Hoor

75 13 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..*


                               06

#Hoor

*ABBA WAZIRI*

            Wazeer na fita Abba dake ta kallon Dad,wanda ke zaune kanshi a ƙasa yace "ka kyauta Muhammad.. Ka kyauta ka ji da ka mayar da mu sakarkaru,saboda ka nunama duniya babu wanda ya isa da kai,babu mai faɗa maka kaji,shi yasa ka ɗauke ɗanka ba tare da saninmu ba ka bar ƙasar,duk tsayin shekarun nan baka taɓa tunanin zuwa kou ka kawoshi ya ganmu ba,saboda mu ba ahalinka bane?" Kan Dad a ƙasa yace "ayi haƙuri Abba" Abba yace "ai kai za'a bawa haƙuri,saboda kai akaiwa laifi,an yi maka katsalandan cikin rayuwarka kou?" A hankali Dad ya girgiza kanshi yace "a'a Abba" Abba Waziri yace "toh! Duk ba wannan ba,ka shirya an jima kaje gidan Sarki,mai martaba na kiranka" daga haka Abba ya miƙe yana faɗin "Allah ya kyauta.. Ni na fita" Daada da bata ce ƙala ba tace "toh Allah ya tsare a dawo lafiya" Abba yace "ameen.." Daga haka ya fita,Dad ya ɗago yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yace "Daada!" Daada tace "a'a karka kira suna na,sanda ka aikata laifukanka kou ni ban sani ba,ina ce muna yin waya da kai? Amma ka taɓa sanar min kana tare da ɗanka? Duk abunda zuciyarku ya raya muku shi ne dai²,bakwa tunanin gaba sai dai kawai kuyi gaban kanku,a rayuwar nan duk wanda ya rasa me gaya masa gaskiya ai ya tafka asara kuwa.." Dad yace "kuyi haƙuri Daada,in sha Allah haka bazata sake faruwa ba" Daada tace "na nawa kuma Allah na tuna" Dad yai murmushi,Daada tace "ka yi dariya mana tunda ga mahaukaciya tana maka magana" zazzaro idanunsa yayi da sauri ya miƙe yana faɗin "Allah ya baki haƙuri ni ba dake nake bafa" ta maka wani kallo ta ɗauke kanta tana faɗin "ka wuce ka tafi kiran Baffan naka" da sauri yace "tou Daada.. Na tafi" Daada tace "Allah ya tsare" ya amsa tare da saurin barin parlon yana sakin murmushi.

*WAZEER*

             Yana ta zaune parlon wani irin baƙon ƙamshi ya fara masa sallama,a hankali yana ta danne² a wayarsa ba tare da ya ɗago kanshi ba,har kyakkyawar matar da shekarunta baza su wuce 45 ba ta ƙaraso tana faɗin "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh! Sannu samari.." Duk duniyar da ya shiga,bazai taɓa manta muryar mahaifiyarshi ba,Miminsa da all this while yake tsananin so da kewarta,wani irin ɗago kanshi yayi dai² za ta zauna,da sauri ya miƙe tsaye yana kallonta idanunsa suna sauyawa ya buɗe bakinshi ya furta "Mimiiiii!" Ita kanta saurin ɗagowa tayi jin sunan da ya kirata da shi,tun tsayin shekaru 20 rabon da taji wani ya sake kirata da sunan sai yau,a duniya bayan yaranta babu me kiranta da shi,tabbas ta san Mysha her little girl ta rasu,yau shekara ɗai² har 20,wanda da ace tana nan yau da shekarunta 23 cif,Wazeer kuma her Abuu-Turab,her Zaki,tunda ranar da Hamood yazo ya ƙwace shi a hannunta ya tafi da shi,bata sake ganinsa ba kou a hoto,ta yi jiran,ta yi kukan,ta yi roƙon gurinsu Abba,amma har yau babu shi babu labarinsa,ina Hamood ya kai mata yaro Allah kaɗai ya sani,dan babu wanda ya taɓa sanar mata ga inda ya kai shi,sanda take kallon kyakkyawar kamilalliyar fuskarsa sai da gabanta yai