Wedding march

87 9 0
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*MIKIYA WRITERS ASSO..*


*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*


                     *♡WAZEER¸.•💥*
                   (A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)


Bʏ.
   *HAWWA__B__KUMO.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
••••••••••

*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*

        _Follow my account on arewabooks @Realsmasher or https://www.arewabooks.com/u/realsmasher.._


                               11

#Weeding march

                Wani matashin soja da ya ɗan sunkoyo yana kallon Mlm Mu'azu driver bayan ya sauke glass yace "assalamu alaikum" driver ya amsa yana faɗin "Oga barka da aiki" sojan da gaban rigarsa aka rubuta A.Y Jega,yana ɗan leƙa back seat da yaga alamar mutum yace "yawwa! Yallaɓai ina zuwa ne? Gurin wa kuka zo?" Mlm Mu'azu yace "Oga mun kawo yaronmu ne,daga emirate muke.. Muna neman Jega,ance idan mun zo mu nemeshi" Jega yace "ok! Bismillah ku shiga ciki,nine Jega,barka da zuwa" daga inda yake yai magana aka buɗe musu get suka shiga ciki shi kuma ya biyo su a ƙafa,babban guri ne iya ganinka dake ɗauke da ɗakunan kwana,ga Corpers nan da suka zo tun jiya,wasu kuma sun kwana biyu saboda nisan tafiyar da sukai daga jahohinsu zuwa Kano,wasu kuma yau suka iso kamar dai Wazeer,Mlm Mu'azu na yin parking,fadawa suka sauko aka buɗe masa mota,Wazeer da yai nisa a duniyar tunani ya ɗago kansa kafin ya sauko yana kallon yanda mutane ke shigowa da kaya niƙi²,kamar wanda suke shirin barin gari,ya taɓe baki a hankali tare da gyara tsaiwarsa jikin mota,fuskar nan nasa a haɗe babu alamar dake nuna ya san wani abu dariya,Jega ya iso gurin da sallama,Mlm Mu'azu na kallonsa yace "Oga yanzu mene ne abun yi na farko?" Jega na kallon yanda Wazeer yai kicin² yace "za'a kai kayan da akazo da shi Police post.. His luggage would be checked,don tabbatar da bai zo da wani abu da ba'a yarda a shigo da shi camp ba,zai rubuta sunansa a can,za'a ba shi number that is very important during the registration period.." Yana kallon Wazeer yace "take a good care my friend,lokacin da kake shigar da number do not misplace it" Mlm Mu'azu yace "toh! Lallai² sai shi yaron ne zai je,ko kuwa wani zai iya zuwa a madadinsa?" Jega yace "no! Shi zai je,amma kada ku damu i will be there,zan kula da duk abunda zai yi in sha Allah" Mlm Mu'azu yace "toh babu laifi,yanzu za mu jira a nan dai kenan har ku fito ko?" Jega yace "ehh! Ku jira ya kammala registration,bari muje kada mu ɓata lokaci a nan akwai mutane" Jega ya kalli Wazeer dake sanye da mask yace "let's go friend" Mlm Mu'azu ya kalleshi yace "Wazeer ka bishi kuje,zai wuce maka kai komai cikin sauƙi" for the first time Wazeer ya ɗaga kyawawan idanunsa ya kalli Jega,ba wani babba bane ya yi nisan duniya shekarunsa su kai 30,babu laifi yana da ɗan haske amma baza ka kirashi fari ba,cike da izza ya ɗan motsa ƙafafuwansa,kafin suka jera suna tafiya Jega na yi masa magana yana sanar da shi abubuwa masu muhimmanci da za su taimakesa a zaman da zai cikin Camp na kwanaki 21,cikin maganganunsa ya fahimci 12 tips da ya faɗa masa sosai,kuma ya naƙalcesu a ransa duk da bai fito ya nuna ya gane kalma ɗaya cikin abunda yake cewa ba,har