Vie

80 13 3
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

        _Follow my account on arewabooks @Realsmasher or https://www.arewabooks.com/u/realsmasher.._


                               12

#Vie

                Kusan raba dare sukai suna hira,kowa na tsimayin ganin gobe,da shiryawa ranar saboda rana ne da kowa zai kece raini,shi ne ranar da kowa yafi ciwa buri a duka ranakun bikin,gayyar da Safwa tayi na ɗaurin aure ko su Baniynah albarka,kuma duka cards ɗin dinner da take shirin karɓa,wanda sukai mata hidima take so ta gayyata,mutanenta ne na groups da take a WhatsApp da samarinta. Around 12am na ranar Saturday,kasancewar dare ko ina yai shiru,mutane duk sun kwanta bacci,su kaɗai ne dai ƴan matan da suke ɗaki kowa da waya a hannunta tana chat,Safwa ta buɗe contact ɗin Aley tai masa sallama,luckily ta sameshi online,cards na ɗaurin aure ta tura masa tas tare da saƙon gayyata,har da ɗan saƙon dake nuna lallai² ya zo,idan yaƙi amsa gayyatar da tai masa ta tabbatar bai ɗauki friendship ɗinsu da muhimmanci ba,kuma itama ta san ba ta da wani matsayi a gurinsa.

