Beseech

82 8 1
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

        '''Wishing myself the happiest of birthdays.. On this special day,i just want to thank Almighty Allah for the priceless gift of life that He has given me and for the wonderful people He has put in my life.  I'm a happy celebrant today! Happy birthday to me.. Happy birthday to me! Happy birthday dear me..'''🥂🎂🦋

                               21

#Beseech

      Lokaci ɗaya mood ɗin Safwa ya sake canjawa,Wazeer dake kallonta ya ɗan lumshe idanu kamar bai san me ke faruwa ba,cikin gajiya da magana yana yatsina fuska yace "an min rowan digits" Safwa tayi shiru ta kasa cewa komai,bata manta maganar da suka yi da shi ba akan number Muniba da ya tambayeta ranan,ɗauke kansa yayi tare da sake lumshe idanunsa,for about 3 minutes babu wanda ya sake magana,can a hankali ya buɗe idanunsa da kyau ya kalli Safwa da tayi shiru tana kallon motar Abba da ya shigo gidan yayi parking ƙasan tent,ana kashe motar Mubasshir ya buɗe ya sauko daga front ya buɗewa Abba dake back seat,yana fitowa ya kallo balcony sai kuma taga sun tsaya suna magana,tunda suka sauko motar Safwa ke kallonsu gabanta na ɗan faɗuwa,duk da bata san me suke magana akai ba amma haka nan taji ta tsargu,for about 2 minutes kuma sai Abba ya wuce ya nufi get driver ya sauko daga motar ya rufa masa baya,while Mubasshir kuma ya nufo balcony fuskarsa a haɗe yayi musu sallama ya wuce ya nufi entrance,Wazeer dake kallon Safwa ta gefen ido ya amsa tare da ɗago kansa da niyyar su gaisa da Mubasshir,sai dai bai samu damar hakan ba don ya riga ya shige,ɗan gyara zamansa yayi kafin ya buɗe baki kamar yana magana da kansa yace "tunanin me kike?" Maganarsa ya taimaka wajen dawo da ita hayyacinta,ta girgiza kai tana ƙirƙiro murmushin da iyakacinsa saman lips ɗinta tace "babu komai" yace "are u sure?" Ta gyaɗa masa kai tace "yap!" Ya ɗan taɓe baki yana kauda kansa yace "ok! I think zan wuce yanzu" tana gyaɗa masa kai tace "ok!" Yace "sai wani lokaci,a gaida Mom" tace "za ta ji" tana sakin murmushin da kamar don dole take yinsa,miƙewa suka yi kusan tare tace "muje na maka rakiya" yace "oh no! Ba sai kin wahala ba,thanks" tace "alright! Na gode sosai da ziyara" ya gyaɗa mata kai yana sauka balcony yace "sai mun yi magana" daga haka ya wuce cikin ɗan sauri,Safwa na tsaye gurin tana kallonsa har ya kai get,yana fita gidan ta ɗauki tray ɗinta ta fito zuwa gida ranta babu daɗi. Tana yin sallama parlour Umma ta ɗago tana kallonta tace "me zan gani?" A kumbure cike taf da haushi Safwa tace "ya tafi" Umma tace "to ya ci abincin?" Zama Safwa tayi jagwab tana kyaɓe fuska tace "a'a bai ci ba" Umma tace "me ya faru to na ganki haka wani iri?" A hankali ta zame ta kwanta saman kujera tana kallon tray data ajiye ta kwashe labarin komai ta sanarwa Umma,Umma tai tsam da ranta tace "toh ni yanzu abunda ban gane ba,ke ya sani ko ita Munibar? Sannan cikin ku biyu wa yake so da yake tambayar number ta bayan yana da taki?" Safwa tace "ni ya sani,amma ni gani nake kamar so yake yace min yana sonta,which is abunda bazan bari ya taɓa faruwa ba,dama tun ranan da ya tambayeni number ɗinta nake zargin haka.." Umma tace "toh! Yanzu na fahimceki,amma me yasa tun farko kema kika nuna masa Munibar? Sakancin da kika fara yi kenan,ke baki san ko miji ne da kai a yanzu ba'a nuna masa ƙawaye ba bare koɗa halayensu a gabansa?" Faɗa sosai Umma tai mata tana faɗin "ko don gaba kada ki kuskura ki ƙara bari ba saurayinki kawai ba koma waye ya san wata ta dalilinki,don haka za'ayi ta yi miki ƙwace da fin ƙarfi kina kallo babu yanda za kiyi" Safwa