suka isa Police post,ya rubuta sunansa tare da karɓar number ɗinsa,Jega yai musu bayanin daga inda yake,jin daga masarauta ya fito yasa ba'a ma nemi kayanshi ba sai dai an tura wanda za su yi checking,yana gamawa da nan suka je accomodation,nan yaga yanda corpers ke bin layi mata da maza babu bambanci,basu tsaya ba Jega ya wuce da shi ciki,bayan ya rubuta suna tare da nuna temporary number da aka bashi a Police post,akai directing ɗinsa ɗakin da zai karɓi katifa,Jega na kallonsa da murmushi a fuskarsa yace "u shouldn't expect comfort a nan kamar dai kana gida,za kaga abubuwa da yawa da baka saba da su ba" Wazeer ya ɗan karkata kansa ya kalleshi,bai dai ce komai ba amma underneath yana tunani da tambayar kansa "me yasa haka?" Sanda suka shiga ɗakin da katifun suke Jega yace "bismillah" kallon mattress ɗin ya dunga yi,a fili ya furta "what's this?" Jega ya fashe da wata dariya yace "don't worry My G,i'm sure they are up to 20 yrs old..They are just an inch thick" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa,Jega ya wuce ya ɗan bincika ya samo masa wata da tafi sauran kumari,shi dai yana tsaye ya kasa motsi,kallon ikon Allah kawai yake yana tunanin yanda zai iya kwanciya akan wannan abun da marbarsa da kwanciya a ƙasa kaɗan ne,ya ga alama katifun gurin za su iya yin shekarun da Jega ya faɗa,shi ya ɗaukar masa suka fita zuwa ɗakin da zai zauna har zuwa sanda zai gama 3 weeks ɗinsa,daga nan suka je yayii registration,it tooks him half of an hour gaba ɗaya,suka je last phase wato kit collection and platoon registration,ya karɓi kayan NYSC ɗinsa,a nan ma Jega yake sanar masa,idan ya duba sun yi masa yawa ko kaɗan zai iya samun wani suyi canji,if kuma he's lucky zai iya samun komai yai masa,luckily takalmi dai yai masa dai² size ɗinsa ya samu,amma kayan kallo ɗaya yai musu ya san baza su shiga jikinsa ba,bai dai ce komai ba saboda Dad yasa an masa wasu,kayan da suke cikin kit ɗin Khaki ne na NYSC,wando da jaket+belts,farar t-shirts 2,farin guntun wando 2 da safa guda 2,sai rigar NYSC,sai wasu ƙananan littattafai kamar Camp schedule,the NYSC anthem,dokoki da ka'idoji (rules and regulations),etc. Bayan ya gama duk wasu abubuwa masu muhimmanci,da taimakon Jega har kayansa duka ya kai ɗaki,after then su Mlm Mu'azu sukai masa sallama suka juya gida,kasancewar shi ne first person da ya fara shiga ɗakin,yasa basu dawo ba suka dunga zagaye cikin camp yana nuna masa gurare yana kuma yi masa bayani "this camp ground is where the 3 weeks NYSC Orientation Course takes place.. It involves physical drills,lectures and training,and social activities intended to foster interactions among Corpers.." Yana sake nuna masa can wani guri daga nesa da sak bai da maraba da kasuwa yace "there is the large market operated by the locals popularly called Mami Market,a nan all camp needs are sold including food and drinks.." Wazeer ya gyaɗa kanshi,yana ci gaba da sauraron surutun da Jega ke masa,sai da suka gama zagayawa sannan Jega yace "idan kana buƙatar wani abu kuma da bamu da shi a nan sai ka neme ni" Wazeer ya sake gyaɗa masa kai,Jega ya bashi wayarshi yace "can we be friends?" Wazeer ya ɗan gyara tsaiwarsa sai kuma ya buɗe ido ya gyaɗa masa kai,za ka rantse ba ya magana,ko kuma dai ya fito cikin halittun reptile