Force play

80 6 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                    (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated, & #Lost..*


                               03

#Force play

                  Da wani irin babban shock ɗin da taji har cikin ƙwaƙwalwar kanta ta dunga kallonsa,shiru ya ratsa tsakaninsu na wani lokaci kafin tai gathering courage tace "Hamood! What are u saying? Ka me kace?" Yana kallonta da kyau yace "i just said it out loud,ba zan maimaita ba,and i mean it.. Na sake ki saki ɗaya.." Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai ta iya furtawa tana kallonshi a tsorace,she can't believe ita Hamood yake cewa ya saki,saki dai divorce da take ji ana faɗa a gari miji ya yiwa matarshi? Irinsa yake nufin ya mata itama? Abunda a rayuwarta bata bata taɓa kawowa zai faru a tsakaninsu ba,saboda ta san Hamood yana matuƙar sonta,kuma itama tana sonsa domin kuwa auren soyayya sukai,a kiɗime idanunta na tsiyayar da hawaye tace "Hamood ka sakeni fa kace!? Akan wane dalilin? Wane laifin nai maka dana cancanci saki daga gareka? Tell me abunda nai na kuskure da yasa ka sakeni da daren nan? Ina kake so naje yanzu?" Yana fesar da zazzafar iska daga bakinsa ya kafeta da mayun idanunsa yace "baki san laifin da kikai ba kika ce?" Da sauri ta gyaɗa masa kai tace "wallahi² ban san me nai maka ba" yace "sakaci.. Hoor ke wace irin uwace da bata kula da ƴaƴanta? Saboda ba na ƙasar kin sakar min yara a hannun me aiki,ita ta haifar miki su da ko'ina kikai sha'awar zuwa za kiyi ficewarki ki barsu tare da ita? A yau na tabbatar ba don sakacinki ba da Mysha bata mutu ba,da ƴata tana nan kusa da ni" da muryar kuka tana girgiza masa kai tace "but kada ka manta Mysha is my daughter also,ina sane zan bari wani abu ya sameta? Ko babu komai ni nai rainon cikinta na haifeta,shin zan kashe ƴata ne da hannuna? Zan so wani abu ya faru da ita? I am her mother zan fi kowa jin ciwon mutuwarta,kuma kou dazan fita sai da nasa Suwaiba taje ta ɗaukota a duk inda take ta dawo da ita gida su zauna.. Idan har za kaga laifina,su sauran mutanen gidan me yasa da suka ga ta je nemanta basu yi tunanin kirana suji kou na tafi da ita ba? I think bai kamata ka ɗaura min laifi ni kaɗai ba.. Ehh naji na yi kuskure kuma nima na bawa kaina laifin rashin tabbatar da inda take,amma hakan ba yana nufin ni na kasheta ba" so pissed off yace "Hoor! U killed her with ur very own hands,son yawonki da rashin kulawarki shi ya janyo na rasa ƴata" Hoor tace "stop saying this Hamood ni ban kasheta ba,da kake cewa ina son yawo har ina da ina naje? A duka tsayin shekarun nan da mukai aure,ina nake zuwa ba da izininka ba? Ina ma nake fita naje idan ba ya kama uzirin dole ba? Mahaifiyata fa na kira na sanar maka anyi admitting a hospital,kuma ka sani tunda na kiraka,ban bar gidan nan ba sai da cikakken izininka,ina dawowa Suwaiba ta fara tambayata Mysha" idanunsa ya lumshe kanshi na matuƙar sarawa kamar zai rabe saboda damuwa,a hankali yace "enough Hoor.. I don't want to hear any surutunki a nan,kije kawai sai da safe.." Tana gyaɗa kanta cike da ƙarfin hali tace "and maganar sakin?" Yace "till tomorrow morning.." Kallonsa ta dunga yi daga inda take,kafin tai ƙarfin halin juyawa tai hanyar ƙofa kuka na zuwar mata,da wanne Hamood yake so taji fisabilillah? Mutuwar ƴarta? Kou kuma sakin da yai mata da daren nan? Babu alamar dake