ta gyaɗa kai ranta a jagule tace "toh Umma yanzu ya za'ayi ni wallahi sonsa nake tun sanda na fara ganinsa,shi kuma ya bijiro da maganarta" Umma ta kalleta tace "a'a babu wannan maganar,ki sha kuruminki ke dai kawai zan san abunda za'ayi akai,amma ko da zai sake yi miki maganarta,kada ki nuna masa ba kya maraba da alaƙarsa da ita,kiyi ta lallaɓasa har mu san nayi" Safwa ta gyaɗa kai tace "toh! Amma Umma bazan sanar da Aunty Hilda ba?" Umma ta girgiza kai tana faɗin "a'a ba sai kin kirata ba,ai wannan aikin bai fi ƙarfina ba nima,akwai warce na sani dake bada taimako kan irin wannan matsalar,Hjy Baturiya ta haɗani da ita,in Allah ya kaimu zan kirata na sanar mata abunda nake so ayi,ba dai kina sonsa ba?" Safwa tai saurin gyaɗa kai a shagwaɓe tace "ehh Ummana!" Umma tace "shi kenan an gama.. Za kiga abunda zai faru,ke dai za ki sha mamaki.. Shi da sake tuna wata Muniba bare yayi maganarta sai idan kin so" Safwa tai zumbur ta tashi zaune tana washe baki tace "da gaske Umma?" Umma tace "ahaf! Kuma dai ba ni na faɗa miki ba? Ke dai tsaya nan kiyi kallo" Safwa tayi ihun murna tace "wayyo Allah daɗi,ai kuwa wallahi Umma da kin gama min komai idan kika sa hankalinsa ya karkato kaina,don baki gansa ba kyakkyawan gaske,na aureshi na gama yin sa'a wallahi,don kaf cikin friend ɗinmu babu wanda ta auri haɗaɗɗe kamarsa" Umma tace "shi kenan.. Tashi kije maza ki kai kayan can kitchen kafin Babanku ya shigo ya dasa min tambayar wannan mene ne? Na waye?" Safwa tayi dariya tare da tashi ta wuce kitchen da tray ɗin data shigo da shi,tana fitowa ta wuce sama tana kiran number ɗinsa taji ko ya kai gida. Not too long ago da tashinta Baba ya shigo da sallama fuskarsa babu walwala,bayansa Awwal ne da Bilal ɗauke da manyan ledoji,Umma data ɗago ta kalleshi sanda yasa taji shakkarsa,ta daure ta amsa da faɗin "sannu da zuwa Baban Bilal" yace "yawwa!" Yana kallon yaran da suka nemi guri suka zauna,then ya sake kallonta tare da jefo mata tambayar "ina Safwa?" Umma tace "tana sama ɗakinta,yanzun nan bata jima da barin nan ba" Baba ya kalli Umma sai kuma ya wuce sama yana cewa "kice mata tazo ta sameni ina son ganinku ke da ita yanzun nan a ɗakina" Umma tai kasaƙe tana faɗin "lafiya dai Baban Bilal?" Baba bai tsaya ba yace "kuzo ku sameni ina son magana da ku" Umma ta gyaɗa kanta tace "toh shi kenan gamu nan" ta dafa kujera tare da yunƙurawa ta miƙe,bata bi ta kan su Awwal ba ta wuce tabi bayansa,tana hawa sama ta ƙwanƙwasa ɗakin Safwa tare da kiranta "Safwa!" Safwa dake kwance tana chat happily tace "na'am" Umma ta buɗe ƙofar daga bakin ƙofar da take tsaye tace "kizo Babanku na kira" Safwa ta tashi da sauri tana zaro ido tace "ni kuma? Ya dawo ne?" Umma tace "sun shigo yanzun nan,da alama sun je wani waje ne da su Bilal" Safwa ta dafa ƙirji cikin zullumi tace "na shiga uku,me nayi?" Umma tace "toh taya za ayi ni zan sani? Ki taso muje maza kada kisa faɗansa ya shafeni" Safwa ta taso da sauri gabanta na wani irin tsinkewa,duk abunda take ba ta mantawa Babanta na iya taka mata burki,baiƙi yasa bulala ya zaneta ba,dan bai da wasa ko kaɗan,a baya tabi Umma har ɗan madaidaicin ɗakinsa,suna shigowa Baba ya ɗaga kai ya bisu da kallo ita da Umma,Safwa ta raɓe gefen kujerar da Umma ta zauna tana faɗin "sannu da zuwa Baba" a daƙile yace "yawwa!" Umma dai kallon Safwa kawai take,ita kanta duk ƴan abubuwan da take don ta shawo kansa a wasu lokutan takan ji shakkarsa,Baba na kallonsu fuska babu wasa yace "yaushe Safwa kika fara tsaiwa da samari ban sani ba? Did i gave u chance ko damar kula wani namiji bayan ƴan uwanki su Awwal da ni nan mahaifinki?" Safwa tayi