Mission

89 17 5
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

      _Join our group domin samun update https://chat.whatsapp.com/LMWOmafckAGJoQ4ebkvdcG.. Follow the REAL-SMASHER SQUARE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Va5voqA4tRrtP6Mvss2q.. Follow my channel dearest domin samun update na book ɗin *WAZEER* da sauran wanda za su zo,har ma da tsofaffi.. Duk wanda nake da contact ɗinsa yayi following ɗina za su nuna min,idan kuna so nayi saving contact ɗinku chat me up @+234 803 511 6372/@+2348165726609. Thanks so much as u do so._


                               17

#Mission

*SAFWA*

          Monday tushen aiki ko Bature na tsoronki,haka dai Bahaushe yake mata kirari,kasancewar ranar aiki duk ma'aikatan gwamnati sun wuce gurin aiki,ƴan kasuwa zuwa wanda suke sauran sana'o'i kowa ya nufi gurin nemansa,hatta ɗalibai suma tun sassafe sun tafi makaranta,idan kabi streets za kaji ko'ina yayi tsit. Kwance Safwa da bata fita school ba take a saman kujera a parlour tana chat,babu yanda Umma bata yi da ita akan ta shirya ta tafi school ba,tace ita sai ta ƙara hutawa jikinta duka ciwo yake mata,Umma ta gyaɗa kai ta tashi tai wucewarta kitchen,tana shirin ɗora sanwar rana take ci gaba da mita tace "idan Babanku yai magana wallahi dama kada ki sake kice na san wani abunda ya hanaki zuwa makaranta yau,zan ce bansan komai ba tunda dai ya baki transport kuma kin amshe kin ƙi zuwa" Safwa tai dariya tace "kai Umma don Allah" Umma tace "toh shi kenan ki ci gaba da cewa kai Umma,sai ya dawo ya tambaya zan sanar masa komai,ni baza ki janyo min faɗan da ya fi ƙarfina ba wallahi ina zaman²a" Safwa tace "ai kema kin san bazai dawo ba fa yanzu" Umma tace "a'ahhaa! Tsautsayi kuma ai yana iya sawa ya juyo" Safwa tace "a'a in sha Allah ma bazai dawo yanzu ba" Umma tace "uhumn! Allah dai ya kiyaye" Safwa tace "ameen" tayi shiru ta ci gaba da chat ɗinta,number Aley take kallo da bai buɗe morning text da tai masa ba yau,a fili tace "ko dai jikin ne wai har yanzu?" Tayi shiru kamar tana tunani sai kuma ta sake cewa "let me call him naji dai" da sauri ta fita daga whatsapp ta shiga phone call ɗinta,number ɗinsa tayi dialing underneath tana addu'ah Allah yasa kada ace mata a kashe yake,cikin sa'a dai² lokacin wayar tasa yana buɗe,kiranta na tafiya tayi ajiyar zuciya tace "alhmdllh!" Kafin ta sake magana ya ɗauka da sallama,Safwa ta amsa tana faɗin "Friend! How are u? Ya jikin?" Daga can gefensa ya amsa,Safwa tace "Allah ya ƙara lafiya,dama na kira ne saboda na ji ka shiru,though muna ta hidimar biki ban samu kaina ba sai yau" Umma dake kitchen ce ta fito ta zauna ta shiga gyara kayan miya,Safwa dake waya bayan sun ɗan yi magana tace "ga Mom ɗina za ta gaisheka da jiki" bai ce komai ba Safwa tasa kiran a speaker sannan ta miƙawa Umma wayar,Umma na mata alamar waye tace "zan faɗa miki idan kun gama magana" Umma ta gyaɗa mata kai tare da karɓar wayar ta kai kunnenta tace "salamu alaikum" Wazeer dake zaune parlour ɗin gidansu yayi baya tare da jinginar da bayansa jikin kujeran da yake kai yace "wa'alaikis salaam warahmatullah wabarkatuh! Barka da safiya Mom" Umma tai saurin ɗaga wayar daga kunnenta jin maganar da ƙarfi,Safwa tace "Umma a handsfree nasa" Umma ta gyaɗa mata kai tana sakin fuskarta ta sake faɗaɗa ta da fara'a tace "barka dai.. Mun tashi lafiya? Ya jiki kuma?" A hankali yace "jiki alhmdllh" Umma tace "Allah ya ƙara afuwa yasa kaffara ne" yace "ameen².. Thank u Mom,Allah ya saka da alkhairi" Umma tace "babu komai,Allah ya ƙara lafiya" ya amsa tare da sake yi mata godiya,tace "sai an jima,ga Safwar" tana miƙa mata wayar Safwa ta cire daga handsfree ɗin da tasa ta kai wayar kunnenta tace "hello dear!" Daga can gefen Wazeer yai mata godiya tare da sallama ya katse kiran,murmushi me sauti Safwa tayi da yasa Umma ɗaga kai ta kalleta,Safwa da ta rungume wayarta a ƙirji ta shiga tunani fuskarta cike da murmushi,Umma dake ta kallonta ba tare da ta sani ba tace "ke kuma lafiyarki lau kike ta dariya? Ko kin sami taɓi ne a ƙwaƙwalwa?" Maganar Umma yasa Safwa dawowa cikin hayyacinta,Umma ta sake cewa "waye wannan da kika bani mukai magana ne?" Safwa tayi murmushi kafin tace "Friend ɗina ne" Umma ta ɗago ta kalleta tace "shima a Bayero University ɗin yake?" Safwa tace "a'a" Umma tace "toh! Allah ya kyauta" Safwa tayi murmushi tace "Umma kin gansa kuwa?" Umma dake ta aikinta tace "ta ina zan ganshi ni Murjanatu bayan ba haɗuwa da shi muka yi ba" Safwa ta kwashe da dariya tace "wallahi Umma ya haɗu,first class ne gurin kyau gashi classy,ko mace albarka wallahi,duk yanda nake jin kaina nake kallon babu wanda ya fini,amma wallahi na yarda shi ya wuce ni" Umma tace "toh! Duk ba wannan ba,mene ne tsakaninku shi nake son ji,kin san dai Babanku bai san komai ba,kuma ba zai so wannan yawan kule²n samarin ba" Safwa ta buɗe ido tace "a'a Umma ce miki fa nayi abokina ne shi" Umma tace "anya Safwa? Kinga nima ban cika son tara samarin da kike marasa amfani ba,gara idan kika samu tsayayye wanda za'a nunawa sa'a sai mu tunkari Engr da maganar duk da bai son maganar aurenki yanzu,amma Allah na tuba ai ba dafaki za muyi mu ci ba,dole wata rana kiyi aure" Safwa ta gyara zama tare da ajiye wayarta gefe tace "wallahi Umma ai nima na fi son nayi auren,ƙawayenmu fa na secondary da wanda muke karatu yanzu sai auren suke yi.. Wallahi gidan Yaa Khalidah ma da muka je sai naji inama gidana ne,sai abunda naga damar yi" Umma tayi murmushi tace "ke dai Allah ya kaimu lokacin,kika samu miji kamar Dr Mohan ai mun yi sa'a" Safwa ta washe baki tace "wallahi kuwa Umma ai sai ma da zamu taho ɗin nan,ji nayi inama ace ni aka kai gidan nan" Umma tace "lokacinki zai zo" Safwa tace "Allah ya kawosa a kusa" Umma tace "ameen.. Yawwa! Wai ni kuwa nace ko ɗan saurayin ma kin yi a bikin nan?" Safwa ta taɓe baki tace "a'a!" Umma ta kalleta da mamaki tace "duk wannan kwalliyar da kayan da kika sa masu tsada,yanzu babu wanda yace yana sonki cikin abokan Mohan ɗin?" Safwa tace "uhumn! Ina dai gani suna kula su Muneerah ana exchanging digits" Umma ta buɗe baki don mamakin da ya cika ta tace "toh amma Muniba fa na ji ance ta yi saurayi? Ko ba a gurin bikin suka fara haɗuwa da wanda naji Baniynah tana magana bane?" Safwa ta kalli Umma tace "waye?" Umma tace "wani babban soja fa da naji ana ta cewa shi ne aminin mijin Khalidah tun yarinta,ni mene ne ma kuwa naji sunansa?" Safwa tai shiru tana kallon Umma,can kamar an mata dole tace "wai wannan Lieutenant ɗin?" Umma tace "shi fa,wallahi sunansa ne ya kwanta min" Safwa ta taɓe baki tace "taɓɓɓ ɗin wannan uban jin