Power of love

73 7 3
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

 
     _https://whatsapp.com/channel/0029Va5voqA4tRrtP6Mvss2q.. Follow my whatsapp channel dearest domin samun update na book ɗin *WAZEER* da sauran wanda za su zo,har ma da tsofaffi.. Wani ƙarin abun kuma duk wanda nake da contact ɗinsa yayi following ɗina za su nuna min,idan kuna so nayi saving contact ɗinku chat me up @+234 803 511 6372 ko @+2348165726609. Thanks so much as u do so._


                               16

#Power of love

            Ina ƙasa ta buɗe Muniba ta shige ciki ta ɓoye kanta,kunyar duniya da na su Mami gaba ɗaya ya taru yai mata yawa,Hjy Hauwa dake kallonta fuskarta cike da murmushi tace "maa sha Allah! Gaskiya ɗana bai yi zaɓen tumun dare ba.. Hjy kin ga dai ikon Allah ko?" Mom tayi murmushi also tana kallon Muniba ta gyaɗa kanta,Hjy Hauwa ta kalli Mami tace "Dr hope baza'a hanamu irin da muka gani ba,ko nace Allah yasa ba'a rigamu ba?" Mami ta sake yin murmushi,kunya irin na bafillata ya hanata cewa komai,a hankali ta ɗauke kanta kafin ta iya cewa "ai wannan magana ba nawa bane Hjy,tunda ga Mamarta nan a zaune duk abunda tace ni ba ni da ja" Mama dake saurarensu tayi murmushi itama kafin tace "baza mu hana bama in sha Allah" Hjy Hauwa tace "that means babu kowa a gabanmu kenan? Za mu iya shigowa da ƙarfinmu?" Mama tace "ehh toh! Ai kin san budurwa ba'a rasa ta da masu nema,amma dai babu maganar kowa a kanta" Hjy Hauwa tace "alhmdllh! Ai tunda babu maganar kowa,mu baza mu tsaya sanya ba,in sha Allah da ƙarfinmu za mu zo ayi komai a gama cikin lokaci" Mama tace "Allah ya amince" Hjy Hauwa tace "ameen yaa Allah.. Amma fa gaskiya mun gode da karamcinku Hjy,babu abunda za muce sai godiya,Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci" Mama ta sake yin murmushi tace "ameen yaa arhamur-rahimiiyn" underneath wani irin farin ciki ke mamayar zuciyarta,gani take a yanzu an gama zama ɗaya tunda aure ya haɗa zumunci tsakaninsu,sannan ga wani kuma yana shirin faruwa though dai yanzu aka fara maganar,amma ta tabbatar baza suyi musu zancen da wasa ba. Duk maganar da su Mama suke yi,har lokacin tana tsaye ta rasa me za tayi ko ta aikata,can ta wurga idanunta ta hango su Yaa Mubasshir su kaɗai a seat ɗinsu,ba tare da ta kalli kowa cikinsu Hammad da Sisters ɗinsa ba,sai don kawai son ta samu mafaka,muryarta na rawa tace "Mm.. Maa.. Mama ga su Yaa Mubasshir ɗin na gani" Mama data karance Muniba tsaf tai ɗan murmushi a hankali tace "gurin nasu za kije yanzu?" Kamar wanda ke tsoron za'a hanata,da sauri ta gyaɗa mata kai idanun nan nata sun yi rau² tace "ehh!" Mama ta gyaɗa mata kai also tace "toh! Kuje can ɗin sai ku gaisa,i think za ku fi sakewa kuyi magana ko?" Kafin Mama ta ƙarasa faɗan abunda ke bakinta,ai tuni kunya yasa tai saurin cewa "sai an jima" Hjy Hafsah tayi murmushi kawai tana kallon yaranta tace "Hammad! Ka kyauta,irin wannan abun na hanaka ba tun yau ba ka ƙi ji,yanzu wannan abun da kayi mata a gaban parents ɗinta da mu,idan me raguwar zuciya ce ai sai kasa ta kuka" Mama tayi murmushi tace "ai kuwa anci sa'a ma da har ta iya barin gurin nan,amma Muniba dake da idon kuka ko ɓaure haka ya ganta ya bari" Hjy Hafsah tace "u see! Sai ka wuce kaje ka bata haƙuri maza²,wannan ba wasa bane na sha faɗa maka,and this should