shiru saboda yanda maganar yazo mata bagatatan,Baba ya juya ya kalli Umma ransa ɓace yace "Maman Safwa kin san yarinyarki na kula samari har ta kai su wani gidan saboda kada na gani ko kuwa kema baki sani ba?" Umma ma tayi shiru,Baba da shirunsu ya fusata yace "zancen banza zancen wofi,ina magana kun yi min shiru dukanku,me kuke nufi? Da saninku kenan komai yake faruwa,ni ubanta aka rufe har sai maƙota ne za su tareni su sanar min abunda ke faruwa a gidana?" Kallo ɗaya za ka yiwa Safwa data kasa kallon Baba ka san a tsorace take,Umma ta karyar da kai kaɗan cikin sanyin murya kai baza kace ta iya hayaniya da ɗaga murya ba idan tana magana tace "ayi haƙuri Baban Bilal.. Amma ban katse maka hanzari ba,a ganina yanzu a shekarun Safwa idan bata tsaya da saurayi ba sai yaushe? Ba tun yanzu ba ake ta yiwa sa'anninta aure,wasu na gidajensu har da rabon haihuwa,idan ba ta tsaiwa ƴar hiran nan,a ina za ta samo mijin aure? In da ace a ƙauye ne yanzu tuni tana da ƴaƴa 3-5,kuma kai da kanka ka sha faɗa min dangi suna ta tambayar yaushe ne aurenta? Na san cikin abokan wasa kuwa baza'a rasa masu yar maka magana akan ta yi nauyin jini ba" Baba yayi tsam yana sauraren maganganun Umma,cikin kwantar da murya tace "ya kamata a duba maganata ranka shi daɗe,ba da wata mummunar manufa nima na goyi bayan ta tsaya da saurayi yanzu ba,illa dai fatan ace ta samu mijin aure mu kawar da ita daga gabanmu" Baba ya ɗan gyaɗa kai cike da gamsuwa kafin ya nisa yace "ban ƙi ta maganganunki ba,amma me yasa idan za tayi zancen baza tayi a ƙofar gidan mahaifinta ba sai ta tafi can gidan mutane? Ni ban isa da gidana bane? Ko kuma raini da kuma ban isa nasa doka abi bane sai dole an karya? To ni bana son haka,idan an raina arzikina ne sai naji,amma kada a sake raina ya ɓaci,zance ne tunda kin kai munzali za ki iya yi,amma ki san da su waye² za ki tsaya,ba ko wane kalar namiji za ki kawo min gida ba.. And daga yau kada wani abu ya sake faruwa ace sai a waje zan ji,idan ba haka ba rai zai ɓaci,am i clear?" Safwa tai saurin kallon Umma ta kasa magana sai ɓari bakinta da jikinta suke,Umma ta gyaɗa kai tace "ai haka ma bazai sake faruwa ba,kuma ko kusa ba raina arzikin gidansu tayi ba,tana dai zuwa can ɗin ne saboda gudun ka ganta kai mata faɗa" Baba yace "to daga yau duk wanda yazo ki kawosa gidanku,kina jina ko?" Da sauri Safwa tace "to Baba" yace "tashi ki tafi,Allah ya bamu alkhairi" tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta miƙe da sauri tace "sai da safe" Baba yace "Allah ya kaimu lafiya" a hankali tace "ameen.. Umma sai da safe" Umma tace "Allah ya kaimu.." Safwa na fita ɗakin Abba ta tsaya tare da dafe ƙirji ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya,wani irin farin ciki ne ya mamaye duka zuciyarta,badon komai ba sai saboda samun damar zance data samu daga mahaifinta,da tana yi ne a ɓoye saboda gudun abunda zai faru,amma yanzu za tayi me licence tunda baba ya cire takunkumin daya sa mata,sai dai abu ɗaya zuwa biyu ne bata ji daɗinsa ba,yanda Baba yai maganar duk da bai fito ya faɗi wanda suka sanar masa ba,ta tabbatar bazai wuce Abbansu Baniynah ba,shima kuma ba wai haushinsa taji ba,tunda ga shi a dalilinsa ta samu damar tsaiwa da ko waye babu shakkar wani abu zai faru,abunda bata ji daɗinsa ba a duka maganar shi ne hanata yin zance da Baba yayi ba'a gida ba,amma babu komai hakan ma da ta samu har ya amince,za ta ci gaba da lallaɓawa amma underneath ta ƙudurce ba kowa za ta bari yazo gidansu ba,saboda akwai wanda take ganin kamar idan ta kawo su tace nan ne gidansu ajinta zai zube.

WAZEER!Where stories live. Discover now