03

7.8K 609 10
                                    

Murmushi Imam yayi yana kad'a kai don mamanshi ta iya girki. Kallonta yayi yace
"Kin mini shiru baki ce komai ba".
"Umm.. Cous cous ne da Kwai sai dankalin turawa da ya kusa k'arewa".
"Idan na fita ki mini text d'insu harda abubuwan da kuke buk'ata ke da yara, in kuma kud'in kike so in baki kije kasuwa ki saya to".
Ta girgiza kai a hankali tace
"A'a ka siyo d'in dai, ni ba sai naje ba".
Bai k'ara magana ba yayi hanyar fita daga cikin gidan, a sanyaye tace
"Mun gode"
"Uhm" kawai yace kana ya fice.

Kallon yaran nata tayi tace
"Kar in sake ganin kunje zaku rungumeshi tunda baya so".
Nanah da ta koshi da abincin ta kwaso duwatsu tana 'yar carar rami tace
"Ai ni dama bana zuwa, Laila ce wawuya har yanzu bata gane cewa Abba baya son a ta6ashi ba".
Laila na jin haka ta taso suka fara dambe akan me zata kirata wawuya, Adama daga inda take zaune take musu magana wai su bar fad'a, amma ina kamar cewa take su k'ara.
Anwar ne ya shigo lokacin da take cewa
"Ku kuka sani, ku cinye kanku in ku mayu ne". Sosai ranshi ya 6aci da kalamanta, suna ganin shi kuwa suka rabu don kansu, sunyi cirko-cirko kamar zakaru yace
"Knell down"
Da sauri kowacce ta zube, kana ya kalli Laila uwar kuka wacce har ta fara sana'ar tata yace
"Me ya hadaki fad'a da yayarki?
Cikin kukan ta fara fad'a mishi, ya daka mata tsawa akan tayi shiru, tsit tayi yace
"Me ya had'a ku? Nanah tace
"Wai don fa mama tace kar su sake zuwa rungumeka tunda baka so, kawai sai nace ai su Laila ne wawaye masu zuwa, shine ta hayayyak'o kaina, ni kuma na casata".
D'iff d'an sauran annurin fuskarsa ta d'auke, kallon Adama yayi wacce take kiciniyar cirewa Yusuf pampers kan ta d'auke shi suka shige d'akinta don ganin har yayi kashi. Sai data k'ule ya dawo da dubansa kan yaran. Shikam ya zaiyi da ita ne???
Sarai tasan bai karya ba amma ko tayin abinci bata mishi ba shida gidansa, d'an addu'a da ake yiwa miji bata mishi, ga qazanta dake cinta ciki da waje, To yanzu kuma so take ta rabashi da 'yayansa, wai shin meyasa ta kasa fahimtan dalilinsa na hanasu ta6ashi muddin jikinsu da dauda?
Ganin hawan jini kan iya kamashi yasa ya shige falonsa dama key din mota ya manta. Bayan ya d'auko ya wuce yaran ba tare da ya kalli inda suke ba. Nana ce tace
"Abba mu tashi ne?.
Bai juyo ba yace
"Ku tashi kuyi wanka, kuma idan na k'ara jin kunyi fada sai na zane ku".

Bayan ya shiga office ne ya gwada wayan Nazifa don ya lura har ya fita bai ga alamar ta fito ba, sai dai har ya tsinke ba'a d'aga ba, ya gwada a karo na biyu nan ma shiru.
A hankali yake scrolling calls d'insa har yazo kan contact din SA'ADATU murmushi yayi kafin ya danna call.
Sallama ta fara cikin sassanyar muryan ta mai
dad'in sauraro, kana tace
"How are u cherry?"
"Lafiya lau, kefa Baby?" Tace
"I am good...".
Hira sukayi na tsawon minti 15 kana sukayi sallama.

Bayan ya tashi daga aiki karfe 6 ya wuce gidansu, a masallacin kofar gidan sukayi sallah tareda mahaifinsa suka shigo gida suna magana a kan harkokin kasuwancinsa.
A falon baban nashi suka yada zango daga bisani Umma (mahifiyarshi) ta shigo da babban tray mai d'auke da Kwanukan abinci, sallama tayi suka amsa mata tace
"Anwar kana nan ne?"
"Ehh umma, anan nayi sallah. Ina wuni?"
Suka gaisa ta ajiye abincin kan dinning ta kalli Alhaji Muh'd tace
"Yanzu zaka ci ko sai kayi sallan isha?"
Da casbaha a hannunsa yana ja yace
"Kawo muci yanzu".
A tsakiyar falon ta ajiye musu kana ta koma d'auko musu ruwa da drinks. Fareeda ne ta kawo ta gaishe da yayan nata kana ta fita.
Bayan fitan ta Alhaji ya dubi Anwar yace
"Fada min abunda ke ranka".
Da murmushi a fuskarsa yake mamakin yanda baban nashi yake karantar fuskarsa. Yace
"Dama Baba wata yarinya ce na gani nake son a nema mini aurenta"
"Aure kuma Anwar?" Baba ya tambayeshi da mamaki a fuskarsa.
Anwar ya sunkuyar da kansa k'asa yana fargaban kar baban nashi yak'i na'am da buk'atarsa.
Ganin shirun yayi yawa yasa ya d'ago kanshi, murmushine shimfide a fuskar dattijon yace
"Baka bani amsa ba"
Anwar ya sosa qeya yace
"Ehh insha Allah baba"
"A ina take?"
Anan Anwar ya fad'awa Baba komai dangane da Sa'adatu inda ya k'arishe maganan da cewa
"Tana da hankali da nitsuwa kuma tanada ilimin addini daidai gwargwado".
Shiru baba yayi can yace
"Kamar dai yanda ka bani labarin kun dad'e da fara nema wanda hakan a musulunci ba abune mai kyau ba, kusan shekara kenan ko?"
Anwar ya gyada kai, baba yacigaba..
"Yau saturday, ka sanar da iyayenta rana ita yau magabatanka zasu je nema maka aurenta insha Allah, kuma auren za'a had'a da na Farida nan da watanni biyu masu zuwa kenan in iyayenta sun shirya".
Sosai Anwar yayi farin ciki da jin haka, har gani yake ma watanni biyu sun mishi yawa don yanda yake ji a jikinsa kamar wannan ne aurensa na fari.
A haka suka cigaba da hira har aka Kiran sallah isha  suka tashi suka nufi masallaci, bayan sun dawo ne suka ci abincin kana ya yiwa iyayen nashi sallama ya tafi. Bayan tafiyanshi Baba yake shaidawa Umma k'arin aure da d'anta zaiyi wanda taji dad'i a ranta, ba don komai ba sai don sanin halin matan nasa da tayi.
Addu'a suka masa Allah yasa yayi a sa'a ya kuma bada zaman lafiya.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now