wani irin faɗuwa,tana kallonsa a hankali fuskarsa ta rikiɗe mata ya koma mata her little Abuu Turab,bakinta na ɓari tana nunashi hawaye suka fara saukowa fuskarta,saurin tahowa yayi inda take,ya durƙusa gabanta da wani irin emotion ya sake cewa "Mimiiiii!" Saurin kai hannunta duka biyu tayi fuskarsa,tana girgiza kanta tace "Waa.. Waz.. Eer!" Gyaɗa mata kai yayi,idanunsa a kanta ya wani irin kai hannunshi ya rirriƙe hannayenta da suke kan fuskarsa yana sakar mata sanyayyan murmushi. Kuka Hoor ta fashe da shi tana kallon ɗanta da yai girma sosai tace "u really grown up" murmushi ya sake yi mata,a hankali ya cire hannunsa daga kan nata ya kai fuskarta tare da share mata hawayen da take,cike da tsantsar so tace "kai kaɗai kazo? Ina Dad ɗinka ya tafi da kai? Me yasa baka taɓa zuwa ba duk tsayin lokacin nan sai yanzu? Ka san yanda nai kewar rashinka?" Idanu ya buɗe da kyau yana kallonta,gaba ɗaya yaji jikinsa yai sanyi,ya kasa amsa tambaya ɗaya daga cikin duka tambayoyin da tai masa,da sauri ta tashi ta kama hannunsa tace "taso muje upstairs ku gaisa da Mama,ur grandma,kullum sai mun yi hiranka da ita.." Gyaɗa mata kai yayi a hankali sannan ya miƙe,ta kama hannunsa kamar wanda ake shirin ƙwacewa,suka nufi stairs suna haurawa tana waige² da kallon fuskarsa,duk ta rikice saboda murnan da ya cikata,tun basu kai parlon sama ba take faɗin "Mama! Mamana!! Kin san wane ne yazo?" Mama dake jiyo yanda muryarta ya sauya kamar da wani abu dake faruwa tace "a'a Auta sai kin faɗa min.. Wane ne yazo?" Dai² suna shigowa Hoor ta saki wani ƙayataccen murmushi tace "Mama kinga wanda yazo.. Kin gane shi?" Yanda Hoor ta riƙo hannunsa tana jansa zuwa gabanta yasa ta kallon fuskarsa,kamanninsa da Hoor ɗinta babu abunda ya sauya,sai dai ya girma ya zama cikakken saurayi,gyara gaman glasses ɗin idonta Mama tayi a hankali,da murya me cike da mamaki tace "Abuu-Turab!" Yanda Mama ta ganeshi yaiwa Hoor daɗi sosai,ta saki ƙayataccen murmushi tare da sakin hannunshi tace "jeka gurinta.. Ta ganeka" fuskarshi a sake da ɗan murmushi ya nufi gurin Mama ya durƙusa gabanta,da sanyayyan yanayinsa ya shiga gaisheta tana amsawa da kallonsa,lokaci ɗaya tace "ina mahaifin naka? Wace duniyar ya tafi da kai?" Da huskey voice ɗinsa yace "California" Mama tai ɗan shiru tana tunani da maimaita faɗar "California.. Ina kenan? Wace ƙasa ce?" Yace "U.S.A" Mama dai hallau bata gane ba,da sauri Hoor tace "Mama America yake nufi" Mama ta gyaɗa kanta tace "auuu toh! Maa sha Allah.. Ai kuwa gaka nan ka zama saurayi,ya karatu fa kou aiki kake?" Ya ɗan girgiza kai kamar yana jin wahalar yai magana yace "na kammala" Mama tace "maa sha Allah.. Saura aiki kou? Yaushe kuka zo?" A taƙaice yace "yesterday!" Mama ta gyaɗa kanta tace "Allah sarki.. Ashe baka mance mu ba" ɗaga kanshi yayi ya kalli mahaifiyarshi dake ta sakin murmushin jin daɗi,Mama tace "Allah ya maka albarka.. Ashe da rabon za mu sake haɗuwa,shekara ɗai² har 20 rabonmu da kai" shi dai bai ce komai ba sai kallon Miminsa yake,me aikinsu ce ta shigo da sallama,ganinsa a parlon sama yasa ta fahimci lallai ba gamagarin baƙo bane,though tun kallon farko da tai masa taso