ne,musamman ƙadangare saboda ƙaunarsa da son gyaɗa kai,ba komai yasa ya amince zai yi abota da Jega ba sai saboda kirkin da yayi masa,da kuma amfanin da zai masa nan gaba a zaman da zai yi,sukai exchanging digits sannan suka rabu Wazeer ya wuce ɗakinsu,yana shiga babu jimawa wani sabon corper ya shigo,a hankali ya kalleshi yai masa sallama,ganin ya samu abokin zama kasancewar da shi kaɗai ne a ɗakin,guy ɗin duka bazai wuce sa'an sa ba ko shi ya ɗan girmeshi,fuskarsa ma'abociyar fara'a a sake yai masa murmushi yace "i'm Abdul-Waheed Ja'afar,from Kaduna State" Wazeer ya ɗan gyaɗa kansa yace "Aliyu.. Nice meeting u Waheed" Waheed yai murmushi yana buɗe idonsa yace "ohh! Kamar ka san sunan da ake kirana a gida?" Wazeer ya gyaɗa kansa,ba tare da ya sake cewa komai ba ya zauna gefen bunk ɗinsa yana ɗauko ledar gurin Mimi na jiya,kallo ɗaya Waheed ya yiwa Wazeer ya fahimci bai da yawan magana kuma bai son a cikashi da surutu,a hankali yace "friend bari na gama shigo da kayana" ba tare da Wazeer ya ɗago ba yace "ok" daga haka Waheed ya fita ɗakin yai remaining shi kaɗai,here ya fito da all abubuwan dake cikin ledar,bedsheets ne masu kyau har guda biyu masu kyau da tsada,kowanne haɗe yake da duvet sai fine net,ya dunga kallon kayan yana jin zuciyarsa na shiga farin ciki,no one told him ya tafi da wani abu bedsheet da duvet,Dad kuma bai tambayeshi yaji ko yaje ya yi siyayyar da yace masa ba,kawai ya tura masa kuɗi shi kenan,ya ɗauki ɗaya daga ciki ya ajiye gefensa sannan ya mayar da other one cikin ledar,tashi yayi ya shimfiɗa bedsheet ɗin ya saka net,idan ba wai bai ji da kyau ba,a bayanin da Jega yayi masa ya sanar masa akwai sauro a garin,shi kuma bai shiryawa yaita fama da kansa ba,yana ƙoƙarin gyara duvet ɗin wani envelope ya faɗo daga ciki,sunkuyawa yayi ya ɗauka ya zauna a nutse ya shiga buɗewa,kuɗi ne ciki masu dama sababbi a miƙe cikin wrapper ɗinsu ƴan 1K,sai short note da Mimi ta haɗa a ciki,ya dunga juya kuɗin a hannunsa yana tunanin me yasa Mimi tasa masa kuɗi,bayan ta san bazai buƙacesu ba? Note ɗin data rubuta yabi da idanunsa _"i know everything about rayuwar camp Son,ba lallai ne Dad ya tsaya yai maka shirin da uwa mace za tai maka ba,na san za kace babu abunda za kayi da kuɗi,saboda mahaifinka ya wadata rayuwarka da komai,amma za ka buƙaci cash wani lokacin,shi yasa nai deciding saka maka ɗan abunda bai fi ƙarfina ba.. Take a good care of urself for me Son,sannan ka tsare kanka da bin al'adun da suka saɓawa addinin Musulunci.. I love u.."_ Wani sanyi yaji har ransa,yanzu ya fahimci dalilin Mimii na yi masa all abubuwan da tai masa,underneath ya furta "thank uuu Mom,i will always love and proud of u" daga haka ya ajiye kuɗin ya gama gyara kayansa,sannan ya ɗan kwanta saboda ya huta kafin lokacin sallah. Yana kwance yana kallon empty bunks,Waheed ya shigo da sallama ya amsa masa,tas yai parking kayansa kusa da na Wazeer,shi dai bai sake ce masa komai ba,har ya ɗora mattress ɗinsa up bunk ya gama gyarawa babu me cewa wani komai,suna nan su biyu kowa na kwance gadonsa mutane suka fara shigowa da kayansu yare daban²,kafin wani lokaci ɗakin ya cika da hayaniyar sababbin corpers,a hankali Wazeer ya kulle idanunsa saboda yanda surutunsu yake hawa masa kai,jijiyoyin kansa banda harbawa