kan,meye abun damuwa a saninsa?" Umma tace "toh ki tuna min sunansa mana idan kin gane shi" can ciki² Safwa tace "Abuu Turab" Umma tace "tabbas! Shi ne wallahi,ai har na fara jiyo ƙishin² ɗin iyayensu mata ma sun san maganar,yanzu abunda yai saura dama a gama bikin" Safwa tace "kaiiii! Umma ke duk a ina kika jiyo wannan maganar? Munibar ma da ba wani sakewa take da shi ba,kamar fa ba ta sonsa ma ni nake ga" Umma tace "anya kuwa Safwa?" Safwa tace "wallahi ko magana ba ta masa fa,shi dai yake ta neman guri da siblings ɗinsa" Umma tace "toh! Amma har a gidan bikin naji ana ta cewa saura bikinsu ita da Baniynah nan ba da jimawa ba?" Safwa tace "taɓɓɓ ɗin! Toh sai dai in kuwa auren dole za suyi mata,ko fa a gurin bikinma ba ta um bare um'um" Umma ta kama haɓa tace "amma meye laifin wannan? Ai na gansa dai matashi ne me jini a jiki ko?" Safwa tace "uhumn!" Sai bata sake cewa komai ba,Umma tayi ƙwafa tana jinjina kai,lokaci ɗaya ta ajiye wuƙar hannunta tace "toh amma bari muyi wata ƴar gulma mana" Safwa data ci gaba da chat tace "na me?" Umma tace "kuma ai naga yana da kuɗi kamar ma zai fi Mohan ɗin ko?" Safwa tace "maybe" Umma tace "toh ba ni hankalinki nan muyi magana" Safwa tace "ina ji" Umma tace "ajiye wayar tukuna ki bani hankalinki nace" Safwa ta ajiye wayar ta zubowa Umma idanu,Umma tace "kika ce ba ta sonsa?" Safwa tace "ni dai haka na gani" Umma tace "in ba ta sonsa ai wannan matsalarta ne,za ta iya samun wanda ya fisa tunda ubanta wani ne a garin,kuma yana harka da ƴan siyasa,ko ɗan shugaban ƙasa zai iya samo mata ko ba haka ba?" Safwa tace "haka ne" Umma ta gyaɗa kai tace "yanzu dai ba wannan ba,ke ya yi miki?" Safwa ta tsaya kallon Umma ta kasa cewa komai,Umma tace "tambayarki fa nake dan walaƙanci kikai min shiru" Safwa tace "Umma ban gane tambayar taki ba" Umma tace "ya yi miki as irin mijin da kike son aure?" Safwa ta buɗe ido da kyau tace "Umma!" Umma ta ɗaga mata hannu tace "ba ni amsa tukuna kafin kice komai" Safwa tace "gaskiya Umma in dan kuɗinsa ne ya yi,amma ni ba na son namiji me jin kai irinsa" Umma ta buɗe baki tace "wannan ai ba matsala bane,in dai ya miki kuma kina sonsa ni na san yanda zanyi hankalinsa ya dawo kanki" Safwa tace "Umma gaskiya ni dai a bar maganarsa,da dai wani ne daban ko akan wannan Aliyun da na baki waya kuka gaisa,amma matsalarsa shi har yanzu ban gama saninsa ba tunda bamu jima da haɗuwa ba" Umma ta gyaɗa kai tace "shi kike so?" Safwa tace "wallahi Umma dan baki ganshi bane,ai ko Yaa Mohan da su Yaa Khalifa wallahi albarka" Umma tayi murmushi tace "yanzu shi kike so dai kenan?" Safwa tace "ehh Umma gaskiya,tun ganin farko da nai masa na tafi da shi" Umma tayi dariya tace "toh babu damuwa,zan dai san yanda akayi" Safwa tace "yawwa Ummata Allah yasa min ke a aljannar duniya da lahira" Umma ta washe baki tace "ameen Safwata kin yi addu'ah me kyau,amma ni dan dai kin dage ne,ai da na karɓo miki ɗan taimako akan wancan sojan saboda yayi min a matsayin suruki" Safwa tace "taimakon me Umma?" Umma tace "ƴan addu'o'i mana da maganin farin jini,ai nima ragon azanci nayi na barki haka nan,da tun kafin ayi bikin nan nai hakan da yanzu kin samo min suruki,war haka ma da yanzu Sojan nan ya zama rabonmu,kawai sai na saki jiki kamar kabewa,na ɗauka a yanda kike da kyaun nan gaki