taga kamanninsa da Hoor,sai dai bata taɓa ganinsa a gidan ba,shi yasa bata kawo komai ba,ƙarasawa tayi ta ajiye tray ɗin hannunta dake ɗauke da bottle water sai lemo da abinci,Hoor dai ta rasa ina za tasa shi ma saboda murna,ta taso da kanta ta ɗauki lemon za ta kwance lid ɗin ta tsiyaya masa,da sauri yace "Mimi! Ki barshi" ɗagowa tayi tana kallonsa tace "baza ka sha ba?" Gyaɗa mata kai yayi yace "i'm ok now" ɓata fuska tayi tace "me kaci? Kuma a ina kaci?" A hankali yace "ban daɗe da yin breakfast ba na fito gida" tai masa wani kallo irin kallon da uwa ke yiwa ɗanta me narkarwa,kafin tai magana ya rigata yace "zanci Mimi kafin na tafi" tace "ok! Sha ruwa tou" ta ɗauki ruwan ta bashi,bai yi musu ba ya karɓa ya buɗe ya zuba a cup yasha,gaba ɗaya Hoor ta kasa cire idanunta daga kanshi,wani irin bala'in sonshi na sake ratsata,wayarshi daya ajiye gefensa ne yai ƙara,da sauri ya ɗaga yana kallon sunan *My Hero* dake yawo a screen ɗinsa,lokaci ɗaya fuskarshi ya sauya,bayan ya gama sauraren abunda Dad ya sanar masa,yace "ok Dad" daga haka ya sauke wayar,Hoor ta ƙureshi da kallo sai murmushi take,komai yake idanunta na kanshi kamar kada ta barshi ya sake yin nisa da ita,a hankali ya ɗaga idanunsa ya kalleta,kamar bai so yai magana yace "Mimi i have to go,Dad na jirana za muje gidan Sarki" ɗan jim tayi kafin tai ƙarfin hali tace "ok! But yaushe za ka sake zuwar mana?" Kallonta yayi kaɗan yace "soon in sha Allah" daga haka ya tashi ya ƙarasa gaban Mama yana kallonta yace "zan tafi Mama" Mama tace "tou Abuu-Turab.. Ka gaida mutanen gidan" ya amsa tare da tashi yana kallon Mimi yace "Mimii" gyaɗa masa kai tayi fuskarta na nuna rashin jin daɗin tafiyarshi da wuri,duka² yaushe ma yazo da zai tafi tun yanzu? Kou fa gama ganinsa bata yi ba,bare suyi hira taji yanda ya rayu,tai masa tambayoyi masu muhimmanci game da kansa,har itama ta bashi labarin yanda ta rayu da kewarshi,da abubuwan da tayi cikim shekarun da suka wuce,a hankali idanunsa a kanta yace "i'm sorry Mimi,zan dawo in sha Allah" a hankali ta gyaɗa masa kai jikinta a sanyaye tace "yaushe za ku tafi?" Buɗa idanuwa yayi yace "where?" Tace "California" girgiza kanshi yayi yana taɓe baki yace "i don't think zamu sake koma can.. But" sai kuma yai shiru,Mimi dake kallonsa tace "ok" tana son tambayarshi Dad ɗinsa fa? Har yanzu bai daina fushi da ita ba? Bai daina ganin laifinta akan mutuwar Mysha ba? Sai dai wani zuciyar ya haneta,saboda kada shi da Mama suga kamar ta damu da shi,kawai sai tai shiru ta miƙe,sallama ya sake yiwa Mama,kafin su taho ta rakoshi har compound,tana ta kallon yanda ya zama saurayi,kai baza ka kalleshi kace ma ita ta haifeshi ba,shekarunsa 28 amma kamar ya kai 30+,ya yi girma sosai,wani ya gansu a haka da suka jero sai yace ƙaninta ne dake binta,murmushi tayi a hankali dai² lokacin driver ɗin da ya kawoshi ya taso daga gurin me gadin da suke ta hira,gaishe da Mimi yayi respectfully ta amsa,da sauri ya buɗewa Wazeer mota ya shiga ya zauna,yana kallon Miminsa kamar ba zai magana ba,a hankali ya ɗan zaro gaze ɗinsa yana miƙa mata tsadadden wayarshi yace "Mimi! Can i ur digit please?" Ya langaɓar da