nuna mata cewa da wasa yake mata bata ganshi ba sam,banda share hawaye babu abunda take har ta shiga bedroom ɗinta,ƙafafuwanta sun mata nauyi,zuciyarta a cunkushe da tunani iri²,ta rasa ma wane kalar zare za ta kama ta saƙa,a hankali ta raɓa saman gadonta ta kwanta kusa da ɗanta ko za ta samu sassaucin raɗaɗi da damuwar da take ciki,hawaye masu zafi da ciwo suka ci gaba da gangarowa daga idanunta suna sauka saman pillow data ɗora kanta,a tarihin rayuwarta wannan daren shi ne dare na uku da ya zama me muni da ciwo gareta,kukan da tayi a ƴan kwanakin nan tunda ta taso a rayuwarta bata taɓa kamarsa ba,ita data taso cikin maraicin rashin uba kenan,tun tana jaririya abbansu ya rasu,bata san zafin mutuwarsa ba sam,sai dai bata rasa gatan uwa da ƴan uwa ba,Yayyunta 3 duka maza,ita kaɗai ce mace kuma Auta,lokacin data taso duk sun kama gari,ɓatan ƴarta da mutuwarta shi ne abu na farko da ya girgiza duniyarta,har akai kiran farko tana nan kwance kukan kansa ta daina sai ajiyar zuciya kawai da take saukewa,bata san ma wane irin tunani take ba,sai da akai kiran assalat sannan ta tashi da ƙyar,kanta kamar zai faɗo ta sauka gadon tana kallon Abuu Turab dake ta bacci numfashinsa na sauka peacefully,a hankali ta miƙe tana riƙe kanta ta shiga bathroom,a daddafe tai wanka tare da ɗauro alwala ta fito,doguwar riga tasa tai sallah bayan ta idar tai addu'o'inta,tana zaune ta jinginar da kanta da gado tana tunani har gari yai haske,tashi tai tana tafiya a hankali ta ƙarasa gaban gadon tana shafa fuskar Abuu Turab dake bacci,a hankali ta shiga kiranshi "Zaki! Abuu Turab!! Babana!!! Wake up" motsawa yayi a hankali yai miƙa kafin ya shiga buɗe idanunsa,Mimi tai masa murmushin ƙarfin hali tace "tashi muje nai maka wanka sai kayi sallah" turo baki yayi a hankali yace "Mimi zan yi da kaina" girgiza masa kai tayi tace "um'um! Tashi muje nayi maka" yace "Mimi ni fa na girma,zan iya yi da kaina" tace "a'a idan ka ƙara girma kaɗan za kayi,tashi muje za mu tafi unguwa" ɓata fuska yayi kamar zai mata kuka yace "ina za muje?" A hankali tace "gidanmu gurin Grandma Mamana" kallonta ya tsaya yi sai kuma ya janye duvet ya sauka yace "zanje Mimi,na fi son gurin Mama" tai murmushin ƙarfin hali tace "alright!" Daurewa kawai take amma ita kaɗai tasan meke damunta deeply,suna shiga bathroom ta kai hannu gurin da brushes ɗinsu suke,akan brush ɗin Mysha idanunta suka fara sauka,nan da nan hawayenta suka fara sauka,kamar yau ne ranar mutuwarta haka ta dunga jin ƙirjinta na mata zafi,Abuu Turab dake tsaye bayanta ɗaure da baby towel nasa yana jiran ta bashi brush,ya taho ya riƙe mata hannu ganin yanda tai poster a gurin tana ta kallon brushes ɗinsu,cikin sanyin halinsa yace "Mimi is everything fine? Why are u always crying?" Saurin goge hawayenta tayi tana kallonsa tace "i'm fine Zakin Mimi.. Kawai na tuna Mysha ne" idanunsa akanta yace "ina take Mimi? Tun ranan nan da taje gurin Daada ban kuma ganinta ba" a hankali Hoor da wasu sababbin hawaye ke saukowa fuskarta tace "Mysha is gone.. Far² away,ta tafi inda baza mu sake ganinta ba" sai kuma ta fashe da kuka,ciccikowa idanunsa sukai da hawaye yace "Mimi ina ta tafi? Waye ya tafi da ita? Dad!?" Girgiza masa kai tayi tace "no.. She's dead.. Su Dad sun kaita gidanta na gaskiya sun binneta" kuka ya fashe da shi yace "Mimi nima zanje,kice da Dad ya kaini gurinta,i know she'll be there and cry alone,zanje