Safwah

98 12 4
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               24

#Safwah

          Kyakkyawan mutumin dake tsaye yana mata murmushi ta ɗan bi da kallon ƙurilla,ba yaro bane daga ganinsa,but akwai jin daɗi tattare da shi wanda kana kallonsa babu buƙatar sai wani ya sanar maka,a hankali take tunani da tambayar kanta "a ina na san me wannan fuskar?" Sai dai ta kasa tunawa,can kamar wanda akaiwa alluran tunawa ta gano mutumin da ta taɓa gani a mota da jimawa sosai² yana ta kallonta,sake ɗan kallonsa tayi har sannan bata yi magana ba,tsadadden suite ne jikinsa brown color,kana kallon skin ɗinsa da yayi luf² da wani gargasa wanda hutu ya gama jiƙawa za ka san akwai masu gidan rana,sai dai duk ƙwaƙwarka baka isa kace ga shekarunsa ba,saboda gayu da jin daɗi sun gama ɓoye hakan a tattare da shi,ganin Safwa ta tsaya though bata yi magana ba,yasa ya ɗan yi taking steps gurin da take tsaye yace "assalamu alaikum" Safwa dake ƙifi² da ido ta amsa,kwarjinin da yayi mata yasa tace "ina kwana?" Ya amsa yana ɗan dai²ta tsaiwarsa fuskarsa a sake yace "if babu damuwa za mu iya yin magana?" Safwa ta gyaɗa masa kai tace "babu!" Yace "alright! I'm Muhammad Hamood Aliyu Waziri.. Na san kin san gidan Wazirin Kano,right?" Ta gyaɗa masa kai da sauri,tun farko data ɗora idanunta akansa komai ya canja mata,lissafinta ya fara neman sauyawa,bugun zuciyarta ya ƙaru,a duk lokacin data shaƙi daddaɗan ƙamahinsa ji take kamar ba'a duniya take ba,yanzu ko da taji sautin muryarsa sai taji wani yanayi ya saukar mata,duk da bata tantance mene ne shi ba ko me hakan yake nufi,yace "na ganki ne some minutes ago,so babu yanda za'ayi na iya yi miki magana saboda bama kusa,and idan kin tafi kuma ban san where zan samo ki ba,like wancan lokacin" Safwa ta sake gyara tsaiwarta tana buɗe ido da kyau cike da mamakin yanda aka yi ya ganeta,tace "Allah sarki.." Underneath tana faɗin "wayyoo Allah ni Safwa ɗan gidan Waziri ne fa,ai daga gani ma ba sai ya yi bayani ba suna da kuɗi" yace "it seems like u are in a hurry?" Tace "yeah ina da test ne" yace "ok! Bari na barki kiyi test,but zan iya jira har ki fito muyi magana?" Safwa ta waro idanunta waje tace "a kan me?" Yace "saboda ban sanar miki abunda ya kawo ni ba" Safwa tace "a'a gaskiya kayi tafiyarka" yace "u don't want me to stay?" Tace "ina da lectures ne gaskiya,kuma ni ban san me za kace min ba,in fact banma sanka ba yau na taɓa ganinka,Babana kuma a nan yake aiki idan ya ganni ko ya samu labarin na tsaya da wani zai min faɗa" yace "ko dai kina tsoron kula strangers ne?" Ta gyaɗa kanta da sauri underneath tace "ni duk ba wannan ba,ka amshi digit ɗina kawai" a fili kuma sai tace "ehh" yace "ok! Ki bani digits ɗinki sai nazo gidanku na ganki muyi magana,i think u will be safe and comfortable with me a nan ko?" Har zuciyarta sai da taji kamar ta buga tsalle tare da yin ihun murna,while a fuskarta kuma ta nuna kamar ba ta son bada number ɗinta,yace "please My dear,ba zan cutar da ke ba,ban kuma zo miki da wasa ba" Safwa ta gyaɗa kanta kaɗan tace "ok!" Tsadadden wayarsa da ko a labari bata taɓa ganin irinsa ba ya miƙo mata,hannunta har rawa yake ta karɓa tasa masa number ɗinta,underneath sai zancen zuci take tana faɗin "wallahi me kuɗi ne" tana miƙa masa wayar ya amsa yace "what name zan yi saving?" Tace "Safwah!" Yayi ɗan murmushi yace "nice meeting u dear.. Allah ya bada sa'an test" tace "ameen.. Thank u" yace "ok! Bari mu wuce sai mun yi waya ko?" Ta gyaɗa kanta tace "Allah ya tsare hanya" ya amsa tare da yi mata sallama ya wuce. Tana juyawa ta wani ƙwalo ido waje daɗi duk ya gama rufeta,ji take kamar za ta tashi sama,sai kuma ta fara ji kamar tai tsuntsuwa taje ta sanar da Umma,ba komai ya ɗauki hankalinta kamar kuɗinsa ba,musamman da taga ba shi yake driving da kansa ba,ai kuwa yanzuma baza tayi ƙasa a gwuiwa ba za ta sanar mata ta waya,tana tafiya a hankali ta waigo sai taga motarshi ya juya though bata sani ba shi yake driving ko kuma driving ɗinsa ake kamar wancan lokacin,a hankali ta sake yin murmushi kafin ta tura hannu cikin jakarta ta fito