kanshi,murmushi tai masa ta gyaɗa masa kai tace "of course yes" ta karɓa da sauri tasa masa,kallo ɗaya yaiwa number ya haddaceshi,a hankali ya ɗan yi tsadadden murmushinsa sannan yai saving,Mimi dake ta kallonsa tace "ka kirani sai naga digit ɗinka" ya gyaɗa kanshi yace "ok!" Tana tsaye gurin tana ta kallonsa underneath tana jin kamar kada ya tafi,sai da motarsu ya fita gidan sannan ta juya tana sauke ajiyar zuciya,sosai yau hankalinta ya kwanta da taga ɗanta da take kewar rashinsa,haka nan farin ciki ya mamayeta,wani irin abu daya tsaya mata a wuya tun ranar da Hamood yazo ya tafi da shi,duk tsayin shekarun tana jin abun kullum kamar ƙurjin wuya,sai yau taji babu shi,ko data koma ciki har Mama sai data fahimci tana cikin yanayi me daɗi. Suna isowa Tudun wuzirci bayan driver yai parking ya sauka ya buɗe masa mota,calmly ya sauko ya wuce cikin gida,ɓangaren Daada ya nufa kai tsaye ya shiga da sallama fuskar nan a haɗe,shi kansa bai so tahowa ya bar Mimi ba,ya so zama da ita ko basu yi hira ba ya ganta,je really² missed her,Daada ta amsa ta ɗaga kai tana kallonshi tace "har ka dawo?" Ganin babu kowa sai ita kaɗai yasa shi buɗe baki yace "Dad fa?" Daada tace "sun fita da kakanku gidan sarki" kallon Daada ya tsaya yana yi,lokaci ɗaya ya juya yana kiran Dad ɗin a waya,Daada dai ta bishi da kallo bata ce komai ba,wato hausawa suka ce hali zanen dutse,kuma suka ƙara da cewa,idan ka kwana biyu baka ga mutum ba,kuna haɗuwa ka fara tambayarsa ya halinshi? Dad yana ɗauka ya sanar masa abunda zai faɗa ya katse wayar,fita yayi daga gidan ya samu driver a zaure zaune,ganin fitowarsa yasa ya tashi da sauri yana tambayarshi "ranka shi daɗe fita za kayi?" A hankali Wazeer ya gyaɗa kanshi,mutumin ya taso da sauri yasa takalminsa ya biyo bayansa,mota ya buɗe masa sai da ya shiga kafin ya rufe ya shiga mazauninsa ya tada motar,yana kallon Wazeer ta mirror yace "ina muka nufa ranka shi daɗe?" A hankali Wazeer yace "gidan Sarki" Malam Uba ya gyaɗa kai yaja mota suka tafi,few minutes drive ya kawosu,Wazeer ya kira Dad yace "here i'm Dad.." A hankali ya gyaɗa kanshi sannan ya katse wayar,Dad ne ya fito yazo tafiya da shi cikin gidan har parlon Mai martaba,can suka samu Abba Waziri da brothers ɗinsa su Abba Galadima da Wambai duk suna zaune suna hira,da sallama a bakinsu shi da Dad suka shiga,Mai martaba da su Abba suka amsa,ƙasa saman rug dai² gaban Mai martaba suka zauna,Wazeer ya fara gaida Sarki,sannan Uncle's ɗin mahaifinsa,sai kallonsa suke suna mamakin girman da yayi,Sarki Abduljalal yasa Iyaad ya kaishi cikin gida ya gaida su Mami,gurin Fulani Halimatu ya fara kaishi,daga can suka shiga gurin Gimbiya Habibah,duk bai jima ba a gurinsu ya tashi,fuskar nan nasa tamke babu fara'a,abunka da me ilimin Psychology,cikin ɗan lokaci ya karanci gidan,Allah ya ganar da shi komai,nan da nan yaji yana son barın kusa da inda suke,kwata² yaji basu kwanta masa ba,ransa bai aminta da su ba,kou ruwa da aka kawo masa da abici babu wanda ya kalla,yace da Iyaad dake shigar da shi gidajen su tafi,daga nan ɓangaren Mami amaryar Mai martaba suka nufa,a nan kam sanda suka gaisa suka nemi guri sua