*WAZEER*

        Tun da ya shiga part ɗinsu yai wanka,kasancewar tun suna hanya aka sakko masjid,yana gama shiryawa yai sallar zhuhur,ko abinci bai tsaya nema ba ya kwanta,sanyayyar iskar ƴanci da rahama na gida da ya shaƙa,nan da nan ya saukar masa da kasala tare da wani irin gajiya me cin jiki,yana son fita yaje aski saboda yanda ya tara gashi,amma yanda yake jin kansa yai nauyi ba ya gane komai dole tasa shi ya kwanta,bai jima ba wani irin ƙaƙƙarfan baccin da ya jima rabon da ya samu irinsa ya ɗaukeshi,ba shi ya tashi ba sai ana kiran asr,ba kaɗan ba ya ji daɗin hutun da ya samu,kansa yai fayau babu damuwa da nauyin komai,wanka ya sake yi tare da alwala ya shirya cikin ƙananan kaya da suka amsheshi,daga masallaci ana idar da sallah yana fitowa ya shiga motarsa ya wuce zoo road,aski da sauran abunda baza'a rasa ba akai masa,daga nan yana barin plaza ya wuce jambulo,bai sanar da Mimi ya dawo ba,duk da a ranar sun yi waya da ita da safe,sai dai da wasa bai ce mata yana hanya ba,yana shigowa compound ɗin gidan yayi parking,ya sauko ya nufi entrance tare da yin knocking,Mimi dake zaune parlour ita da Mama suna hira ta ƙwaloma me aikinsu Kubra kira "Kubra!" Kubra ta fito da sauri respectfully ta durƙusa nesa kaɗan tace "ga ni Aunty" Mimi tace "duba waye yake knocking.. Think bazai wuce Little Abuu Turab ba,yanzun nan muka gama waya da Aunty Zainab ta ce min ta aikoshi" Kubra tace "toh Aunty" ta tashi da sauri ta tafi,tana buɗe ƙofa Wazeer ya kalleta fuska ɗaure tamau,da sauri Kubra ta matsa tana cewa "sannu da zuwa" Mimi ta waigo don ganin waye Kubra ke yiwa sannu da zuwa,Wazeer ya shigo da sallama,haɗa ido suka yi da Mimi ta ɗan waro idanunta cike da mamaki tace "Zakin Mimi! Yaushe ka dawo?" Yana kallonta a taƙaice yace "yau" Mimi tace "amma shi ne baka sanar min ba ɗazu da mukai waya?" Mama dai kallonsu take tana murmusawa,ya durƙusa gabanta bayan ya iso yace "barka da yamma Mama" Mama tace "barka dai Abuu Turab.. Ka dawo lafiya? Ya hanya da mutanen gidan naku?" Yace "lafiya lau alhmdllh" Mama tace "maa sha Allah.. Allah ya taimaka,yayi maka kyakkyawan jagoranci" Mimi da shi suka haɗa baki gurin cewa ameen,Mimi dake ta kallonsa ya gaisar,tana masa wani kallo cike da so tace "ka dawo lafiya?" Ya amsa a gajiye,cike da zolaya tace "na ga ka yi ƙiba ka ƙara kyau,da alama zaman camp ɗin ya karɓeka ko?" Buɗe baki yayi cike da mamaki ya kasa cewa komai,lokaci ɗaya ya shagwaɓe fuska kamar zai yi kuka yace "Mimiiiii!" Mimi tana ƴar dariya tace "Mama kalleshi kiga,bai ƙara ƙiba ba?" Mama na girgiza kai tace "a'a Hoor baza kisa nayi ƙarya ba,yaro ya rame yai duhu kamar ba shi ba saboda yanda ya fita hayyacinsa kice ya yi kyau? Allah na tuba indai irin abubuwan da kika bani labarin suna faruwa a gurin nan,ai dole a tausayawa duk mutumin da yaje gurin ya fito da ransa" Mimi tace "kai Mama namiji ne fa,dan ya je Camp ya ɗan sha ƴar wahalar nan kike goyon bayansa,kawai dai an shagwaɓa shi ne,amma dole ya saba da wahala,saboda nan gaba kaɗan zai yi aure ya ajiye iyali.." Mama tace "duk da haka wallahi ni dai na jinjina masa,ka yi ƙoƙarin sosai² Abuu Turab,Allah ya kawo aiki me kyau da mace ta gari.." Mimi tace "ameen.." Abinci da drink Kubra ta kawo masa,Mimi na kallonsa tace "sauko ka ci abinci Zaki" kamar zai ce ba ya ci,kuma sai ya tuna ai bai ci abinci ba duka yinin yau tunda ya dawo,ya sauka saman rug ya zauna,Mimi ta sauka ta fara zuba masa,yace "Mimi ya isa" ta kalleshi da sauri tace "wannan abincin me zai maka?" Ta sake ƙara masa,shi dai bai sake cewa komai ba,yayi bismillah ya fara ci,yana gamawa ya tashi,Mimi tace "ka je ka gaida Uncles ɗinka ko?" Ya gyaɗa mata kai yace "toh!" Mama na kallonsa tace "anya zai gane gidan kuwa,da kike cewa yaje? Ai da kin kira an turo yaro sai ya tafi da shi ko?" Mimi tayi murmushi tace "Mama bazai gane ba fa kika