be the last,kada ka sake yiwa wani irin wasan nan,idan ba haka ba wallahi zan saɓa maka" Hammad ya gyaɗa kansa jikinsa a sanyaye yace "ok Mom.. I'm really sorry,na biyota ne mu gaisa,ban yi tunanin gurin parents ɗinta tazo ba,da ban yi haka ba,amma kuyi haƙuri please" Hjy Hafsah tace "ok! Kuje ka sameta ka bata haƙuri" ya ɗan gyaɗa kansa fuskarsa da ɗan murmushin nadama yace "in sha Allah Mom" daga haka yaiwa su Mami sallama ya wuce tare da ƙannensa,Hjy Hafsah bata sake kallonsu ba suka ci gaba da maganar da suke ita da Hjy Hauwa,Mami da Mama suma suka ci gaba da maganar da suke Mama na yabawa Hjy Hafsah kan irin tarbiyyar da taima yaranta. Table ɗin su Mubasshir Muniba ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tace "Yaa Mubasshir tun ɗazu nake ta nemanka" Mubasshir ya kalleta yana sakin murmushin da ya ƙara masa kyau yace "bamu shigo da wuri ba,ya akai? Any news?" Muniba tai ƙasa da murya tace "kawai na kasa sakewa a gurin nan ne,don Allah ko za ka kaini gida?" Mubasshir ya sake yin murmushi yace "me yake faruwa? Wani ya takura miki ne?" Girgiza kai tayi innocently tace "a'a kawai ni dai na gaji,so nake na koma gida" Mubasshir ya ɗan haɗe fuska yace "to haka za kije gidan ki zauna ke kaɗai?" Ta gyaɗa masa kai tace "ni dai zan iya zama ka kaini pleaseee" a hankali yace "ko dai Soja ne ya takuraki?" Da sauri Muniba ta kalleshi,sai kuma ta girgiza masa kai tace "a'a ni haka kawai nake son tafiya" kallon tsaf Mubasshir yayi mata kafin yace "to gaskiya bazan iya mayar dake ba,tunda ba ki da wani dalili da zai sa ki tafi" Khalifa dake jinsu tun sanda suka fara magabar bai ce komai ba,lokaci ɗaya ya ɗago ya kallesu yace "what did she just said?" Mubasshir na danna wayarsa fuska ɗaure yace "wai gida zan kaita" Khalifa yace "sai ka kaita ai" Mubasshir yace "ba ta da dalilin komawa gidan fa,ni bazan kaita na ajiyeta ita kaɗai ba alhalin kowa yana nan" Khalifa yace "ohh! Thought ai za ka mayar da ita,yanzun nan na sanar da Mama" Muniba ta kalleshi kamar za tayi kuka tace "kai Yaa Khalifa don Allah,kai da za kasa baki ya kaini shi ne kake zugashi" Khalifa ya ɗauke kai kamar ba da shi take magana ba,Mubasshir dake ta kallonta yace "sorry lil Sis,ki yi zamanki a nan har a tashi sai mu tafi" Muniba da lokaci ɗaya hawaye ya cika mata ido tai saurin kifa kanta saman table ta kama kuka,tana wannan yanayin Baniynah ta zo gurin,a hankali ta dafata tana kiranta "Sweetheart! What's up? Me yake damunki kika zo nan kika zauna?" Muniba bata kulata ba ta ci gaba da kukanta,ɗago kanta Baniynah tayi tana faɗin "what happened to u?" Ɗauke kanta tayi hawaye na sake rolling down daga idanunta,a rikice Baniynah ta janyo kujera ta zauna tana kallonta tace "Sweetheart! Don Allah me akai miki? Kukan me kike?" Yaa Khalifa ya tsaya kallon Muniba da mamaki jin kalmar kuka a bakin Baniynah,kafin ya maimaita yace "kuka!?" Baniynah tace "wallahi kuka take,me akai mata? Ita da waye please?" Khalifa yace "a'a na shagwaɓa take yi" Baniynah ta kalleshi ta kasa cewa komai,Mubasshir da yai suman zaune saboda mamaki yace "ok! Tashi muje na kaiki" da sauri ta miƙe dai² lokacin Lieut. Abuu Turab yai musu sallama tare da bawa su Mubasshir ɗin hannu sukai musabaha,idanunsa akan Muniba da ta sunkuyar da kai ta ƙi yarda ko kallonsa tayi,ya ɗan juya yana kallon