zauna,Mami sai hira suke ita da Iyaad yana jinsu,da yake duk rashin maganar Iyaad bai kama ƙafarsa ba,sosai Wazeer yaji ya nutsu da ita,har ya sake ya ɗan ci abincin da Mami tasa aka kawo musu,Iyaad sai kallonsa yake da mamakinsa,a ranshi yake tambayar kansa "kada dai ace daga zuwansa har ya fahimci wani abu dake faruwa gidan?" A hankali yayi murmushi ya bawa kansa amsa da "no wonder.." Part ɗin gidan kaf har nasu sai da suka shiga da gurin Gimbiya Atika,sai da aka kira zhuhur suka je sallah suka dawo,Mami ta samu ƴan hira yau,bashi ya bar gidan ba sai ana kiran maghreeba sannan yaiwa Mami sallama,tana ta sawa rayuwarsa albarka,ya amsa da ameen sannan suka wuce masallaci Iyaad na faɗin "give me ur digits bro.. Akwai family groups ya kamata ace kana ciki" Wazeer yace "ok! Idan mun fito sallah" Iyaad yace "alright" suna yin sallah bayan sun fito,tsayawa suka yi Iyaad ya karɓi digits ɗinsa,daga nan ya rakashi har inda motar da yazo yake,Iyaad na tsaye yana kallonshi da tunani akan kansa,yanda bai cika magana ba yau ya samu ɗan uwa,haka kawai ya samu kansa da sakin murmushi,Wazeer na tafiya ya juya cikin gida. In just 2 weeks da saukarsu Nigeria,gaba ɗaya Wazeer bai samu lokacin kansa ba,kullum su ne fita zuwa wancan gida,groups ɗin family babu wanda bai ciki,though bai cika magana ba,tun introducing kanshi sai dai yaita kallonsu suna magana,idan ba Iyaad ya gani ba kou sallama sai ya manta rabonsa da yi,akwai wani group ma na matasa da aka sashi *YARAN TUMBIN GIWA*,group ne aka yi shi saboda ire²nsu yaran masu kuɗi da masu mulki,tun daga sarauta har zuwa yaran Mmmm siyasa,yana ganin yanda ƴan mata da samari ke hira,ba wani abu dai ake mara kyau ba,saboda ƙarfafa zumunci ne tsakaninsu,sai idan wani abu ya samu mutum na jaje kou taya murna,sukan haɗu kou ayi grouping wanda za su walkici sauran suje ma mutum,kamar rashin lafiya,mutuwa da biki,mafi yawanci dai su Iyaad ɗin ne a ciki,sai yaran manya na Kano ƴaƴan masu da shi,asalin ajebotters,wasu ma basu san ya akai akasa su a group ɗin ba,sun tsinci kansu ne kawai a ciki,idan yana zaune ya rasa abun yi haka zai ta bin hirar da ake,Dad tunda suka zo bai zama sai can dare yake shigowa,shi kaɗai yake yini a part ɗinsu da aka gyara tunda suka sauka. Kwance yake a parlour,daga shi sai 3 quarter da armless,gashin jikinsa sun yi luf²,tamkamar wani ua aikeshi,haka kawai ya shiga whatsapp,group na *YARAN TUMBIN GIWA* ya buɗe,ganin yau shiru babu kowa cikin gidan yai sallama,within a minute aka amsa shi,da farko idonshi bai kula da sunan da ya gani ba kawai ya tura "how are u bro?" Surprised emoji aka turo masa da same number,sai kuma ga message an masa DM da new number,kafin ya buɗe message ɗin ya shiga profile yana duba asalin ta inda suka haɗu,yaga daga group na yaran tumbin giwa ne,voice note ɗin da akai masa sending ya shiga yai playing,muryar mace ce yaji hakan yasa yai shiru yana sauraren abunda take cewa,she's complaining ya mayar da ita namiji,cike da shagwaɓa take magana,tana yi kamar za ta kece da kuka,murmushi ya samu kanshi da yi,for the first time a dukkannin rayuwarsa,yau yai magana da wata mace da bai sani ba,cikin