fara tas²,kuma mazan wannan zamanin na san yanda suke son farar mace,duk zatona baza ki rasa farin jinin da samari masu shi ɗin za su biyoki ba,amma yanzuma bai ɓaci ba ai tunda ba wani nisa akai ba na gano bakin zaren.. Toh amma ya kike gani yanzu,in sa a karɓo miki dai za kiyi amfani da shi? Kada sai na amso kisa nayi asarar kuɗina a banza? Dan yanzu zamani ya canja,ƴan mata ma wasu su suke kai kansu su nemo sa'a,ai an daina zama kowa mafita yake nema" Safwa ta ƙyalƙyale da dariya tace "wallahi zanyi Umma ki amso,ƙawayenmu fa ina jin suna labarin a makaranta,suna cewa ba a banza samarin suke musu abunda suke so ba,amma kuma idan ka tambayesu me suke yi sai suce falalar salati ne" Umma ta gyaɗa mata kai tace "toh shi kenan sha kuruminki zan kira Hilda muyi maganar,a yanzu dai banga lokacin zuwa Minna ba gaskiya,da ɗaukanki zanyi mu tafi ayi komai a gaban idonki,to amma na san in nai maganar da itama ɗaya ne,za tayi min komai kamar ina nan,in yaso sai ta aiko min kamar yanda aka saba.." Safwa tace "yanda aka saba kuma?" Umma tace "ehh mana aiken da ake yo mana daga can gidan na kayan gona idan akai noma" Safwa tace "aihoo! Ehh wallahi ta aiko" Umma tace "toh shi kenan ai tunda kin amsa na san bazan yi aikin banza ba" Safwa ta gyaɗa kai kafin tace "ni wallahi har mamaki nake wani lokaci idan naga yanda friends ɗinmu suke yin samari manyan masu kuɗi" Umma tace "a'ahhaa! Kema in dai wannan ne za ki gansa a kanki,nan ba da ɓata lokaci ba za ki ɗorar da abunda ke faruwa" Safwa tai dariya tace "wayyo ni Safwa,ai kuwa Umma wallahi nayi saurayi me kuɗi ko,sai kin san ƴarki ta samo miki irin mijin da kike buri" Umma tace "Allah Safwata?" Safwa tace "wallahi kuwa Umma sai wani ma ya san na je inda zaki huta,duk aikin gidan nan sai dai masu aiki suyi miki,ke kuma kina gefe kina hutawa da bada umarni" Umma tai shewa tayi guɗa tace "Allah yasa,ina daga zaune ai min komai" Safwa tace "har Saudiyya zan kaiki,daga can kiga likita akan matsalar ƙafarki" Umma tace "toh Allah ya bamu sa'a" Safwa tace "ameen².. Wallahi har na fara imagination" Umma tayi dariya tace "toh! Ai har kin fini ɗauki da zumuɗi ma" Safwa tace "Allah Umma ni yanzuma ji nake inama ina da kuɗi,ai da tafiya Minna zanyi gurin Aunty Hilda kawai" Umma tace "ahh! Lallai ashe dai da gaske kike" Safwa tace "wallahi i'm damn serious Umma,ƙawaye nawa muna tare da su suna munafurka,ai gara nima na tashi tsaye su san cewa ba su kaɗai suka san kan gari ba" Umma tace "kai amma na ji daɗi da Allah yasa kike da fahimta,yanzu da wata ce sai tace min ba haka ba,ta kama faɗa min ƙauli da ba'adi" Safwa tace "a'a wallahi ni dai ina so" Umma tace "ai kuwa tunda har kika nuna min ina da muhimmanci,yau ɗin nan zan kira Hilda nai mata maganar,dama tana tai min zancen ya kamata nai miki shiri ba tun yau ba,ni ce dai na tsaya ina nuƙu² ina cewa ai ƴata me kyau ce ba sai na wahalar da kaina akan wannan ba" Safwa ta buɗe baki tace "taɓɓɓ ɗin! Toh wallahi Umma har wanda suka fini ma suna yi,ni dai ki mata magana ta aiko min na fara fantamawa nima" Umma tace "toh bari na gama girkin nan dai sai na tsara abunda zan ce mata ayi koh?" Safwa tace "ehh! Ki gama" Umma ta tashi ta kwashi kayanta tai kitchen tana cewa "bari dai nayi sauri na kammala.."

WAZEER!Where stories live. Discover now