gurinta na dawo da ita Mimi" saurin durƙusawa tayi on her knees ta rungumeshi tana kuka yana yi tace "babu wanda zai iya bin wani domin ya dawo da shi,idan mutum ya mutu ba ya taɓa dawowa,shi kaɗai za a binneshi a cikin kabarinsa,aikinsa na alkhairi ne kawai zai zama abokinsa har zuwa lokacin da Allah da kansa zai yi umarnin a tashemu dukanmu" Abuu Turab da bai taɓa sanin wani abu mutuwa ba,saboda tunda aka haifeshi bai taɓa jin anji mutuwa a gidan ba,though yana ji a islamiyyarsu ana faɗa,amma bai san yaya mutuwa take ba,yana kuka a jikinta yace "Mimi yaushe za mu mutu? Ni ina son bin lil Mysha.. I really² missed her" ɗago kanta tayi tana kallonsa zuciyarta a karye tace "Babana ba'a mutuwa sai lokacin mutum ya yi,itama Allah ya hukunta kwanakinta kenan a duniya,sai dai muyi ta mata addu'ah duk sanda muka tuna ta,kou muka ji muna kewarta,Allah yasa me cetonmu ce ranar gobe kiyama" kuka sosai yake,ƙwaƙwalwar yaro akwai saurin ɗaukan abu,bare irin Abuu Turab da kana faɗa masa yake ɗaukewa,ya gane da tace Mysha baza ta sake dawowa ba kuma baza su ƙara ganinta ba,da ƙyar tai masa wanka suka fito idanunsa sun yi jaa,a tsayin rayuwarsa yau duk sai yake jinsa wani iri,haka ya zauna yai shiru yana kallon Mimi dake shiryashi,har ta gama ta kama hannunsa tace "zo muje kayi breakfast" babu musu ya sauko ya riƙe hannunta,he's really missing his lil Sis,banda ajiyar zuciya babu abunda yake saukewa,a parlour suna fitowa Suwaiba ta taho tana kallon uwar gijiyarta tace "Mimi gashi inji Dad yace na baki" kallon takardar da take miƙo mata kawai take gabanta na wani irin bugawa,hannunta dake rawa tasa ta karɓa,a hankali tace ma Suwaiba "ki kawo masa breakfast" Suwaiba ta amsa ta tafi kitchen,duk yanda gabanta ke tsananta faɗuwa a haka ta daure ta buɗe takardar ta shiga bin content ɗin da kallo,abunda idanunta suka gani ya sake girgizata,da gaske Hamood ya saketa? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take faɗa a ranta,lokaci ɗaya ta tashi idanunta a soye ta wuce bedroom ɗinta,ƴar purse ta ɗauka sai wayarta da hijab then plat shoe,har sannan tana riƙe da takardar a hannunta ta fito,hawaye gaba ɗaya sun ƙafe a idonta,tana fitowa parlour ta samu Suwaiba tana bawa Abuu Turab abinci amma yaƙi karɓa,sai lallaɓashi take ya kauda kai ya haɗe rai kamar ba da shi take ba,bata kalli inda suke ba tace ma Suwaiba "ki ɗauko hijab ɗinki tare da shi za mu fita" Suwaiba tace "Mimi abincin fa ya ƙi ci" Hoor tace "mayar da abinci kiyi sauri,ku sameni waje" amsawa Suwaiba tayi respectfully ta wuce hanyar ɗakinta,hijab da takalmi kawai ta ɗauko tana fitowa Hoor dake tsaye waje taja ƙofar ta rufe sannan ta wuce kai tsaye suka nufi hanyar fita gidan,al'amarin dai ya bawa Suwaiba mamaki sai dai bata tambaya ba,har suka kai zauren gidan,cikin sa'a yauma babu kowa Abba Waziri ya fita yana can gidan Sarki,binta kawai Suwaiba dake riƙe da hannun Abuu Turab take a baya suna tafiya har suka kawo bakin titi,kafin su tsallaka ta tsare musu taxi tana kallonsa tace "Malam Jambulo second gate" yace "toh bismillah" bata tsaya tambayar nawa za ta bayar ba ta buɗe ta shiga Suwaiba dai mamaki kawai take ganin za su shiga motar haya,sai data fara shigar da Abuu Turab kafin itama ta shiga ta rufe,me taxi yaja suka ɗauki hanyar barin Tudun wuzirci,a hankali Hoor ta kwantar da kanta jikin kujeran tana kallon hanya,tunani iri² na zuwar mata,few