seconds ya tura mata "i'm sorry! I didn't know u were a little girl" ai kamar ya tunzurota yace mata little girl,nan ma ta sake yo masa sabon VN,kunnawa yayi yana saurarenta,da siririyar muryarta tace "stop calling me little girl Man.." Buɗa idanuwa yayi sai kuma ya tura mata "alright! I'm sorry" daga haka ya fita gaba ɗaya ya kashe wayar ya ajiye,rufe idonshi yayi yai shiru,a hankali yake tunanin Mimi,underneath his breath ya furta "ya kamata naje na ganta" kiran da ya shigo wayarshi yasa shi buɗe ido,a hankali ya ɗauki wayar yana kallo,ya gane number da suka gama magana ne yanzu,shi a rayuwansa kallo ɗaya yake yiwa abu ya ɗauke,answering yayi yasa a handsfree ya ajiye gefen kansa,da huskey voice ɗinsa yai sallama,daga can gefen aka amsa,kou dan siririyar muryarta ya ganeta,cike da iyayi tace "I'm *SAFWA* from Yaran tumbin giwa,wanda ka mayar namiji.. Muna magana na ga kayi offline,shi ne na kira saboda ka tabbatar ni ba namiji bace" idanunsa a lumshe yace "yeah! Anything else?" Murmushi tai masa tace "nothing.. Kawai na kira to confirmed that,ni ba namiji bane" a hankali cike da izza yace "ok then?" Murmushi Safwa ta sake yi tace "and if babu damuwa,can we be friends?" Kamar bazai amsa ba sanda ta sake maimaitawa,yace "kina son hakan?" Boldly daga muryarta kana iya ganewa tace "ai ni na tambaya dama,kai me kace?" Yace "ok! Friends" ta gyaɗa kai tana murmushi tace "thanks.. Later?" Yace "uhumn!" Da ɗan sauri tace "wait a minute.. I like to know u.. Ur name please?" Kamar bazai ce komai ba yai shiru,sai kuma ya furta *"ALIYU!* But u can call me.." Sai da ya sake yin shiru kafin a hankali yace "Abuu-Turab" dariya tayi me sauti tace "ohh! Ni ba na son wannan,akwai friend ɗita sunan Yayanta kenan,tunda we are friends yanzu ni zan kiraka da sunan da yai min,wanda ni kaɗai ne zan na faɗa" taɓe baki yayi yace "ok! Wanne kenan?" Har ranta taji daɗin yanda yake amsa mata,tace *"ALIYOS* or *ALEY!"* Gyaɗa kanshi yayi yace "ok dear.. Bye for now zan je wani waje" da sauri Safwa tace "alright! Take a good care of urself for me" yace "thanks" daga haka ya katse wayar ya tashi ya wuce bedroom ɗinsa,wanka ya sake a gurguje ya shirya ya fito cikin ƙananan kaya,rigar polo ɗin nan zaune a jikinsa kamar dama a haka akayota,kaji yanda yake zuba ƙamshi za kai zaton ɓarin turaren yayi duka a jikinsa,ƙamshin ya haɗu ya bada wani irin yanayi me daɗi,duk nacinka da son sanin wane turare ne yai amfani da shi,za ka shekara baka gane ba,shi mutum ne da a rayuwarsa bai son gasa,komai nasa is different da kowa,car keys na sabuwar motarshi da Dad ya siya masa ya ɗauka sai facemask ɗinsa da wayarshi ya fito,sanda ya tsaya ya rufe part ɗinsu sannan yai waje abunsa. Daga Tudun wuzirci gidansu Mimi ya nufa kai tsaye,yai parking compound ya sauko ya wuce,gaban entrance ya tsaya yai knocking,daga ciki ya jiyo maganar Mimi na faɗin "ana zuwa" ba'ayi 2 minutes ba aka buɗe ƙofar,ɗaga idonsa yayi ya kalli wanda ke tsaye,Mimi dake kallonsa da mamaki tace "Zaki!" Har ya manta rabon da yaji wani ya kirashi da sunan,ɗan gajeren murmushi ya saki,Mimi tace "shigo mana" babu musu ya shiga da sallama a