Envious 2

86 12 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

    

                               20

#Envious 2

*MUNIBA*

          Ko da ta baro gurin Abba kasa komawa downstairs tayi,jikinta a sanyaye tai shigewarta bedroom ta kwanta,maganganun da Abba yayi mata sosai suka tsaya mata a rai,duk motsin da za tayi sai ta sauke ajiyar zuciya,har zuciyarta taji tana son yin shawara da ko Baniynah ce saboda ba ta da kamarta haka itama,but wani gefe na zuciyarta ba ya son yin zancen kwata²,zuciyarta rawa yake sosai² akan al'amarin,bata taɓa yin saurayi ba,bata san yanda soyayya yake ba,duk wani abu da ta sani bai wuce tace ta karanta a novels ko ta saurara a some songs ba,ko da suka yi magana da shi yesternight bata taɓa kawowa da wuri haka yake nufin iyayensa za su zo ba,sam bata shiryawa fuskarta ko wane irin ƙalubalen da zai faru da ita daga family'nta ba,ganin komai take wani banbarakwai kuma as newest thing saboda wani abu kamar wannan bai taɓa faruwa da ita ba,mabanbantan labaran da taji daga bakin mutane suka shiga yi mata yawo a ƙwaƙwalwa,gefe ɗaya tana tunanin makomarta idan ta bashi dama,while wani gefen kuma na mata huɗuba akan opposition na abunda zai iya faruwa,ma'ana akan yaudarar samari,juyawa ta ɗanyi ta zubawa wayarta idanu,tunani daban² suna sake zuwa cikin kanta,tana son yin karatu amma yanayin da take ji a jikinta ya hanata yunƙurawa ta tashi,a hankali cike da wani irin mutuwar jiki ta kai hannunta ta janyo wayar tare da jefata a flight mode,tana buƙatar ta samu lokacin yin tunani da yanke hukuncin abunda zai dace da ita da rayuwarta,besides kuma ga exam dake sake tunkarota gadan² don tuni aka kafe musu timetable,amma tunani iri daban² sun hana zuciyarta samun nutsuwa,tana nan kwance wani irin baccin da bata shiryawa ba yazo ya ɗauketa. Kamar wasa tunda Abba yai mata maganar Lieut. Abuu Turab,da kuma ganin Mami bata ce mata komai ba,and za ta iya cewa ya samu automatic karɓuwa gurin iyayen nata da family,sannan ta fahimci inda nasihar da Abba yayi mata ya tafi,kawai tayi zero wa mind ɗinta za ta amshesa da hannu bibbiyu,but not now,kawai dai ta yanke shawara akan baza ta fara bashi dama a yanzu ba har sai ta kammala papers ɗinta,tana yawan jin labarin yanda soyayya ke dagulawa mutane lissafi,akan burinta baza ta so wani abu yazo ya shiga tsakaninta da muradinta ba,gara koma mene ne zai faru idan ta kammala exams ɗinta ta samu break sai ta fuskancesa da dukkanin zuciyarta. Ranan Monday kamar yanda yake a tsare suka fara paper ɗinsu,abun kamar wasa within 2 weeks suka ƙare,ga mamakinta har zuwa lokacin Lieut Abuu Turab bai zo ba,bai kuma kira ko da Baniynah ya tambayeta ina take ba,though Abba ya sanar mata sun bashi dama yazo suga juna,kuma ita kanta bata taɓa kawowa za'a ɗauki lokacin nan ba tare da ya zo ba ko ya kira wani nata yaji lafiyarta ba,mutumin da yake abu kamar yana jiran ƙiris,duk yanda al'amarin ya bata mamaki,haka nan pressure ɗin exam da stress suka sa ta mantawa sam da batun. Fitowarsu kenan daga exam hall,a