minutes drive ya kawosu unguwar jambulo,dai² link ɗinsu tasa yai parking suka buɗe suka sauka,a hankali ta buɗe purse ɗinta Allah ya taimaketa akwai kuɗi ciki,Naira ɗari biyar shi ne babban kuɗi a lokacin ta ciro ta miƙa masa ya dunga kallonta kafin yace "ba ni da canji Hjy yanzun nan na fito,kuma duka tafiyar bai wuce Naira ɗari ba" Hoor ta kalli kuɗin hannunta kafin tace "karɓi kawai kaje na gode" yasa hannu biyu ya karɓa,da sauri ta juya bata tsaya jiran jin ta bakinsa ba tai cikin link ɗin,me taxi sai addu'ah yake mata yana godiya,Suwaiba taja hannun Abuu Turab suka wuce suka bi bayanta. Hoor na isa gidansu ta buɗe get ta shiga,ta windown parlour Mama ta hango shigowarta,sanda gabanta ya faɗi data ganta a irin lokacin nan,ta ƙarasa tare da knocking ƙofar parlonsu,me aiki ta taho ta buɗe mata,da sallama ta shiga Mama ta amsa sai kallonta take har ta ƙarasa gurinta a hankali ta zauna tare da sauke hijab ɗin jikinta,murya a sanyaye tace "ina kwana Mama?" Mama ta amsa mamaki duk ya cikata tace "ya gida da haƙurin rashin Mysha?" A hankali Hoor tace "alhmdllh" sai kuma duk sukai shiru,cikin sanyin jiki Mama dake jin ba daɗi tace "lafiya dai auta na ganki haka da safen nan? Kuma ku da akaiwa mutuwa ai kou dan baki bakwa fito ba tun yau" Hoor ta ɗaga kai tana kallon Suwaiba da suka shigo sai tai shiru bata ce komai ba,gaisuwar Suwaiba Mama ta amsa tana kallon Abuu Turab dake gaisheta shima ta amsa tace "zo nan *WAZEER..* Taho ka zauna kusa da ni megidana" babu musu ya tafi gurinta,Hoor dai kallonsa kawai take,saman cimyarta Mama ta ɗorashi tana kallon fuskarsa da yanda har lokacin yake sauke ajiyar zuciya tace "me akai maka kake ajiyar zuciya? Waye yasa ka kuka? Mmmm?" Kwantar da kanshi yayi a jikinta da sanyayyar maganarshi yace "Mimi ce tace baza mu sake ganin Lil Mysha ba ta mutu" Mama na shafa kanshi ta gyaɗa kanta tace "ehh ta mutu,wanda ya mutu ba ya dawowa.." Nan ta shiga yi masa bayani kamar wanda take magana da babba,Hoor sai kallonsu take ta kasa sanarwa Mama batun sakin da Hamood yai mata. Nan suka yini har dare,da Mama taga basu da niyyar tafiya,tana kallon Hoor lokacin su kaɗai ne a zaune cikin ɗakinta tace "Auta sai yaushe za ku tafi ne? Kin san dare na sake yi fa kuma gaki da yara,sannan na ga alama ba da mota kika fito ba" a hankali tana sauke wani irin numfashi kanta a ƙasa idanunta na ciccikowa da hawaye tace "Mama cewa yai na taho gida ya sakeni" salati Mama ta fara tana kallonta a tsorace tace "Auta! Me nake ji?" A hankali ta ɗago kanta tace "abunda yace kenan tun jiya da dare,i thought wasa yake sai da safe ya bawa Suwaiba divorced paper ta bani" Mama tai shiru tana ta kallonta can tace "amma kuma Auta tunda kika zo sai ki kasa sanar min? Me haka yake nufi? Me yasa za kiyi shiru? Ina takardar yake?" Purse ɗinta ta kalla tace "yana ciki" Mama ta dunga kallonta ta kasa yarda,kamar wanda aka mintsina sai kuma ta tashi ta tafi gurin data ajiye wayarta ta ɗauka,number Yaa Abuye ta lalubo da kanta ta shiga kiransa,ba'a jima ba ya ɗauka da sallama,Mama tace "Abuye kana ina?" Yace "ina gida,nazo ne kina son ganina?" Mama tace "ehh! Yi maza don Allah kazo kaji" yace "toh Mama,gani nan in sha Allah" tace "sai ka iso" tana katse kiran ta nemo number Yaa Mansoor ta kirashi,sai Yaa Umar da Hoor take bi shima,within few minutes suka iso dake dukansu gidajensu babu nisa a nan cikin Jambulo ɗin suke,Mama