bakinsa,Mimi da Mama wacce ke zaune suka amsa,sanda Mimi ta rufe ƙofar sannan ta biyo bayansa tana faɗin "daga ina Zaki?" A taƙaice yace "gida" Mama dake ta sakin murmushi tana kallonsa tace "Abuu-Turab! Kai ne haka da ranar nan a gidan namu?" Ya gyaɗa kanshi kawai a hankali yayi ƙasa ya fara gaisar da ita,ta amsa tana tambayarsa mutanen gida da su Daada,ya amsa da "suna lafiya" Mimi ya gaisar ta amsa,sannan ya koma saman kujera ya zauna,me aikinsu Mimi ta kira ce ta kawo masa ruwa da lemo,shi dai yana zaune tun gaisawar da sukai babu um bare um'um,sai da Mimi ta kalleshi tace "ya kamata kaje gidan Uncle's ɗinka ka gaishesu" yace "ok!" Sai kuma ya kalleta yace "da waye za muje?" Hoor ta kalleshi sai kuma tace "bari na kira Abuu-Turab yazo sai ya kaika" shi dai bai kuma magana ba,yana dai ta tunanin wane Abuu-Turab ɗin zata kira? Waya tayi gidan Yaa Abuye tace a turo mata Abuu Turab,ba'a jima ba yaronn da baifi 10yrs ba yazo,yana shigowa ya gaida su Mama,sannan ya gaisar da Wazeer dake kallonshi,Mimi na kallonsu tace "Abuu Turab ka raka Yayanka gidanku ya gaida su Abbu" Abuu Turab ƙarami yace "tou Aunty" Hoor ta kalli Wazeer tace "tashi kuje" babu musu ya tashi ya kama hannunsa yana kallonsa yace "shall we?" Gyaɗa masa kai Abuu Turab yayi yace "yes!" Ya kalli Mimi yace "sai mun dawo" tace "ku gaishesu" inda yai parking motarshi ya kalla kafin yace "da nisa gidan?" Dariya Abuu Turab yayi yace "a'a can ne baya,da ƙafa nazo fa" Wazeer yace "ok!" Suka fita suna tafiya da ƙafa,a hankali Abuu Turab yace "yaya sunanka Yayanmu?" Wazeer ya kalleshi yace *"ABUU-TURAB!"* Abuu-Turab yace "kaiii! Sunanmu ɗaya ne da kai?" Wazeer yace "yes!" Abuu-Turab ya gyaɗa kanshi kawai,surutu yaita yiwa Wazeer da bai magana sai eh da um'um,har suka kai gidasu,suna shiga ya gaisar da Uncle ɗinsa,Yaa Abuye ya sake manyanta sosai,abunka da namiji me nauyin iyali,a haka ma wai akwai jin daɗi,tabbas da bai gamu ba,har cikin gida ya shiga suka gaisa da su Aunty Zainab haka su Yaa Umar ma,duka gidajensu babu wanda bai je ba,su duka sun yi mamakin ganin girmansa,kuma sunji daɗin yanda ya girmamasu yaje gidajensu,kowa ya samesa a gidansa Uncle Mansoor da Uncle Umar,duka sun yi farin ciki sosai,sai dai duk sun ƙara manyanta,kowa da family'nsa haka aka gabatar da shi ma wanda basu sanshi ba sai a labari,ranar har dare yana nan gurin Miminsa,sai da zata tafi hospital kasancewar night duty gareta sannan yai haramar tafiya shima,tare suka fito bayan yaiwa Mama sallama,tana tai masa addu'ah da sawa rayuwarsa albarka,a compound sukai sallama da Mimi kafin suka rabu yana cewa "Mimi sai na sake zuwa" kusan tare suka fito daga gidan,shi ya ɗauki hanyar Tudun wuzirci ita kuma ta ɗauki hanya mafi sauƙi da zai kaita AKTH...



           #A gaskiya bazan ɓoye muku ba,Hoor ta ɓata min rai da bata manta wani Hamood ba,mutumin da baya ta tata,fisabilillahi mene ne nata da har za taji son ta tambayi Wazeer shi?

https://chat.whatsapp.com/LMWOmafckAGJoQ4ebkvdcG



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*


#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

WAZEER!Where stories live. Discover now