Inexplicable

85 10 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*

                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)

Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      

                               22

#Inexplicable

           Rasa me za tace masa tayi saboda yanda maganar yazo mata ba-zata,yana aiko mata sanyayyan murmushi yace "idan baki shirya ba kada kiji komai,just tell me,zan iya jiranki har zuwa lokacin da kika ji kin amince" a hankali ta girgiza kanta tana sauke idanunta ƙasa tace "ni bance haka ba" yace "ok! Me Matar Abuu Turab tace?" Da sauri ta kautar da kanta gefe tana dariya me cike da kunya,yace "Baby are u ready? Ko kina ganin mu jira zuwa wani lokacin?" Tace "Mmm!" Yace "Mmm.. What?" A ɗan kunyace tace "i'm damn ready?" Ya buɗe ido sosai yace "u are damn ready,kike kallon wani waje daban?" Kamar za tayi kuka tace "to da sai nayi yaya?" Yace "sai ki kalleni ki sanar min mana" ta juyo a hankali idanunta sun yi rau² tace "ni bazan iya kallonka ba" yana mata murmushi yace "ok! Yanzu dai kin amince na yi magana da Daddy?" A hankali kamar ba ta so ta gyaɗa masa kai,yace "wow! Thanks Sweet.. In sha Allah zan yi magana da Daddy kafin na zo Kano,and duk yanda muka yi zan sanar miki sai ki sanar da su Abba zuwan mutanena ko?" Ta ɗan ɓata fuska kaɗan sai kuma tayi murmushi tace "ok! Allah ya kaimu" yace "ameen" basu jima ba sukai sallama,ya katse wayar da alƙawarin sake kiranta not too long,wani irin riƙe wayarta tayi,lokaci ɗaya fuskarta ta cika da wani irin yanayin da ba ya buƙatar fassara,kana kallonta za ka iya hango tsantsar farin ciki kwance cikin idanunta da ilahirin kyakkyawar fuskarta,dai² tana sakin ƙayataccen murmushi Baniynah ta shigo tana faɗin "wai matar nan zaman me kike yau a ɗaki? Ki sauko muyi breakfast kin ƙi kin zauna nan ni kin barni sai jiranki nake,cikina tun ɗazu sai kuka yake wallahi kamar babu ƴaƴan hanji fa" murmushin da taga Muniba na yi ya ɗauki hankalinta,tana binta with a suspicious look tace "a'ahh! Wannan smile² ɗin fa Sweetheart?" Muniba ta ɗago tana kallonta,murmushin ta sake yi mata tare da miƙa mata hannayenta duka tace "come Sweet ki ji" da sauri Baniynah ta kama hannunta ta zauna kusa da ita,tana buɗe manyan idanunta tace "what's up?" Muniba tace "albishirinki?" Baniynah tace "goro fari tass" Muniba tace "ok! I have 2 gist for u,wanne kike son ji?" Baniynah tace "duka.. Allah yasa masu daɗi ne" Muniba tayi ɗan jim kafin ta taɓe baki tare da gyaɗa kanta tace "Mmm.. Maybe" cikin ƙaguwa da son jin me za ta faɗa Baniynah tace "don Allah faɗa min,am eager naji ko mene ne yasa ki farin ciki da safen nan" Muniba ta gyaɗa kanta tana ƙunshe dariya tace "Yayanki akaiwa ƙarin girma,kin san ya yi promotional exam,so ya yi passing ya hau rank ɗin Colonel,yanzun nan ya kira ya sanar min" Baniynah tace "awwnnn! Ina taya murna Sweetheart,Allah ya tabbatar da alkhairi.. In sha Allah zan kira na masa Allah ya sanya alkhairi.." Muniba tace "ameee yah Allah" Baniynah tacce "na ji na farko saura na biyun" Muniba tace "kin san me yace min kuma?" Baniynah tace "wait! Shi ne ɗayan labarin?" Muniba ta gyaɗa mata kai,Baniynah tace "a'a! Me yace?" Muniba ta sauke ajiyar zuciya,a hankali ta ɗan sha mur kamar abunda za ta faɗa mara daɗi ne,a sanyaye tace "cewa yayi zai yi magana da Daddy za su zo ayi maganar auren.. Muuu" wani irin ihun murna Baniynah ta fasa da ƙarfi ta rungume Muniba tana faɗin "Alhamdulillah! I'm so so so happy Sweetheart,Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" Muniba tayi murmushi tana rungumeta back tace "ameen.. Amma kin san mene ne?" Baniynah tace "a'a" Muniba tace "wai cewa yayi idan ya kira Daddy duk yanda suka yi,zai sanar min sai na faɗawa su Abba,amma ai kinga bazan iya samun Abba na faɗa masa ba ko?" Baniynah tace "ohh! Noo.. Kada ki damu zan sanar da Mami,idan kun yi maganar sai ki sanar min sanda suka yanke za su zo" Muniba ta saki murmushi tace "ok! Thanks" Baniynah tace "yanzu dai matar Colonel tashi mu tafi muyi breakfast,kin san idan ciki ya ɗauka to komai zai zo da sauƙi,ba'a haɗa jin yunwa da komai" Muniba tace "toh Matar Dr Khalifa Mijinyawa mai rumbun zani,tashi mu tafi kafin kisa yazo yaga laifina" Baniynah tayi fari da ido tace "ya son ranki?" Muniba dake dariya tace "ahh! Ai kin fi kowa sani" Baniynah tai dariya ta kama hannunta tace "let's go ni dai yunwa nake mugun ji" suka miƙe suka fito Muniba na tsokanarta.

WAZEER!Where stories live. Discover now