sai kallonsu take bayan sun gama gaisawa,Yaa Abuye yai ƙarfin hali yace "Mama lafiya? Kiran me kikai mana haka da sauri?" Mama na kallon Hoor tace "ga ta nan tai muku bayani da bakinta" Yaa Umar ya kalli Hoor da kanta ke sunkuye kamar mara gaskiya yace "Hoor! Auta!! Me yake faruwa?" Muryarta na trembling tace "babu komai" Mama tai saurin katseta tace "ban gane babu komai ba? Ƙarya kikai min ni da kika ce min Muhammad ya sakeki?" Duka su Yaa Abuye suka zubawa Mama ido,cikin ƙarfin hali Yaa Umar yace "ya saketa kuma Mama? Akan me? Laifin me kikai masa ya sakeki daga mutuwar ƴarku yau 5 days?" Mama dai kallon Hoor kawai take data ƙi magana,lokaci ɗaya ta kalli Yaa Mansoor tace "kai ɗauko min jakarcan,ana mata magana ta yima mutane shiru,ɗauko takardar ka karanta mana ai tace yana ciki" Yaa Mansoor dai ya ma kasa magana,ya tafi ya ɗauko purse ɗin ya buɗe,sai ga folded takarda a ciki ya ciro ya shiga warwarewa,content ɗin ya fara bi da ido yana karantawa a fili _"Ni Muhammad Aliyu Waziri,na saki mata ta Hooriyah Aliyu saki ɗaya,bisa sakaci a matsayinta na uwa,data kasa kula da nauyin ƴaƴanta.."_ Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai dukansu Yaa Abuye suke maimaitawa,Mama ta kama baki tace "idan na fahimceshi dai² yana nufin ita tai silar mutuwar Mysha kou?" Yaa Umar ya gyaɗa kanshi yace "haka yake nufi" Mama ta dunga jinjina zancen tana gyaɗa kanta,Yaa Abuye kam ita Hoor ɗin yake kallo ya kasa magana,sai can yai ƙarfin hali yana sauke numfashi yace "Mama ina ga gobe in Allah ya kaimu za muje mubi ba'asin zancen nan,in sha Allah everything will be fine" Mama ta gyaɗa kanta tace "toh shi kenan Allah yasa" suka amsa kafin sukai musu sallama suka tafi. Washe gari da safe kamar yanda suka tsara,kou gidan Mama basu zo ba,kasancewar weekend babu office meeting point sukai a gidan Yaa Abuye,suna haɗuwa Yaa Umar ya amshi key ɗin motar Yaa Abuye da za su tafi a ciki,Yaa Mansoor na back seat Yaa Abuye kuma a front kusa da Yaa Umar dake driving suka nufo Tudun wuzirci,dai² ƙofar gidan Waziri Yaa Umar yai parking suka sauko tare cikin shigar mutunci suka nufi babban zauren gidan da suke gano takalma a waje,da alama Abba Waziri na nan bai fita gidan Sarki ba,a wajen suka kwaɓe takalmansu suka shiga ciki da sallama,Abba na kallonsu fuskarsa ta faɗaɗa da murmushi,zaunawa sukai ƙasa suka gaisheshi ya amsa,yana ta musu sannu tare da tambayar jikin Mama suka amsa,kafin Yaa Abuye ya ɗan gyara zamansa yace "Abba wata magana ce ta kawo mu,amma bamu sani ba kou Muhammad ya sanar muku" Abba yana gyaɗa kanshi yace "toh! Mu shiga daga cikin gida kou?" Respectfully Yaa Abuye yace "toh Abba" Abba Waziri yace "ku shiga gurin Sa'adatu gani nan shigowa zan sameku yanzu" sai da suka amsa kafin suka tashi sukai cikin gidan,daga bisani bayan Abba Waziri ya sallami baƙinsa ya taso ya biyosu zuwa ɓangaren Daada,ya shigo da sallama suka amsa,suna dai zaune dukansu suna hira da Daada tana tambayar jikin Mama,zaunawa yayi saman kujera bayan sun sake gaisawa yake faɗin "Abubakar! Wane magana ne kuka zo da shi?" A hankali Yaa Abuye ya sake gyara zama yace "jiya Hoor ta je can gida,duk dai bamu sani ba sai da Mama tayi kiranmu,kou da muka je sai muka iske zancen wai Muhammad ya saketa,tou shi ne mukai shawara za muzo mu sameku da maganar,bamu sani ba kou shi ɗin ya sanar muku,idan kuma da yiwuwar zai mayar da ita ɗakinta shi kenan.. A