Mislike

69 11 2
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

         _So sorry dearest,WhatsApp sun yi banning sabon number na,shi yasa kuka ji ni shiru,wanda suka san sun min magana ta kan this number +234 803 511 6372 please kuyi haƙuri kada kuga ban amsa ba,ku min magana ta tsohon account ɗina idan kuna da shi,if babu ga shi nan na ajiye muku +2348165726609. Thanks so much.._

                               18

#Mislike

          Wazeer ya buɗe ido sosai yana kallon Dad,cikin tarin mamakin mahaifin nasa yace "my office?" Dad yayi masa murmushi tare da gyaɗa masa kai,rasa abun cewa Wazeer yayi saboda mamakin da ya bayyana har a fuskarsa,ya san dai Dad ba ya masa wasa,musamman a irin wannan ɓangaren,tunda ya faɗa he so mean it,dama can da yana yaro Dad ba ya neman shawararsa ko ya tambayi ra'ayinsa akan abu,idan dai shi abun ya yi masa to zai siya masa ne kawai,har yanzu kuma da ya girma ya mallaki hankalin kansa bai daina yi masa duk abunda yaso ba,basu bar Company ba sai gurin 1pm,suna tafiya a hanya Dad na sake masa ƙarin bayanin lokacin da yai setting target ɗinsa na buɗe Company,a zahiri ka kalli industry ɗin za ka iya cewa an gama komai,to amma abun mamakin da tambayar da suka tsaya masa a rai shi ne,shi dai bai ga sunan Company ba a duka abubuwan da Dad ya nuna masa,sai kuma dai bai tambaya ba har suka kama hanyar gida,yana da tarin tambayoyi da suke yawo a kansa tsayin shekaru,yana tsananin son samun amsarsu,sai dai bai shirya yinsu kai tsaye a lokaci guda ba,even though ya kula a yau Dad na cikin wani irin farin ciki,and yana iya cewa burinsa na son mallakar Company ne da ya cika,ya jima yana son yai masa magana but rashin ganin fuska yasa ya bari har zuwa right time,a yanzu da ya gansa cikin irin yanayin da yake muradi har wani ajiyar zuciya yayi,a hankali kamar ba shi ba yana kallon hanya ya ɗan buɗe bakinsa tare da furzo iska waje,sai da ya gama tattara nutsuwarsa a guri ɗaya kafin yace "Dad! Can i ask u?" Dad ya juyo da sauri tare da barin abunda yake a tsadadden wayarsa yace "what's it Son?" Wazeer ya ɗan waiga ya kalli Dad a hankali,kamar bai son furta maganar yace "why ain't u get back to square one?" Dad ya ɗan yi blinking idanunsa kafin yace "i don't get u Son,what are u talking about?" Wazeer ya kalleshi da kyau,idanunsa babu alamar tsoro ko shakka yace "i'm talking about ur relationship kai da Mimi" Dad yai shiru yana mamakin maganarsa,jin shiru yasa Wazeer ci gaba da magana "why are u apart duk tsayin shekarun nan? I think ko wane irin laifi tayi zuwa yanzu ya ci ka yafe mata,hukuncin da kake mata bai yi tsanani ba Dad? Har yanzu dukanku baku yi aure ba? What are u 2 waiting for? Ko ni da nake yaro ba komai na sani akan rayuwarku ba,but to me hukuncinka is more than harsh,i'm sure kuna son junanku har yau,me yasa kuka kasa yafe laifin? Shin wane irin laifi ne ma wannan da ya janyo kuke wahalar da junanku tare da furnishing kanku,ehh?" A tsayin rayuwarsa zai iya cewa bai taɓa magana mai tsayin wannan ba,ko da yana yaro ma ya san bai cika magana ba,sai in Mysha ta tsokaneshi,shima bai cika kulata ba,haka za tai ta janshi tana masa abubuwan da dole za susa yayi magana,idan taga ya ƙi kulawa ta kwaɓe fuska,wani lokaci sai ta fara kuka sannan zai rikice ya fara lallashinta,yanzu data zo masa a rai gaba ɗaya rauni ya saukar masa,jikinsa yayi sanyi,zuciyarsa ta shiga begenta da kewar rashinta,da ace yau tana raye a duniyar,wata ƙila da abubuwan da suka faru basu faru ba,he so missed mutum biyun nan Mysha da Mimi a tare da shi,Dad yayi shiru yana kallon ɗan nasa da ya lumshe idanunsa ba tare da ya ce komai ba,fuskarsa kaɗai ya isa bayyana how sad he is a lokacin,ba zai iya cewa ga tunanin da yake ba,ko dalilin da yasa shi shiga damuwa,sai dai shi a gare shi maganganun da yayi sun tsaya masa a rai,haka nan dukansu suka ɗauke wuta,har suka iso Tudun wuzirci babu wanda ya sake magana a tsakaninsu.

WAZEER!Where stories live. Discover now