da wayarta,number Umma ta shiga kira,Umma na ɗauka tace "hello Safwa! Ya ya akayi? Kin isa makarantar?" Safwa cikin ɗoki tace "Ummana albishirinki?" Umma tace "me yake faruwa?" Safwa tace "ke dai Umma ki amsa min" a saɓule Umma ta amsa "goro.." Safwa tace "wani mutumi ne ya biyo ni yanzun nan har school,Umma kin ga motar da yake ciki? Kin gansa kuwa? Wallahi me kuɗi ne,kuma ma ɗan gidan Waziri ne shi" Umma dake saurarenta tace "alhmdllhi! Irinsu nake ta miki fatan ki samu ai,ince dai kun yi musayar lambar waya ko? Bai tafi haka nan ba?" Safwa tace "ya karɓa" Umma tace "toh shi kenan mun gode Allah,sai kin dawo ma yi maganar.. Kun yi test ɗin ne?" Safwa tace "a'a yanzun nan ai muka rabu da shi,ban ma shiga class ba ina hanya ne" Umma tace "to babu laifi sai kin dawo" Safwa tace "to Ummana.. Yawwa Umma yau Aliyu ya ce min zai zo" Umma tace "toh shi kenan sai kin dawo dai" Safwa ta amsa ta katse wayar. Around 2pm ta fito lectures,tare da wasu cikin student abokan karatunta suka fito suna tafiya suna hira har suka kai get,nan kowa ya nemi tricycle da zai yi hanyarsa ya shiga,tunda ta kamo hanyar gida take tunani da sakin murmushi,gaba ɗaya yinin yau da tayi a school ba ta da aiki banda na tunanin Hamood Waziri,lokaci² kuma tana duba wayarta,she's expecting his call amma ko new number ɗaya bai kirata ba,dai² street ɗinsu ta sauka bama ta bari yau har sai da suka shiga ciki ba,ta bashi kuɗinsa yaja machine ɗinsa ya tafi,itama ta wuce gida cikin wani irin yanayi,tana yin sallama Umma ta amsa da fara'a tana faɗin "an dawo?" Safwa tace "ehh! A gajiye nake wallahi" Umma tace "to ai sai aje a huta" Safwa tace "yanzu zanje na kwanta na samu bacci" Umma tace "sai kin tashi za ki bani labarin mutumin?" Safwa ta ɗan ɓata rai tace "Ummaaaaa!" Umma tace "ah'ah! Yo ai baki sanar min yanda kuka yi ba naga" Safwa tace "Umma ba fa yaro bane,kawai dai yana da kuɗi,ni abunda yasa ma na tsaya kenan har mukai exchanging digits,wallahi kuɗinsa ne suka tafi da ni,don baki ga motar da yake ciki ba" Umma tace "ban fahimceki ba Safwa? Kina nufin bai miki bane ko kuwa yaya?" Safwa tace "don yi gaskiya bai da makusa,kawai dai ni na fi son na auri matashi,wannan fa Allah yana da mata,ni bana yiwa kaina fatan auren mijin kowa gaskiya,na fi son na auri nawa.. Kuma ga Aley ma me zan yi da babba?" Umma ta saki baki tana kallonta tace "ke dai kam amma an yi wawuya wani lokacin,ke fa da bakinki kika ce Aliyun har yau bai san kina yi ba,tunda haka ne yanzu kin samu wani ai sai ki bashi dama kiga me zai faru,kuma Allah na tuba yaron da kike magana,ai da shi gara ki samu ubansa,shi babba advantage ɗinsa shi ne da kuɗinsa,duk abunda za ki ganshi da shi nasa ne,mallakinsa ne guminsa da wahalarsa ne,amma shi kuwa yaro nema yake" baki Safwa ta turo tace "ni dai duk da haka ina sonsa a haka,kuma wallahi ban ƙi nayi komai akansa ba" Umma ta buɗe baki tace "to shi kuma wannan fa ki kaisa ina?" Safwa tace "ni kuɗinsa kawai nabi,zan ci rabona na sallamesa" Umma tace "amma wannan ƴa kina da abun mamaki" Safwa tace "me nayi to kuma?" Umma tace "don ubanki ba haka ake yi ba,in dai ya fi Aliyu kuɗi ni dai ban damu da tsufarsa ba,ki kawoshi gida suyi magana da Babanku,cikin ƴan kwanaki ba kawai sai dai kowa yaji ana ayyiriri ba,nima zan aurar dake ki tafi gidanki,sai kuma muji da ƴan uwanki kafin su girma lokacinsu yayi suma" Safwa tace "kaiiii! Gaskiya ni dai Umma a'a kada ma ki fara wannan maganar" Umma da haushi ya ciyo tace "don ubanki ba ke kika kawo min zancensa ba? Ni da ina nan gida ban san kun haɗu ba,don na baki shawarar yanda za kiyi sai kice min ba haka ba? To ai shi kenan sai kiyi yanda kika ga ya yi miki" Safwa ta tashi tana kumbure² tace "bari na hau sama" Umma tace "ki shiga ƙarƙashin ƙasa ma daga can in kin so" Safwa ta kalli Umma ganin yanda ta haɗe rai tace "to Umma ai ba cewa nayi fa bazan kulashi ba" Umma tace "ke kika sani kuma,ni ba ni guri kada kisa raina ya ɓaci" Safwa tace "Allah ya huci zuciyarki" Umma dai bata kulata ba ta ɗauke kai ta ci gaba da abunda ke gabanta.

WAZEER!Where stories live. Discover now