taƙaice dai mun zo ban haƙuri ne saboda dalilin da ya rubuta wanda yasa ya saketa" nan ya ciro takardar dake wajensa ya miƙawa Abba Waziri ya karɓa,ya ciro glasses a aljihun tare da sawa a idonsa,a fili ya shiga karantawa Daada na ji ta kasa magana saboda mamaki,Abba Waziri ya dunga kallon Daada bayan ya gama karanta takardar kafin yace "ina Muhammadun yake?" Daada ta girgiza masa kai tace "toh! Ni dai tun safe da ya shigo min yace zai je unguwa ya fita,ban sake sakashi a idona ba" Abba ya sauke numfashi a hankali kafin ya laluba wayarshi dake jikinsa ya ɗauko,number Hamood ya laluba ya kirashi,bugu biyu ya ɗauka da sallama,Abba Waziri ya amsa tare da cewa "kana ina Muhammad?" Daga can ya amsa,Abba yace "maza² duk inda kake kou me kake ka bari kazo gida yanzu ina son ganinka.." Daga haka ya katse wayar,for about 30 minutes suna zaune suna jiran isowarsa,sai ga shi yai sallama ya shigo,Daada ta dunga binsa da kallo,shi kuma su Yaa Abuye yake ta kallo har ya zauna kusa da Daada,Abba Waziri na kallonsa ya miƙa masa divorced paper hannunsa yace "mene ne wannan Muhammad?" Kallon paper Hamood ya tsaya yi kamar bai gane tambayar da Abban nasa yake masa ba,sai da yai masa tsawa yace "tambayarka nake takardar mene ne wannan?" Kanshi a ƙasa yace "na saki ne" Abba na masa wani kallo yace "saki!? Wa ka saka Muhammad?" Hamood yai shiru,rufeshi da faɗa Abba yayi yace "karɓi ka karanta min abunda ka rubuta" babu musu ya karɓa sai kuma yai shiru yana ta kallon paper,Daada dai sai kallonsa kawai take taƙi cewa komai,Abba yace "Malam kada ka ɓata mana lokaci,kai muke sauraro,ai ka san abunda ke rubuce kou? Tunda kai ka rubuta da hannunka" Hamood yai shiru,Abba yace "ka karanta min nace" kamar wanda akaiwa dole ya shiga karantawa fuskarshi tamke kamar wanda aka aikowa saƙon mutuwa,Abba na saurarensa har ya gama karantowa yai shiru,cikin tarin takaici Abba yace "saboda a kanka aka fara rashi kou kuma tawakkali ne ba ka da shi Muhammad?" Yai shiru kansa a ƙasa ya kasa cewa komai,faɗa Abba ya rufeshi da shi,ta inda yake shiga ba ta nan take fita ba,sai da yai masa tatas kafin yace "umarni na baka ba shawara ba,lallai² yau ɗinnan ka mayar da matarka,saboda babu laifinta a cikin mutuwar yarinyar nan,in fact ita da take uwa mace ta rasa ƴarta kuma ta fika juriya da tawakkali,sai kai namiji za ka aikata wannan haukan? Tou bazan lamunta ba,danginmu ba'a sakin mace sai idan ta aikata wani babban laifi kou ta shigo da alfasha,yau ɗinnan na baka umarni ka mayar da ita ba tare da maganar ya fita ba" kanshi a ƙasa ya ɗago ya kalli Daada dake ta kallonsa,Abba yace "kuma ƴan uwanta ma sun yi hankali da suka zo suka sanar mana,dan ta kai baka ƙi muga anzo ana ɗiban kayanta ba kenan kou? Tunda har ka fice baka sanar da kowa ba,da na ji maganar nan,kaima ka san tun a jiyan nan babu inda Hooriyah za taje har ta kwana kou wani ya sani.. Lallai² ka mayar da ita ba na son shashancin banza" daga haka ya tashi yana kallonsu Yaa Abuye yace "Abubakar ayi haƙuri bamu san haka al'amari ya faru ba,idan kun koma gida ku bawa mahaifiyar taku haƙora on behalf of us,ita kuma Hooriyah zan aika aje a ɗaukosu in sha Allah ta dawo ɗakinta" godiya su Yaa Abuye sukaiwa Abba Waziri da addu'o'in gamawa da duniya lafiya yana amsawa da ameen² sannan ya fita ya barsu,sukaiwa Daada sallama tare da godiya kafin suka tafi.

WAZEER!Where stories live. Discover now