Rivalrous

74 12 1
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

     _Join our group domin samun update https://chat.whatsapp.com/LMWOmafckAGJoQ4ebkvdcG.._

    _Jinjinar girmamawa gare ku my co-writers,Mother's,Aunties,Sisters and brothers:Hjy Maryam Alhassan (Mamma),Na'eema Abdull Tafida (My Zarah) AKA Maman Baby'na,Binta Umar Abbale,Khadijah Candy,Jamila Umar (Janafty),Na'eema Sulaiman Shu'aibu (Nimcyluv),Fauziya Tasi'u (Oum Hairan),Autar Mama,Nazeefah Jikar Nashe,Ayushercool,Abeedatou (Maman Inayah),Muhammad Khareem,Yaa Hassan Atk,Yaa Hussain 80K,da sauran duk wanda ban ambata ba,especially ahalin cikin MIKIYA WRITERS,anjad shukraan'kthiir² ilaikum habibaatiiy,Allah ya biyaku da mafi kyawun sakamako.. Son so fisabilillah!❤️_

                               14

#Rivalrous

*WAZEER*

            Yana barin GRA kai tsaye unguwar Jambulo ya wuce cikin tricycle,rana ta farko a rayuwarsa tunda ya mallaki hankalinsa da zai iya Buɗe baki yace ya shiga motar haya da kankin kansa,duk sai yake jinsa wani iri,jikinsa yai sanyi ya shiga tunani da tambayar kansa "ya ya mutanen da basu mallaki abun hawa ba suke ji lokacin da uzuri ya taso musu? Shin idan basu da kuɗin hawa abun hawan uzurin gaggawa ya shigo musu,ya ya suke yi?" Yau ɗaya da yake ta zirga² a motar haya,har wani sabon imani ya dunga ji yana sake shigarsa,sosai tausayin talaka da rayuwar da yake ciki suka sa zuciyarsa yin rauni,gangar jikinsasa tayi laushi,tunda ya isa gidan suka gaisa da Mama da kuma Mimi ya zauna yayi shiru,nan gidan ya yini saboda bai son komawa gida su haɗu da Dad,ya san definitely ne sai ya tambayeshi inda yaje,da dalilin da yasa ya tafi without ya sanar masa,sai guraren maghreeba bayan ya yi sallah sannan ya yiwa Mimi da Grandma ɗinsa sallama zai tafi,Mimi ta rakosa compound suna ƴar hira tana tambayarsa "ina aka yi posting ɗinka ne service?" Yana ɗan lumshe idanunsa hannayensa zube cikin aljihun wandon shaddar dake jikinsa yace "ban duba ba tukuna" Mimi tace "alright!" Ganin babu motarsa da ya saba zuwa a ciki yasa ta sake kallonsa,ya ɗan tsaya a hankali kamar bazai ce komai ba yace "Mimi bari naje" Mimi dake son tambayarsa tace "a ina ka bar motar naka? A waje kayi parking? Me yasa baka shigo da shi ba?" Girgiza kansa yayi kaɗan yace "ban zo da mota ba" Mimi na kallonsa da kyau tace "me yasa? Wani abu ya samu motar naka? A me ka zo?" Ɗan murmushin da iyakarsa saman laɓɓansa yayi yace "me tricycle ne ya sauke ni" Mimi tace "motar naka ya samu matsala ne?" Yana girgiza mata kai yace "um'um! Mun fita da Dad a motarsa,daga can ban koma gida ba na sauka na taho nan" Mimi na gyaɗa kai tace "ok! Toh yanzu a motar hayan za ka tafi?" Yace "Mmmm" Mimi tace "um'um! Bari na baka nawa motar ka tafi da shi,sai kasa a kawo min daga baya" girgiza kansa yayi yana lumshe idanunsa yace "no Mimi,zan tafi a tricycle,akwai inda zanje yanzuma" Mimi tace "a'a ka karɓa kaje da shi" yayi murmushi kaɗan da ya ƙara masa kyau yace "Mimi sai anjima,i'm getting late" daga haka ya fara tafiya cikin ɗan sauri²,Mimi tace "ba sai ka yi ƙoƙarin guduwa ba,na san dalilin da yasa baza ka karɓi motana ka tafi a cikinsa ba,saboda kada mahaifinka ya gani ya tambayeka ne kou?" Gyaɗa mata kai yayi murmushi na sake bayyana a fuskarsa,komai yayi bala'in kyau yake masa,Mimi tace "ai shi kenan.. Ka gaida gida da su Daada" yace "za su ji.." Sai da Mimi taga fitarsa daga gidan sannan ta koma ciki. Wazeer na isa bakin link ya samu me tricycle,yana tsayar da shi ya shiga yace "dai² gidan Wazirin Kano za ka saukeni" me tricycle yace "tou Galadanci ko?" Wazeer yace "um'um! Tudun wuzirci" me napep ya ɗan juyo yana kallonsa yace "Galadanci dai ko?" Wazeer ya ɗaga idanunsa ya kalleshi,kamar bazai ce komai ba ya gyaɗa kansa yace "Mmmm! Nan" me napep yayi murmushi yace "ai na san unguwar sosai,da alama kai baƙo ne ko me gida?" Wazeer dai bai ce masa komai ba,me napep ya tada machine ɗin suka kama hanya,suna tafiya yana ta yiwa Wazeer surutu,shi dai bai ce komai ba bayan damunsa da mutumin yayi,sai dana sanin shiga tricycle ɗi da yake ta yi,ga surutunsa sai hawa masa kai yake,amma ko kaɗan bai buɗe baki yace masa ya yi shiru ba,suna kawowa Tudun wuzirci ya sauka ya sallamesa,bai tsaya jiran jin komai ba yayi tafiyarsa. Ya ci babbar sa'a da bai tarar da Dad a gida ba,a gaggauce ya wuce bedroom ɗinsa,wanka da alwala yayi sannan ya fito,har ya gama shirinsa na tafiya dinner cikin tsadadden shaddarsa light brown,da aka yiwa ɗinkin zamani sai royal cap daya saka kansa,ƙafarsa a cikin half royal cover shoe dake nan kalar hularsa sak,duk kushen mai kushe,da hassadar mai hassada bai isa ya kushesa ko yace ya gano wani aibu tare da shi ba,yana fitowa gidan ko ɓangaren Daada bai tsaya shiga ba ya wuce masjid,ana fitowa sallar ishaa daga masallaci ya nufi titi sai wani irin ɗan banzan ƙamshi yake tafiya yana barwa mutane a hanya,tricycle ya tare ya sanar masa gurin da Safwa ta turo masa text tun yana Jambulo,me napep ya amsa masa ya shiga suka bar unguwar.

WAZEER!Where stories live. Discover now