Strangerlike

70 7 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               23

#Strangerlike

           Tas Wazeer ya ɗauke wuta a gurin,banda zafi babu abunda yake ji a jikinsa,gumi ya wani irin fara yanko masa,yana jin babu daɗi kuma yana son yayi magana but he couldn't,even ya buɗe baki ya kasa,Safwa tana dariya tace "kuma ka san har an tsayar da ranar auren in the next 2 months?" Wazeer ya runtse idanunsa sosai,lokaci ɗaya fuskarsa ya sauya,kamanninsa suka jirkice,face ɗin yayi wani irin ja,a rayuwarsa bayan mutuwar Mysha da rabuwar iyayensa da zai iya cewa bai ma gane me yaji ba a lokacin,tabbas bai taɓa shiga yanayi na tsoron rasa wani abu ba kwatankwacin wannan ba,sun ɗauki tsawon lokaci a yanayin shiru har sannan ya kasa magana,Safwa ta katse shirun ta hanyar aiko masa tambayar "when are u coming? Sai muje musu Allah ya sanya alkhairi?" Cike da ƙarfin hali da dauriya ya buɗe idanunsa da sukai jajir,ji yayi gaba ɗaya tunaninsa ya kulle ya kasa cewa komai,yana sauke numfashi me zafi kawai ya katse wayar ya ajiye tare da yin shiru,a hankali wani irin sanyi ya fara shigarsa,bai taɓa kallon ƴa mace da wani nufi ba,bai taɓa tsaiwa da wata ba tun tashinsa,ko a can California bai kula matan turawan nan,bama suga fuska ba bare suyi masa magana,maza ma ba shiga harkarsu ya cika ba bare wasu mata duk saboda khuɗubar Dad,mutumin da ba kowa ya sansa bama saboda yanda yake ɓoye kansa,kullum fuska rufe yake fita,da yawa basu san kamanninsa ba bare sunansa sai dai Mr mask,ko kwatancensa za ayi kana cewa Mr mask za'a san wa kake nufi,kaɗan ne suka san sunan Wazeer,suma dalilin Dad ne saboda nacinsu da son lallai sai sun yi mu'amala da shi,sababin ziyartarsa da suke gida yasa suka jiyo sunan,amma idan za ka shekara kana faɗan Aliyu,babu me ce maka ga shi,ita ya fara gani kuma zuciyarsa ta nutsu,har yaji yana son ya samu kusanci da ita,tun a kallon farko yaji zuciyarsa na masa waƙe akanta,yanayin fitar numfashinsa ya sauya,but kwatsam sai akai masa shigar sauri,shi bai ma san me zai yi ko yace ba akan maganar nan,ya tabbatar abunda yaji ɗin nan babu ƙarya ciki,amma ta yaya zai tabbatar da maganar Safwa? Duk da ya tashi wani ƙasar kuma cikin mutanen da ke da ƙarancin ilimin addini,ba zai ce bai yi karatu ba kwata² domin kuwa mahaifinsa shi ne malaminsa,duk wanda yasan gidan Waziri ya san gidan karatu ne,yana ji Safwa na sake kiransa ko kallon wayar bai ba bare ya iya amsa kiran nata,daren nan sosai yazo masa a hagunce,bai taɓa kawowa wani abu kwatankwacin wannan zai faru da shi ba,bacci kuwa sai dai in yana cikin nutsuwarsa,ko da ake cewa ɓarawo bai iya ya sace shi ba,haka ya kwana juye² da tunani,guraren asubah ana kiran farko tunani ya sakeshi,cikin yanayin mutuwar jiki ya tashi ya sauka gadon ya wuce bathroom,alwala kawai ya iya ɗaurowa saboda sanyi²n da yake ji da yayi masa kama da na wanda zazzaɓi ke son kamashi,ko masjid bai iya fita ba yayi sallah tare da yin addu'o'insa kafin ya ɗan samu nutsuwar zuciya,ya jima a zaune doing nothing banda tunani kafin yaja jikinsa da yai masa nauyi ya koma saman gadonsa ya kwanta,a hankali yana sauke numfashi ya lumshe idanunsa da suke azabar zafi,al'amari da yawa suka taru suka haɗe masa,nan da nan kansa yayi azabar ɗaukar charge,ganin damuwa na neman sawa ya fita hayyacinsa ya juya idanunsa da ƙyar,then a hankali ya tashi yasa palm a ƙafarsa ya fita bedroom ɗin,wani room da Dad ya mayar tamkar clinic ɗinsu ya shiga,bincike² yayi tayi yana hargitsa manyan kwalayen maganin da suke ciki,bai fita ba sai da ya gano abunda yake nema,ya fito ya wuce parlour ya ɗauko ruwa sannan ya koma bedroom ɗinsa,sai da ya rage gudun AC dake aiki ɗakin sannan ya ƙarasa gaban gadonsa ya  zauna a daddafe,maganin da ya ɗauko ya ɓallo ya watsa bakinsa ya korasa da ruwa,jijiyoyin kansa da suka firfito sun yi wani raɗa² a saman forehead ɗinsa,kana kallonsa za ka san he's not fine,a hankali ya wuce ya kwanta tare da lumshe idanunsa while hannunsa ɗaya yana kan goshinsa yana murzawa,ya jima a haka kafin wani irin wahalallen bacci yazo ya ɗauke shi a gurin.

WAZEER!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang