Adviceful

89 8 5
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.

*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               25

#Adviceful

          Shiru Wazeer yayi yana kallonta,he could feel how the words came from the bottom of her heart,Safwa ta sake cewa "i really do love u" kasa cewa komai yayi saboda yanda kalamanta suka wani irin ɗaɗɗaure shi,Safwa tai kamar za tayi kuka tace "love me Aley ko da kaɗan ne,love me back please,tun kafin mu fara haɗuwa wallahi zuciyata ta kamu da sonka,na yi shiru ne ban nuna maka ba,na bari naga ko za ka fahimce ni,amma kamar baka san ina yi ba,ina sonka wallahi har ban san dame zan kwatanta ba.. Let's break the layer da yake tsakaninmu,ni ba abota nake nufi muyi ba tun farko,na ce haka ne saboda tunanin wata rana za ka gane ka so ni" lumshe idanunsa yayi a hankali har yayi shutting nasu off ya wani irin runtse su yana jin zuciyarsa na bugawa da sauri²,Safwa ta marairaice tace "will u love me Aley? Za ka iya bani guri a zuciyarka? Za ka iya bama soyayyata gurbi da muhimmanci? Har ka karɓeni as a girlfriend please?" Rasa me zai ce mata yayi,yanda take magana ya isa bayyana masa da gaske take,ya san mene ne son abunda bai san kana yi ba,ya ɗan ɗana so duk da ya yi ne a inda ba'a san da shi ba,a hankali ya numfasa kafin ya buɗe idonsa da sukai laushi,maganganunta sun sanyaya masa jijiyoyin jikinsa,kuma sun sa tunaninsa kullewa,bai taɓa zaton haka za ta faru ba,bai taɓa tunanin a matsayin da Safwa take,za ta iya buɗe baki tace tana sonsa ba,though ya fahimceta since from the very beginning,amma bai yi zaton a matsayinta na ɗiya mace za ta iya furta tana son namiji ba,even though ya san ba haram bane yin hakan,amma bai ma taɓa kawo tunanin za ta iya yin haka ba. Ganin ya yi shiru idanunsa kuma a kanta yasa ta kauda kai tana share idonta da ƙwalla ya taru tace "if baza ka so ni kwatankwacin yanda nake sonka ba,ko da kaɗan ne ka mayar min son zan ji daɗi,kuma zan yi farin ciki,zan san cewa ban yi so a banza ba,ban kuma so wanda bai san mutucina ba" numfashi me ɗumi ya sake saukewa still ya kasa buɗe baki yayi magana,tabbas Safwa ta bashi tausayi a yau,but 1 thing da ya yarda da shi kuma yake kallon kansa shi ne,ba zai taɓa cutar da wani ba,shi ɗa ne halastacce da ya san halacci,tun da har ita da take mace da aka sansu da kunya ta iya buɗe baki ta faɗi tana sonsa,to shi me zai sa yace ba ya sonta? Ko da ba ya sonta akwai hanyoyin da zai bi ya fahimtar da ita,ba tare da ya cutar da zuciyarta ba,ba kuma tare da yasa ta yi tunanin aikata wani abu na badai² ba,sai dai yana buƙatar lokaci ya yanke hukuncin abunda yake ji game da ita,lokaci ya ɗan kalla da idanunsa,a hankali yana furzo iska daga hunhunsa yace "i think lokacin tafiya na ya yi" Safwa na kallon ƙasa ta ɗan gyaɗa kanta,a hankali muryarta yai ƙasa² tace "ok! Sai yaushe?" Yayi ɗan shiru kafin yace "za muyi waya idan na isa gida" ta sake gyaɗa kanta tace "ok! Allah ya tsare.. Na gode" yace "a gaida Mom" ta gyaɗa masa kai,tana tsaye ya wuce ya tafi,yau kam ko get bata iya yi masa rakiya ba,yana fita gidan ta sauke wani kafirin ajiyar zuciya,a hankali fuskarta ya cika da wani irin miskilin murmushi,kafin ta haɗa chairs ɗin ta ɗauki tray ta fara mayarwa sannan chairs ɗin then ta wuce cikin gida.

*SAFWA*

      Tana shiga parlour Umma dake kallonta cike da takaici tace "ki je Babanku na kiranki" Safwa ta kalli Umma da sauri tace "ni kuma? Me nayi?" Umma ta wurga mata wani kallo tace "sai dai kije ki titsiyesa sai ya sanar miki da kansa" waro idanunta Safwa tayi sai kuma ta wuce ɗakin Baba,tana yin sallama Baba dake ciki ya amsa yana cewa "yes shigo" Safwa ta buɗe ƙofa jikinta a sanyaye ta ƙarasa ciki tare da durƙusawa tana faɗin "Baba sannu da hutawa" Baba ya ɗago ya kalleta kafin yace "ina mahaifiyar taku take?" Safwa tace "tana can parlour" kafin Baba yayi magana Umma tayi sallama,Baba ya amsa yana faɗin "yanzun nan nake tambayarki" Umma tace "wallahi na tsaya ne na kwantar da su Asim" ta ƙarasa ta zauna tana sauke numfashi,Baba ya kalli Safwa data takure gefe yace "Safwah!" Yanda ya kira sunanta kawai sai da ƴaƴan hanjinta suka kaɗa,tace "na'am" Baba yace "kin san dalilin da yasa nace ina son ganinki a daren nan?" Safwa ta girgiza kai,Baba yace "na samu labarin akwai wanda ke son aurenki,ke kuma kince akwai wanda kike so,right?" Safwa ta sake gyaɗa kanta tace "ehh Baba" Baba yace "good.. Kin san me yasa nake miki tambayoyin nan?" Safwa tace "a'a" Baba yace "da fari na baki dama ki tsaya da samari ne saboda me?" Tace "idan na samu miji ku min aure" yace "kin san da haka?" Ta gyaɗa kai tace "ehh!" Baba yace "Safwa bazan miki auren dole ba ki san da wannan,saboda ni ma ba'ayi min ba,kuma ba zan yiwa ƴata ba,u are my only child mace a duk duniya,saboda me kina da wanda kike so kawai zan tauye farin cikin ƴata? Wannan dalilin yasa nake so ki sanarwa shi wanda kike so,idan har da gaske yake sonki to yazo muyi magana ya aiko magabatansa ayi maganar aurenku,idan ba haka ba ni da kaina zan dakatar da shi,am i clear?" Safwa tace "toh! Baba" Baba yace "shi kenan tashi ki tafi,Allah yayi muku albarka" Safwa tace "ameen.. Sai da safe" Baba suka amsa. Tana fita ta haura sama,bedroom ɗinta ta shiga tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya,kafin tasa hannu ta ɗauki sabuwar wayarta,missed calls ɗin Hamood Waziri was abunda ta gani a kai,bata fara kiransa ba ta shiga kiran Malama Gaaji ta sanar da ita abunda ya faru tsakaninta da Aley a daren da kuma abunda Baba yace mata,kan maganar turo Aley da yace tayi yana son ganinsa,yanda take mata bayani cikin damuwa,yasa Malama Gaaji ta ƙara mata ƙwarin guiwa then sukai sallama tana sanar mata a taimaka ayi mata taimakon da aka saba,ta yanda bai isa ya kalleta yace bai sonta ba kuma zai zo yaga Baba suyi maganar aurensu,suna gama waya ta shiga kiran Radhiya,tana ɗauka Safwa tace "hello ƙawata! Ya kike? Ya yau?" Radhiya tace "lafiya lau wallahi.. Ya Umma da su Bilal?" Safwa tace "kowa lafiya.. I have a gist fa" Radhiya na dariya tace "ok! Gist me,me yake faruwa?" Safwa tace "yau na sanarwa da mutumin fa" Radhiya tace "wane mutumi? And me kika sanar masa?" Safwa tace "na faɗa masa ina sonsa.. And u know what?" Radhiya da mamakin Safwa ya kashe tace "kin faɗa masa? But why ƙawata? Idan yace miki a'a fa? Kin san bazai miki daɗi ba,ni dai ina jiye miki abunda zai faru wallahi,da kin bi ta tawa wallahi baza ki taɓa faɗa masa kina sonsa ba,ko da zai yi ajalinki" Safwa ta zaro ido tace "what? Haba ƙawata,baki ga son zai ajalina bane,ai ko ke da kanki sai ki nemosa ki faɗa masa" Radhiya tace "yanzu duk ba wannan ba,yaya kuka yi da shi?" Tas Safwa ta kwashe yanda suka yi ta faɗa mata,Radhiya ta sauke ajiyar zuciya tace "to Allah yasa muji alkhairi" Safwa tace "ameen.. And kin san wani abu kuma?" Radhiya tace "nope" Safwa tace "na fa sake waya" Radhiya tace "ke don Allah?" Safwa tace "wallahi.. Wani muka haɗu da shi rannan a school,bamu haɗu bane ai da kin sha labari" Radhiya tace "wallahi fa tunda muka je gidan su Muniba" Safwa tace "yaushe zan sa rai da ganinki? I want to see u fa,akwai case da ya taso min ina so ki bani shawarar yanda zanyi,yaushe za ki shigo dai kawai muyi maganar?" Radhiya tace "do u want to see me ne haka da gaggawa?" Safwa tace "of course yes,akwai fa labarai ne,kuma idan ba haɗuwa muka yi ba babu yanda za'ayi kiji" Radhiya tace "shi kenan zan shigo in sha Allah" Safwa tace "sai kin zo.. A gaida Ammi" Radhiya ta amsa da "za ta ji.." Safwa na ajiye wayar kiran Hamood Waziri yana sake shigowa,ɗan taɓe baki tayi kafin ta ɗauka tana yin ƙasa da muryarta tace "hello! Good evening" Hamood Waziri ya amsa yana sakin ajiyar zuciya kafin ya shiga tambayarta "ina gimbiyar mata ta shiga?" Safwa ta zauna bakin gadonta tana sauke veil tace "i have a guest ne yau,shi yasa ban samu lokacin kaina ba" yace "ok! Mace ko namiji? I want to know,because i don't want u kina mu'amala da wasu mazan idan ba ni kaɗai ba,ina da tsananin kishi sai kin yi haƙuri da ni" Safwa ta zaro ido tace "laaaa! Mace ne" yace "mace ce dai ko?" Tace "anyways haka nake nufi" Hamood ya sauke ajiyar zuciya yace "ok! Yanzu hankalina ya kwanta.." Hira suka ɗan yi kafin Hamood Waziri yace "Baby ina son zuwa na ganki,and i want to see Dad,ina son gabatar da kaina.. U know na faɗa miki ba da wasa nazo miki ba,idan kin amince min cikin ɗan lokaci za'ayi komai a kaiki gidana" Safwa da gabanta ke wani irin faɗuwa ta fara kame² jin maganar da yake,jin ta kasa magana yayi ɗan murmushi yace "kina buƙatar lokacin yin shawara,right?" Ta gyaɗa kai kamar yana gabanta tace "ehh!" Yace "hope it won't take long?" Ta sake cewa "ehh!" Yace "ok! Yaushe zan zo to?" Tana kallon nails ɗinta da suka taru a yangance kamar tana neman amsar a gurin tace "gobeeee!" Yace "hakan ya yi miki nazo babu matsala?" Tace "ehh" yace "ok! Thanks.. Sai mun yi waya?" Ta gyaɗa kai tace "toh" sanda sukai sallama shiru tayi tare da ɗaure fuska,a fili ta furta "ni fa bance maka zan aureka ba,ni gaskiya kuɗinka nake so kuma shi ya jani,shi na bi.." Tashi tayi ta shiga bathroom tana fitowa tayi shirin kwanciya,tunanin maganar Baba da na Hamood Waziri ta dunga yi,da ƙyar bayan ta gama tattara hankalinta akan tunanin ta yanda za ta sanar da Aley kiran da Baba yake masa ta sauke ajiyar zuciya. Kusan 3 days Safwa basu haɗu da Radhiya ba,ga maganar na cinta,gefe ɗaya kuma Hamood Waziri kullum sai ya tambayeta shawarar data yanke,sai dai tace masa ya ƙara mata lokaci. Yau tunda ta tashi kasancewar bata je islamiyya ba,da wuri ta gama shirinta ta fito,Umma dake zaune parlour ta ɗaga kai ta kalli wall clock da yake nuna 12pm,then ta waigo ta kalli Safwa tace "toh! Sai ina kuma?" Safwa tace "wallahi gurin Radhiya nake son zuwa,mun yi da ita za mu haɗu yanzu ga shi har 3 days kenan" Umma tace "haka dai kullum sai dai ke kije gurinta" Safwa tace "kaiii Umma uzurina ne fa zai kaini dama" sallamar Radhiya yasa dukansu kallon entrance suka amsa,Safwa ta saki dariya tace "ƴar halak! Yanzu fa shirin fita nake naje gidan na sameki" Radhiya tayi murmushi tace "wallahi nima na gama aikin da nake nace bari dai nazo,ina ta jan lokaci yau nace gobe" Safwa tace "Allah ya hutar da ni" Radhiya ta durƙusa ta gaida Umma,ta amsa tana faɗin "ai yanzun nan nake mata ciwon bakin bakya zuwa sai dai ita tace min za taje" Radhiya tayi murmushi kawai,Umma ta tashi tana faɗin "bari na baku guri" Radhiya tace "laa! Umma da kin yi zamanki wallahi" Umma tace "um'um! Kitchen zan shiga na ɗora sanwar rana,ni da ba matayi nake da shi ba,ai dole nayi na gama da wuri kafin rana yayi a kaima yaran nan abinci" Radhiya tace "toh Umma a fito lafiya.." Tana kallon Safwa data zauna kusa da ita tare da ajiye mayafinta tace "baza ki tayata bane kika samu guri kika zauna? Ai nan zan wuni yau" Umma da har ta juya ta waigo tace "attoohh! Gara dai kiji kema ko kya yi mata faɗa,kina ganinta nan babu tsiyar da ta iya,komai ni nake yi a gidan nan.. Yanzu idan akai mata aure fisabilillahi me za taje gidan mijin tayi?" Radhiya ta kalli Safwa da buɗaɗɗen baki tace "ƙawata! Anya kin kama hanyar dai² kuwa?" Safwa ta tsuke fuska tace "kin ga ba na son haka,zuwa kika yi muyi magana ko kuma kin zo ne ki gaggaya min magana?" Radhiya na dariya tace "duka biyun" Umma ta taɓe baki tace "ai ba ta son a gaya mata gaskiya.. Shi kenan sai kiyi ai,amma dai ki sani akwai ranar ƙin dillanci.. Da ya za ta ɗakin ƙanwa" daga haka Umma tayi wucewarta kitchen,Radhiya za ta sake magana Safwa tai kicin² tace "wallahi Allah kika ƙara cewa wani abu akan wannan maganar za mu samu matsala dake" Radhiya ta gyaɗa kai kawai tace "shi kenan tunda ba kya so,amma don ina sonki ne da alkhairi,in ba ni ba kin san babu me gaya miki gaskiya,ko da za'a ganki kina shirin faɗawa wuta" Safwa tace "to ki adanata maybe tayi amfani nan gaba" Radhiya ta gyaɗa kai ba tare da ta sake cewa komai ba,hira suka shiga yi har sanda suka gangaro kan zancen haɗuwarta da Hamood Waziri,bata ɓoyewa Radhiya komai ba da ya faru tsakaninsu,Radhiya tace "to shi yanzu ba kya sonsa me yasa kika yarda har yazo gidanku? A ganina da baki ma fara bashi fuska ba bare number ki" Safwa tai mata wani kallo tace "whatttt? Haba Radhiya kin ga kuɗinsa kuwa? A'a wallahi bazai yiwu ba.. Ni kawai maganar auren da yazo min da shi ne bai min ba,kin riga kin san akwai wanda nake so fa" Radhiya ta buɗe baki tace "ban gane ba!? Idan bai zo miki da maganar aure ba da me kike so yazo?" Umma da ta gama jinsu tas ta fito kitchen tana faɗin "bar sha³.. Ke a wannan zamanin har za ki samu mutum yace yana sonki zai aureki,sai ki tsaya shashanci kina hauka da kidahumanci,gara da Allah yasa naji maganar nan tun da wuri" Safwa ta turo baki tace "ni fa Umma ina da wanda nake so kin sani" Umma tace "son banza da wofi,ga mai sonki da gaske kin tsaya hauka da shirme kina wani maganar ga wanda kike so" Safwa tace "aahh! Umma dama na faɗa miki tun farko kuɗinsa nake so" Umma tai mata wani kallon takaici kawai ta ɗauke kanta,ba tare da ta sake ce musu komai ba ta juya ta bar parlon.

WAZEER!Kde žijí příběhy. Začni objevovat