ce? Ai ya taɓa zuwa" Mama tace "duk da haka,sau ɗaya ne fa kawai" duk maganarsu yana jinsu,ya buɗe baki yai magana abu ya zama aiki,sai da ya miƙe tsaye tukuna yace "Mimi bari naje na dawo" Mama ta kalleshi tace "za ka iya zuwa? Ko dai a turo yaro yazo ya tafi da kai?" Yana ɗan girgiza kansa yace "zan iya zuwa" Mama tace "toh shi kenan,a gaishesu.. Idan kuma baka gane ba ka dawo,ka ji kou?" Ya amsa a ciki tare da wucewa ya fita. Yana barin gidan Mimi tace "ai na faɗa miki zai iya zuwa dama" Mama tace "ai ni na ɗauka bazai gane gidan bane,saboda sau ɗaya ya taɓa zuwa,kuma ga shi hanyar duk an yi gine² sababbi" Mimi dai tayi murmushi kawai,ita ta san yaronta,Abuu Turab ɗinta na da ƙoƙari sosai,sau ɗaya yaga abu ko yaji an faɗa ya riƙe shi kenan,tunda ya tafi bai dawo ba sai da yayi sallar maghreeeba,yana shigowa Mama tace "me sunan Waziri kuma ka gane gidan?" Yace "Mmmm" Mama tace "Allah sarki.. Sannu da ƙoƙari,ka same su lafiya?" Yace "alhmdllh" Mama tace "Allah ya rubuta ladan zumunci,yayi maka albarka" Mimi data amsa ya ɗan kalla,sai daɗi take ji tana kallonsa tana murmusawa,yace "Mimi zan tafi" Mimi tace "toh shi kenan,na gode sosai da ziyara" ya gyaɗa mata kai,sannan a hankali yace "Mama a tashi lafiya" Mama tace "toh Abuu Turab.. Allah yayi albarka,Allah ya kaika gida lafiya" yace "ameen" Mimi ta tashi ta biyoshi a baya,sai data rakashi har gurin motarsa,bata bar compound ɗin gidan nasu da yi masa waving ba,har sai da motarsa ta fita gidan sannan ta koma cikin gida. Yana yin parking garage,ya sauka motar ya wuce cikin gida,da sallama a bakinsa ya shiga ɓangaren Daada,duk da a ciki² yayi amma bai sa Daada ta kasa ji ba,ta amsa tana faɗin "Zainul-abideen ina ka shiga haka ni Sa'adatu? Tunda ka dawo nake ta sauraron shigowarka,baka zo ka ci abinci ba kuma baka sa azo a karɓar maka ba" yana zaunawa saman kujera yace "na fita aski ne" Daada tace "toh! A kawo maka yanzu?" Yace "um'um" ta kalleshi da kyau tace "toh ka ci a wani wajen ne?" Yace "ehh" Daada tace "toh ai shi kenan.. Yanzun nan kuwa babu jimawa Mamman ya shigo yana tambayar ina kake?" Ya kalli Daada da sauri yace "Dad ya dawo?" Tace "ehh ya shigo babu jimawa,bai daɗe ba ya fita ya tafi can gidan naku,ina jin kai ya tafi nema tunda ya tambayeni nace kana can" miƙewa yayi yace "sai da safe" Daada ta bishi da kallo baki buɗe tace "mu kwana lafiya.." Yana barin gidan ya wuce ɓangarensu,sanda ya buɗe ƙofa ya shiga,Dad dake zaune parlour sanye da jallabiya ya ɗago yana kallonsa,murmushi kwance a fuskarsa yake kallon ɗan nasa yace "welcome back My dear" Wazeer ya ƙarasa ya zauna kusa da shi yana faɗin "good evening Dad" Dad yana shafa kansa yace "evening,how are u? Ya camp?" Wazeer ya kalleshi fuska babu walwala yace "alhmdllh" hira Dad ya dunga jansa da shi,amma bai cewa komai bayan um ko um'um,har akai kiran ishaa suka fita masallaci sallah,suna dawowa kuma suka zauna parlour,aka kawo musu abinci daga ɓangaren Daada suka ci,suna gamawa Wazeer ya yiwa Dad ɗinsa sai da safe ya wuce ɗakinsa,yana shiga ya cire kayan jikinsa ya wuce bathroom,yana fitowa ya saka lightweight kayan baccinsa ya fesa turarukansa masu sanyi ya hau gado,MacBook ɗinsa da tun kafin ya tafi camp ya kashe ya barshi a gida yaja ya kunna,sama² ya ɗan kalli Korean film da yake dasu,guraren 12am sannan ya kashe ya buɗe data na wayarshi ya shiga WhatsApp,a nan yaci karo da saƙonnin Safwa,ya buɗe yana kallon abunda tace,a hankali ya ɗan taɓe baki,ko me ya tuna kuma kawai ya rubuta mata "in sha Allah zan amsa gayyatar da akai min.. This is my promise.." Yana turawa ya kashe network ɗin wayar,har ya yi silencing ya ajiye wayar,kamar wanda aka kama kunnensa aka tuna masa wani muhimmin saƙo ya sake ɗauka,for the first time yai saving number wata ƴa mace bayan Mimi da grannies ɗinsa.

WAZEER!Where stories live. Discover now