Thought pattern

93 11 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

        '''I really missed u Sis Zarah Abdull Tafida AKA Maman Baby'na Ikraam,Allah yasa kina cikin aminci da kiyayewarsa..😪🦋💖'''

       _Sorry for the late update,na yi typing editing ya gagara kusan kwanaki,Zarah Abdul ga update nan,na ji kokenki kuma ƙorafi ya karɓu,banda kin yi magana ban san sai yaushe zan yi editing ba wallahi,ku ƴan Wattpad kuna son update,amma abunda ke muku wahala comments,to ko baku yi ba ma ɗan voting ɗin nan idan kuka yi zan san kun gani kuma kun yaba min,su dama WhatsApp ba'a ta su,sai dai kaji muƙus kawai malam..🤭😂_
      

                               26

#Thought pattern

          Radhiya tace "ƙawata! Dabara fa ya ragewa mai shiga rijiya.." Safwa tace "kamar ya? Ni ban gane me kike son faɗa min ba,kin san Hausar nan ni ba wani iyawa nayi sosai ba,musamman proverbs ɗin nan masu shegen kulle kai" Radhiya ta sauke ajiyar zuciya tace "abunda nake son cewa a nan shi ne,ki yi istikhara ki nemi zaɓin Allah tsakaninsu biyun,ko Aliyu ko Hamood Waziri,duk wanda Allah ya baki ki karɓa kiyi addu'ah,think tun farko baki yi ba,kuma na san kin san yin yana da amfani" Safwa ta gyaɗa kanta a hankali tana ɗan yatsina fuska tace "ehh! Zan sa ayi min" Radhiya tace "whatttt? Wa yace sawa za kiyi ayi miki? Ke fa za kiyi da kanki.. Didn't know how za kiyi? An yi mana fa a islamiyya,mene ne abun wahala a ciki?" Safwa tace "shi kenan zan yi" Radhiya tace "please kiyi ƙoƙari ki yi,sai kisa a miki bincike kan shi Aley,gidansu da komai da ya shafesa,a haka dai ina kallonsa as mutumin ƙwarai me gudun duniya,ina ganin kyawawan halaye da ɗabi'u tattare da shi,i don't want u to miss him" Safwa tace "toh!" Radhiya tace "and i will include u in my daily prayers nima" Safwa tace "thanks ƙawata" sun yi magana sosai kafin su yi sallama,tana katsewa kiran Hamood Waziri na shigowa,sanda ta ɗauka suka gaisa,jikinta a sanyaye tace "when are u coming back dear?" Cikin taushin murya Hamood yace "do u want to meet up?" Safwa tayi shiru kafin ta gyaɗa kai kaɗan kamar tana gabansa tace "ehh" yayi ɗan murmushi me sauti yace "ok! I will be back soon,hope idan na zo zan samu labari me daɗi?" Safwa tayi shiru kaɗan,sai kuma ta sake gyaɗa kai tace "ehh" yace "wow! Allah yasa,in sha Allah will be on my way in the next few days" Safwa tace "ok! Allah ya dawo da kai lafiya" yace "ameen² thanks" daga nan sukai sallama ta sauke wayar,sai kuma tayi shiru tana tunani. Buɗe ƙofar da aka yi yasa ta ɗago kanta,Umma ce ta shigo ɗakin tana kallonta tace "thought kin kwanta" Safwa ta ɗan girgiza kai tace "a'a! Na amsa waya ne" Umma ta zauna next to her tana sauke ajiyar zuciya tana kallon ƴar tata ta kirata "Safwa!" Safwa da jikinta ke a sanyaye,zuciyarta na mata babu daɗi,tunani da yawa sun cunkushe mata kai,ƙwaƙwalwarta ta rufe ruf akan al'amarin dake gabanta,ta daure tace "na'am" Umma ta kai hannu ta dafa laps ɗinta,muryarta cike da lallashi tace "za mu iya yin magana yanzu?" Safwa ta gyaɗa mata kai tace "why not?" Umma tace "ok!" Tana tattaro abunda ke zuciyarta tace "me yasa baza ki bar maganar Aliyu ki amshi Hamood Waziri ba,mmm? I think kin gani kuma kin fahimci inda za kije ba ke kaɗai ba har muma iyayenki da ƴan uwanki za mu huta,tun daga haɗuwarku zuwa yau akwai rana ɗaya da Hamood Waziri zai zo ya tafi haka ba tare da ya kawo mana abubuwan arziki ba? Kyauta ma kina ganin yanda yake yiwa ƴan uwanki da mu kanmu.. Shin me tarayyarki da Aliyu ya tsinana miki? Me kikai gaining? In fact me na sama ma yaci bare tsinko jeho min? Ke ko mu babu wanda ya taɓa cin ƙwandalarsa,ina jin ko ɗan katin nan ma bai taɓa sa miki ba,bare kyautar nan da ake yi,nan har girki kike masa yazo ya cinye ya tashi ya karkaɗe jallabiyarsa yayi gaba.. Wallahi Safwa ina jiye miki ki nace akan lallai sai yaron nan,azo ayi aure kije wahala yasa ki lalace,ina tabbatar miki akai aurenku a haka kullum sai kin zo mana kina baran mu taimaka muku da abincin da za ku ci.. Ke ni banma yarda da yaron nan ba gaba ɗaya,don da yana da gaskiya da bai ɓoye miki asalin ko waye shi ba har zuwa wannan lokacin,sai dai kullum yazo ya ɓata miki lokaci ya kwashi girki yayi gaba.. Ina dalili?" A hankali Safwa ta ɗaga kanta ta kalli Umma tace "Ummaaaa!" Umma tace "ai maganar gaskiya nake faɗa.. Don haka ya kamata ki zauna kiyi nazarin maganata,kin san dai babu yanda za'ayi ace ina mahaifiyarki naso abunda zai cutar da ke,bazan ma iya ganin abun cutarwa a inda kike na bari ya tarar da ke ba tare da na yi yanda zan yi na kawar miki shi ba.. Yanzu fa 5 days ya ƙare cikin kwana 7 da Babanku ya bashi,amma shiru babu wata magana,ke da ganin haka ai kin san bazai iya bane ya cika wandonsa da iska,ai gara da Baban naku ya masa maganar ma tun ba'a je ko'ina ba,da haka zai ɓata miki lokaci a banza.. Don haka idan za ki yiwa kanki faɗa tun ba'a yi nisa ba ki yi,in kuma auren ne baki shirya yi ba,ga fili nan sai ki zo muyi ta zama daga nan har mahadi ya bayyana,amma wallahi kin ji na rantse miki kikai saken da Hamood Waziri ya suɓuce miki kin tafka asara ba ƴar ƙarama ba,kuma na tabbatar baƙin ciki kikaiwa kanki da mu.." Umma na faɗin haka ta miƙe ta fice cikin ɓacin rai. Sakin baki Safwa tayi ta bi Umma da kallo with suspicion,ɓacin ran data gani ya fi komai tsaya mata a rai ta shiga faɗin "akan ƴar maganar nan ne ranta ya ɓaci?" Taɓe baki tayi a hankali ta furta "to wai ba sai ina sonsa zan bashi dama ya aureni ba? Naga dai ban rasa masu so na ba.. Ha'ah!"

WAZEER!Where stories live. Discover now