nayi" bai gama rufe bakinsa ba Wazeer yace "i said it out loud ba haka bane" Dad dake cikin shock yace "ok! Haka kace?" Wazeer yace "sure" Dad da yakai maƙura gurin ɓacin rai yace "tunda ka amsa min da bakinka,ka ƙaryata ni,ina so yanzun nan ka tattara ka fice min daga gidana" gyaɗa kai Wazeer ya shiga yi,lokaci ɗaya fuskarsa ta cika da murmushi me cike da ƙunci yace "ka koreni daga gidanka saboda na faɗa maka gaskiya?" Hamood yace "na koreka saboda ba ka da tarbiyya,har ni zan yi magana ka mayar min ba tare da tsoro ba? Who do u think u are Wazeer? Kai yaro ne wanda na raina cikin soyayya da kulawa,amma yau da ni kake sa'insa? Ina faɗa kana bani amsa,are we mate?" Wazeer yace "u said na bar maka gidanka,right?" Hamood cikin ihu yace "ka fice ka bar min gidana,babu ni babu kai tunda ban isa da kai ba" Wazeer yace "ok! Zan tafi and dama ba zama nazo yi ba" Dad da gabansa ke dukan 💯² yace "kuma ka tattara komai da kasan ya fito daga gurina,i so mean komao dana mallaka maka ka dawo min da shi,daga yau in ka isa kaje ka nema da guminka,ka yiwa kanka komai da nake maka,shi ne zan tabbatar da abunda ka faɗa,zan tabbatar cewa ka haifu,kuma ba ni Hamood Waziri ne mahaifinka ba.. After then u can leave my house for good.." Gyaɗa kansa Wazeer ya ci gaba da yi yace "deal.. But ina so ka sani,Allah shi ne gatana,kuma gatan kowane bawa.. All this years shi ya rayani na kawo yau.. Yanda ka furta ka tsani mahaifiyata a gaban idona yau sosai² yasa ƙimarka zubewa,and maganar in na isa na dawo maka da duk wani asset daka bani i will,yau ɗin nan zan bar gidanka kamar yanda ka nema,i know ba ni da sauran amfani a gurinka,so zan ƙarasa sauke maka nauyi na tafi,zan bar cikin rayuwarka saboda na zama annoba,but ina so ka ƙaddara,daga yau kuma daga yanzu duk inda za mu haɗu,ba na so ka nuna ka taɓa sanina,ina so ka goge duk wata alaƙa dake tsakaninmu,ka fiddani daga cikin rayuwarka,ka shafe duk wata alaƙa data taɓa haɗamu,nima zan manta cewar na sanka,i'm sure zan rayu cikin yardar Allah,but ni da kai ina so kowa yabi hanyarsa,hanyar jirgi daban na mota ma haka.." Yana faɗan haka ya shiga zaro key ɗin mota da sauran abubuwan da yasan sun fito daga Dad ɗin nasa ya ajiyesu saman couch,Hamood da bai taɓa zaton abunda maganarsa zai haifar ba kenan yace "Wazeer!" Wazeer bai saurareshi ba yana gama ajiyewa ya wuce ya nufi hanyar fita yana faɗin "na barka lafiya and for good.." Yana faɗan haka ya wuce cikin sauri ya fita zuciyarsa na masa ƙuna.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 06 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WAZEER!Where stories live. Discover now