babu abunda suke,bai taɓa tsintar kansa a noisy guri irin nan ba,duk shi bai san wannan ƙaddara na bautar ƙasa ba,banda a Nigeria ko africa zai ce nema,shi dai bai san ana yin wani abu service ba,guraren zhuhur ana fara kiran sallah Waheed dake bunk ɗin sama ya leƙo yana kallon kamilalliyar fuskarsa yace "Aliyu!" He thought bacci yake shi yasa ya ɗan kirashi yanda zai ji,Wazeer ya buɗe idonsa da sukai mugun ja saboda masifaffen ciwon kai,Waheed ya sauko yana cewa "za ka fita masallaci ne?" Wazeer ya tashi ba tare da ya ce komai ba,slippers kawai yasa sai wayarsa da ya ɗauka suka jera tare suka fita zuwa masallaci,a can gurin alwala suka haɗu da Jega,bayan sun idar sun yi sallah,suna fitowa Jega yace "za ku iya cin abincin nan ko za'a nemo muku wani abun?" Wazeer ya ɗan kalli Waheed alamar yai magana,murmushi Waheed yayi yace "babu matsala Oga,za mu duba Mami market idan akwai abunda muke buƙata" Jega yace "ok! But don't call me Oga again,za ka iya kirana Jega as u can see it here" ya nuna jikin rigarsa,Waheed yace "ok! Thanks" za su tafi Wazeer ya ɗan tsaya yace "a ina zan samu medication na ciwon kai?" Jega yace "kanka na ciwo ne?" Wazeer da bai son magana yace "gurin nan is too noisy,i don't think zan iya zama har 3 weeks" Jega yai murmushi yace "don't worry My G,idan ka kwana biyu za ka saba,yanzu bari na samo maka maganin" Wazeer ya kalleshi kawai,sai dai bai ce komai ba,ba ya tunanin ko kwana 💯 zai yi zai saba,tunda ya taso tsayin shekarun da yayi a duniya,bai taɓa samun kansa a guri makamancin wannan ba,suna komawa ɗaki Waheed ya ciro musu babban pray mat ya shimfiɗa area ɗinsu sannan ya shiga fito musu da lafiyayyen abincin da ya taho da shi daga gida,kallo ɗaya za kai masa ka san ba daga gidan talakawa yake ba,yana kallon Wazeer dake matsa forehead ɗinsa yace "get down friend,mu ci abinci sai na duba maka drugs,i think na taho da medication saboda uzurin gaggawa" Wazeer ya ɗan buɗe idonsa ya kalleshi,Waheed yai masa murmushi kawai,yanda yake bai da surutu da hayaniya yasa Wazeer yaji zai iya zama da shi,sannan ko babu komai neighbor ɗinsa ne,a addinance ya san hakkin maƙotaka,shi yasa ya kasa ignoring ɗinsa,suna zaune Jega ya shigo da maganin a hannunsa,Wazeer ya karɓa yai masa godiya saboda yanda yake taimakonsa babu gajiyawa,zai tafi Waheed ya tsayar da shi su ci abinci,abunka da wanda ya jima rabonsa da abincin gida,haka ya zauna suka ci tare su 3,Wazeer ya ɗauko musu containers da Mimi tai masa chops da drinks,har da wani dambun naman da tai masa,suna gamawa Jega yace su huta kafin yamma yayi za su fita ground,sannan yai musu sallama ya tafi. Ana asar suka shirya suka fita,bayan an musu lectures da sauran duk abubuwan da Jega ya sanar masa da safe,ba su suka dawo ba sai guraren maghreeba,wanka da alwala kawai suka sake yi suka tafi sukai sallah,daga can basu dawo ba suja tsaya tare da Jega,Waheed da shi kawai suke hirarsu,suka duba abunda za su iya ci Wazeer ya biya,daga can kuma suka tafi sallar ishaa,sai a hanyarsu ta komawa ɗaki sannan ya samu ya kira Mimi da su Abba suka gaisa,ya sanar musu ya isa lafiya,duka sai tambayarsa suke baƙunta da kaɗaici,shi dai bai ce musu komai ba har sukai sallama ya kashe wayarsa.

WAZEER!जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें