Break away!

94 5 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2024.



*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*TIKTOK:ASLISMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*


                               30

#Break away!


*WAZEER*

          Tun ranar da ya baro gidansu Safwa walwala da sukuni sukai masa ƙaranci,ba ido biyu ba hatta a bacci mafarkin cin mutuncin da tayi masa yake,tun yana ɗaukan al'amarin da sauƙi har abubuwa suka fara dagule masa,idan ya fita aiki bai da nutsuwa,haka idan yana gida ma babu sukuni,ya yi iya yinsa na ganin ya sauƙaƙawa kansa tunanin abubuwa da yawa amma al'amarin ya gagara. Zaune yake ya yi nisa cikin tunanin hanyar da zai bi ya shawo kan matsalar data sako shi gaba,wayarsa dake ajiye yake kallo jikinsa duk babu daɗi,bazai iya lissafa adadin kiran da ya yiwa Safwa ba a cikin kwanakin nan da suka tasarwa sati ɗaya,haka nan saƙonnin ban haƙuri suma ya aika mata su babu adadi sai dai ko guda ɗaya bai samu amsarsa ba har kawo yanzu,ya je ƙofar gidansu ya aika a kirata ta ƙi fitowa. Gwauron numfashi ya sauke a lokacin da zuciyarsa ke sake bashi shawarar ya sake jarraba kiranta,wayar ya ɗauka yayi dialing number ɗinta,luckily wayar yana shiga ta ɗauka da faɗin "don Allah Malam wai me kake nema a gurina ne? Na faɗa maka aure zan yi ka ƙi ka barni na huta,sai damuna kake da kiran da ba zai min amfani ba,idan ba so kake nasa a ɗaureka har buzunka ba ka daina kirana don Allah,i'm getting married in the next few days,kar ka ƙara kirana ba na so na faɗa maka" za ta yanke kiran da muryarsa da yayi sanyi yace "Safwa don't hang up.. Na ji za kiyi aure,and ba wai yarda ne ban yi ba,but please say a word kin yafe min ɓata miki lokacin da nazo nayi,that's all i need from u,daga haka in sha Allah bazan sake neman komai daga gurinki ba,ni musulmi ne na yarda da ƙaddara,na san nema cikin nema it's Haram a addininmu,besides Allah bai hukunta cewar ni dake will became spouse ba,so ina miki fatan alkhairi,Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba" siririn murmushi Safwa ta saki da bai taɓa tunanin za tayi ba,ta amsa da "ameen.. Thank u" a hankali ya lumshe idanunsa da suke zafi yace "and pardon me please" tace "i have forgiven u Aley,Allah ya baka mace ta gari,wacce za ta soka a matsayin da kake" yana gyaɗa kansa yace "ameen yaa hayyu yaa ƙayyum.. Thank u so much Safwa,Allah ya sadamu da alkhairi" tace "ameen.. And u are invited to join us,ai za kazo ko?" Yace "in an gayyace ni zan amsa in sha Allah" tace "toh! When are u coming ka amshi cards ɗinka?" Yace "whenever you want me to" tace "ok! Kazo gobe ka amsa,yau ba na gida na je gyaran jiki" yace "ok! Allah ya kaimu" tace "ameen.. Sai ka zo" yace "in sha Allah!" Ita ta fara hanging kiran,Wazeer ya sauke nauyayyar relieved ajiyar zuciya,har ga Allah bai taɓa shiga damuwa ba sai a dalilin Safwa,but for now yana jinsa kamar bawan da aka ƴanta,don ko babu komai ya sauke nauyin dake wuyansa na hakkin Safwa,sake lumshe idanunsa yayi tare da adjusting zamansa saman swivel chair da yake kai ya shiga juyi yana tasbihi tare da istigfaar ga Allah,ya jima a haka kafin ya miƙe saboda wani azababben baccin dake ci masa idanu,a hankali ya tattara all his belongings ya fito office zuwa elevator,gida kawai yake son wucewa don dama lokacin tashinsa ya yi tuni kawai dai bai son komawa ne yanzu da wuri saboda yawan tunane² da yake addabar kansa da yi,hakan kuma ba kaɗan ba ya taɓa lafiyarsa a cikin kwanakin,don dole ya dawo ta'ammali da glass ɗinsa saboda yanda ganinsa ya samu rauni. Sanda ya iso gida yana yin parking ƙofar gida ya sauko mota ya wuce ciki,zaure babu kowa yau sai shimfiɗun da Abba ke zama,da alama ba ya nan ya fita wani uzuri ko gidan Sarki,ɓangaren Daada da akaiwa gyara aka canja komai ya iso da sallama a bakinsa,cikin kwanakin nan yanayin abubuwan da suke faruwa ko da ba ya zama,sannan bai damu da ya san me ake ciki ba,ya tabbatar masa akwai abunda zai faru a gidan,Daada dake zaune suna hira da hadimanta cikin sakewa ta ɗago kai tana amsa masa "ameen wa'alaikumus salaam warahmatullah wabarkatuh!" Wazeer ya ƙarasa tare da zama saman kujera yana gaisheta,ta amsa masa da kulawa tana faɗin "ya aikin Zainul-abeedin?" Yace "alhamdulillah!" Tace "sannu da ƙoƙari Zakin maza,Allah ya yi maka jagora,ya zama gatanka a ko da yaushe" hadimanta da shi suka amsa tare "ameen" bai jima ba ya miƙe yana cewa "sai an jima" Daada tace "Allah ya nuna mana da rai da lafiya" yana sawo kai waje suka kusan cin karo da Dad,tsayawa yayi saurin yi tare da bawa Dad hanya,Hamood dake cikin sauri yace "Son! Ina ka shiga kwana biyu?" Wazeer yace "ina nan" Dad da ya tsaya also yace "kana nan a ina? I've been trying to get u,duk safiya kafin na shigo ka fice,and da dare ba na sanin ka shigo,anya kana kwana gida ma?" Wazeer yace "sure Dad" Hamood na girgiza kansa yace "i'm not sure kana kwana gida,ina ka tafi ka zauna kwanakin nan?" Cikin ƙosawa da magana Wazeer yace "Dad ni banje ko'ina ba,kai ne dai baka ganina amma su Daada ai sun san ina nan" Hamood yace "ok!² Yanzu ka jirani a gida za muyi magana,bari na ga Daada na fito" Wazeer yace "ok!" Daga haka ya wuce apartment ɗinsu Dad kuma ya shiga gidan Daada.

WAZEER!Where stories live. Discover now