Baniynah da ta tashi tsaye also,yana son yi mata magana amma sai yaga hankalinta duka na kan Muniba,riƙe hannun Muniba Baniynah tayi muryarta ƙasa² tace "Sweetheart please,don't go back home tun yanzu,ki bari har a tashi,kin san fa babu kowa a can,mene ne amfanin ki tafi ki zauna ke kaɗai? Kin san Mami taji za tai miki faɗa" Muniba ta kalleta ta maƙe kafaɗa sai dai bata ce komai ba ta ci gaba da share hawaye,Baniynah ta dage sai roƙonta take amma ta dage,handkey dake fidda wannan sihirtaccen ƙamshin nasa Lieut. Abuu Turab da ya gama jinsu ya ciro ya miƙa mata,da huskey voice ɗinsa da yayi sanyi yace "whippe up ur face ki zauna" she can't tells me ya faru,kawai ta amshi handkey ɗin ta share hawayenta,duk yanda kake kusa da su ba lallai ka iya cewa ga abunda yace mata ba,kawai suka ga ta koma ta zauna tana sake share hawayenta,shi kuma ya ja kujerar kusa da inda take ya zauna tare da kame kansa,sakin baki Baniynah tayi tana kallon ikon Allah,Mubasshir kam da Khalifa murmushi kawai sukai,Khalifa ya kalli Baniynah yai mata alamar tazo da ido,da ƙyar ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya sannan ta ja kujerar kusa da shi ta zauna,ƙasa² yace "kina mamaki ne?" Baniynah ta ƙifta idanunta tace "i'm speechless wallahi,na gama roƙonta ta ƙi ji amma daga yi mata magana har ta koma ta zauna kamar tsafi" Khalifa yace "this is what bature yake kira Power of love.." Baniynah ta gyaɗa kai kafin tayi murmushi. Da sallama Hammad yazo gurin fuskarsa a sake ya bawa su Mubasshir hannu suka gaisa har ƴan matan,they don't need any further explanation,kamanninsu da Lieut. Abuu Turab ya wadatar da su fahimtar waye su,Hammad dake murmushi ya zauna kusa da Lieut yana faɗin "Auntynah! Good evening" Muniba ta amsa masa ta kasa kallonsa,yana sakin murmushi yace "i'm so sorry for my mistake,i never knew.." Kafin ya ƙarasa Muniba ta saki murmushi,kamar wani abu bai faru ba ta girgiza kanta tace "babu komai.. I understand" Hammad yace "really?" Ta gyaɗa masa kai tare da lumshe kyawawan almond eyes ɗinta tace "Mmmm" yace "wow! Gaskiya u are way too soft,baki da riƙo sam.." Muniba tai ɗan murmushi kawai,Hammad yace "i'm Muhammad amma za ki iya kirana Hammad,junior broh na Lieut.. Dukanmu siblings ɗinsa ne,this is Husniyah and Abrar" ƴan matan sai murmushi suke suna kallon Muniba har suka gaisa tana musu murmushi me cike da kunya,ƙasa² suke magana da juna ba'a jinsu suna kallon Muniba sai kuma su kalli Lieut,Lieut da yai shiru kamar ba ya gurin duk yana jinsu,Muniba tace "Allah sarki! Nice meeting u" Hammad yayi murmushi yace "thank u.. But ban san sunan Aunty'n nawa ba,kada mu sake haɗuwa na rasa sunan da zan faɗa,kin san Aunty suna da yawa idan na faɗa ba lallai ki juyo ba ko ki san dake nake" Muniba tayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoranta tace "sure" Hammad yace "yawwa! Ur name please,na san dai yanda kike me kyau sunanki ma zai zama unique" duk maganar nan da suke yi bata iya kallonsa ba ta daure tace "Muniba" yace "maa sha Allah.. Kinga ban faɗi ba dai² ba ko?" Ya kalli Yayansa zai magana,Lieut yai masa wani kallo,dole tasa Hammad ya haɗiye maganarsa tare da fashewa da dariya su Khalifa suka tayashi,dole tasa Lieut. Abuu Turab yin murmushin da bai shirya ba kafin yai fuska.

WAZEER!Where stories live. Discover now