mugun gajiye suka wuce carline bayan sun yi sallama da wasu friends ɗinsu daga nan suka wuce gida,sanda suka shigo kasancewar safiya don bai wuce 10am ba,shiru ɗin da suka tarar da gidan shi ya tabbatar musu babu kowa sai su kaɗai,ko upstairs basu iya zuwa ba suka baje nan a parlour,babu ɓata lokaci wani irin baccin gajiya ya kwashesu,Baniynah dake cewa da sun dawo za su tafi can gidansu su yiwa Mama hutu,ba su suka farka ba sai past 3pm kuma tun 10am suka shigo gidan,kasancewar Friday yasa basu san ma lokacin sallah ya yi ba,a gurguje sanda suka tashi sukai sallar zhuhur,suna idarwa suka hau shirin tafiya,after sun gama abunda za suyi tas suka tsaya sukai sallar asr sannan suka fito,lokacin suna nufar parking spot Muniba da ta ɗan faɗa saboda rashin samun bacci ta shiga kunna wayarta,yana gama booting texts suka fara shigo mata,ba tare da ta tsaya dubawa ba suka shiga mota suka bar gidan,few minutes drive ya kawo su line gidan Uncle ɗin nata,suna isa get tayi horn Baba me gadi ya fito ya buɗe musu,sanda ta tsaya suka gaisar da shi a mutunce yayi musu barka da zuwa,sannan suka shiga ciki tayi parking suka sauka,a parlour suna yin sallama Mama ta amsa fuskarta da fara'a tace "oyoyo ƴan makaranta.. Ai na yi tunanin kun fasa zuwar mana hutun da naga yamma yana neman yi" Muniba data tsuguna kusa da ƙafafuwan Mama a saman rug tace "bacci muka yi da muka dawo,bamu jima da tashi ba.. Ina yini Mama?" Mama tace "lafiya lau alhmdllh,ya exams da mutanen gidan? Kun baro su lafiya?" Muniba tace "lafiya lau.. Basu dawo ba ai muka fito" Mama tace "Allah sarki! Rabbi ya taimaka ya bada sa'a,ya yi muku jagora" Muniba ta amsa,sannan Mama ta amsa gaisuwar Baniynah,hira suka ɗan taɓa akan some al'amuran rayuwa kafin tace "ku tashi maza kuje ku samu ku ci abinci tukuna,yana nan a dining tunda kukai waya za ku zo nai muku girki,shiru² ina ta zuba ido ni kaɗai kuma nace Allah yasa ba fasa zuwa kukai ba,ga shi na yi riga malam masallaci,maimakon na jira har na ganku tukuna,na fara ɗaura sanwa ta ku" Muniba tayi dariya tace "a'a Mama bamu fasa ba" Mama tace "ehh tunda na ganku yanzu kam ai hankalina ya kwanta.. Kuje ku ci abinci dai,sai muyi hirar sosai na yaushe gamo" Muniba tace "ni dai ba yanzu ba Mama" Mama ta kalli Baniynah tace "ke fa Inna Mairamu?" Ai basu san sanda suka kwashe da dariya ba,Baniynah tace "Allah Mama babu daɗi sunan,wani iri kamar za ki kira tuwon ƙauye yazo" Mama tace "a'ahhh! Babu ruwana ke da Abbanku,ko tambayata yayi zance ban san anyi ba" wayar Muniba ne ya hau ruri,da sauri ta kalli ƙaramin handbag ɗinta,kafin wani yayi magana ta fito da wayar,sunan Husniyah da ta gani saman screen ɗinta yasa tai saurin ɗauka tayi sallama,Husniyah ta amsa da faɗin "Aunty ina yini?" Muniba ta amsa cikin ƴar kunya tace "lafiya lau dear,ya Mom da su Sis Abrar?" Husniyah tace "lafiya lau Aunty.. Yanzun nan mun zo gida security suka ce kun fita not too long,nace bari na kiraki ko zan sameki,kwana biyu idan mun kira wayarki is off,yanzuma gwadawa dai nayi na sanar miki,so za mu juya gida sai wani lokacin" Muniba ta ɗan waro idanunta kaɗan tace "laaa! Ba nisa muka yi ba,gamu a gidan Uncle ɗina" Husniyah tace "gidansu Yaa Khalidah koh?" Muniba tace "yeah! Nan" Husniyah tace "alright! Bari mu ƙaraso,mun fito ne muka ce za muzo gaisheki,kwana biyu muna ta kiran wayarki ba'a samu,mun tambayi Yaa Abuu Turab kuma shi ne ya sanar mana kina exams" Muniba ta ɗan gyaɗa kanta tace "sure.. But alhmdllh i'm done today" Husniyah tace "Allah ya bada sa'a Aunty,bari muzo nan ɗin mu gaisa" Muniba tace "kin san gidan ne ko na turo miki address?" Husniyah tayi ƴar dariya tace "laaaa! Aunty har da mu fa aka zo ɗaukan amarya" Muniba tace "ok dear,sai kun iso" tana sauke wayar ta kalli Baniynah da faɗin "Sweet su Husniyah ne suka je gida bama nan" Baniynah tace "Allah sarki ai na ji kin ambaci sunan Abrar" Muniba tace "ehh! Amma Gasu nan ƙarasowa ma" Baniynah tace "Allah ya kawo su lafiya" Muniba tace "ameen" lokaci ɗaya kuma ta kalli Mama tace "Mama muna da baƙi" ba tare da Mama ta tambayeta su waye ko yaya suke da su ba tace "to daughter Allah ya kawo su lafiya" Muniba ta amsa,ba'ayi 5 minutes ba sai ga su Husniyah sun yi knocking,Muniba ta tashi tana cewa "i think sun iso" ta tafi gaban entrance,tana buɗewa ta gansu su biyu tsaye ita da Abrar,murmushi sukai wa juna kafin ta furta "sannunku da zuwa" suka amsa mata suna rungume juna,Muniba tace "bismillah ku shigo" Abrar tace "Aunty tare muke da Yaa Hammad fa,ya ma ce mu faɗa miki yana mota za ku gaisa" Muniba tace "alright! Bari na sanar da Mama sai naje mu gaisa" Husniyah tace "mu shiga mu gaisa Abrar" Muniba tace "amma ba dai har tafiya za kuyi da wuri ba ko?" Husniyah tace "a'a! Za mu fara gaisawa da Mama dai" Muniba tace "ok!" Sallama sukai suka shigo cikin parlon,Mama da Baniynah suka amsa cikin sakin fuska sukai musu sannu da zuwa,Husniyah da Abrar suka amsa suka zauna tare da gaisar da Mama,a mutunce Mama da ta shaida fuskokinsu ta amsa tana tambayarsu mutanen gida,after then suka tashi za su fita Mama tace "ba dai har tafiya za kuce za kuyi ba daga zuwa?" Husniyah tayi murmushi tare da girgiza kai tace "a'a Mama.. Za muje gurin Yaa Hammad ne suna mota suna jiranmu za su gaisa" Mama tace "a'ahhh! Ku kirasa ya shigo ciki don Allah,bari na baku guri ku gaisa,ai gida kuka zo ba baƙon guri ba" Husniyah ta kalli Abrar tace "to Mama bari dai muje,ba lallai ya amince ya shigo ba,and ba shi kaɗai bane" Mama tace "to babu komai" Muniba tace "Sweet zo muje mu gaisa" Mama ta tashi tayi sama abunta tana cewa "Baniynah kice su shigo ciki" Baniynah tace "to Mama" tare suka fita su huɗu suna ƴar hira har suka kawo parking spot gurin da motar yake,maimakon su tsaya driver side sai suka bi ta gefen me zaman banza,da yake tinted glass ne da motar yasa ba'a ganin na ciki,haka kuma yasa Muniba basu kawo komai ba,Husniyah tayi knocking glass ɗin wanda ke ciki ya saukesa,da zuciya ɗaya Muniba ta ɗago kanta tana kallon wanda ke cikin motar gabanta ya wani irin faɗi.

WAZEER!Where stories live. Discover now