33

6.2K 742 31
                                    


"Ban tara ku a nan dan neman rigima ko fad'a ba, Girma da arziki ya taramu da kuma taya murna ga 'yar uwarku abokiyar zamanku."
Yana kallon yadda Nazifa ta sauke wani wulakantaccen kallo a kan Sa'adatu, sai dai nishadin da zuciyarsa ke ciki bai bashi damar maida kai gareta ba, ya ci gaba.
"Adama ke ce babba, dan haka ki kula da girma da mutuncinki, kamar yadda kika gani, Sa'adatu kanwa ce gareki, na kuma tabbata zata baki duk wani girma da ya kamata ta bawa na gaba da ita. Haka kema Nazifa."
Ya maida dubansa gareta,
"Mutuncinki ya fi komai daraja a gareki, so ki kula da shi, ku zauna lafiya da juna, domin ban tara ku dan ku rinka tayar mun da hankali ba gaba d'ayanku. Ban k'i ace kun zama tsintsiya mad'aurinki d'aya ba, ban k'i ace zan shigo in sameku kuna wasa da dariya tamkar yan uwan juna ba. Da wannan nake cewa ku zauna da juna lafiya matsawar kuna son ganin farin cikina."
Adama na ganin yadda yake bayani yana satar kallon matar da yake kira da Amaryarsa, anya zata iya jure wannan takaicin kuwa?
Da sauri ta kauda kai, jin zafafan hawayen da suka taru suna barazanar sauka samar kuncinta.
Shirun da yaji duk sunyi ya sanyashi kai duba ga Amaryarsa, ya murmusa,
"Gare ki Sa'adatu, ga 'yan uwanki nan abokan zamanki, ki rike su da girma da arziki ku zauna lafiya, duk da ina ji a jikina ba za ki bada matsala ta wannan 6angaren ba."
Tabbas Adama ta ji zafin kalamanshi, amma ya zata yi? Dole ta saukar da kanta k'asa tana mai wasa da yatsun hannunta.
"In sha Allah zan kula da duk abinda zai haifar da farin ciki gareka, zan kuma rike su tamkar yan uwan da muka fito gida daya."
Yadda take furucin cikin nitsuwa sosai ya tafiyar da imanin Anwar, idanunsa ya daidaita yana dubanta, yana jin sabon nishad'i na kara ratsa zuciya da gangar jikinsa.
'Ya ma za ayi ace kada yayi alfahari da wannan halittar da ke zaune gabanshi? Matar da ta iya tsara kalamai, a lokaci guda kuma kallonta kawai, kan iya tafiyar da duhun da matanshi suka jefa zuciyarsa.'
A kasar zuciyarsa yake wannan tunanin, daga bisani ya saki murmushi mai kyawu,
"Akwai mai wani abun cewa ne?"
Babu wacce ya samu kallon arziki daga gareta, idan aka d'auke hararar da Nazifa ta aika masa, sai kuwa Sa'adatu da idanunta ke k'asa tana kare ma zanen carpet din da ke malale a k'asa kallo.
Hakan ne ya sanya shi gyara zama,
"Sai maganar kwana, Adama ya kike ganin ya dace mu tsara tunda kece babba a cikinsu."
Shiru ta yi na sakwanni tana k'ok'arin daidaita nitsuwarta don kar su fahimci halin da take ciki.
Sai da ya k'ara maimaita tambayarsa sannan ta bud'I bakinta da ya bushe tace,
"Duk yanda suka yanke yayi dai-dai."
Sanin cewa baza ta fad'a ba yasa ya dubi Nazifa ya tambayeta.
"Kwana d'ad'd'aya." Ta bashi amsa a tak'aice tana dokawa Sa'adatu harara da ta kalleta.
"Ke fa Sa'adatu?"
"Tunda Aunty Nazifa ta yi magana a barshi a hakan." Ta fad'a a sanyaye cike da ladabi cikin kalamanta.
Murmushi yayi ya dubi Adama wacce tamkar bata falon, dalilin ko numfashin kirki bata yi.
"Kin ji yanda K'annen naki suka yanke, shin ko ya miki?"
"Yayi." Tace dashi tana d'aga kai.
Hamdala yayi cikin zuciyarsa don dama shima hakan yaso a tsara, kwana biyu kenan zai na sadashi da muradinsa wato Sa'adatu.
"Next week rana ita yau, ke Adama zaki k'arbi girki..."
Bai k'arishe magananshi ba Nazifa ta Antayo ashar ta zuba, ta dafa hannun kujeran da take kai ta fara masifa.
"Ban gane niswik ba (nextweek)! Kana nufin har wata zaka yi a dakinta ko me? Yanzu Anwar daga shigowanta ka fara nuna mana banbanci? Wallahi muddin aka danne mini hakkina Allah ya isa."
Murmushi kawai yayi yana kallonta, sai da ta k'are jan Allah ya isanta yace,
"Tunda baki yi boko ba kamata yayi da kin ji sabuwar kalma sai ki tambayi me yake nufi kafin ki fara hauka. Next week nace, ina nufin wata sati."
"Kamar ya wata sati? Ai budurwa ake yiwa sati ba bazawara ba." Ta fad'a tana yiwa Sa'adatu kallon banza.
Ranshi ne ya sosu da ta alak'anta Amaryarsa da bazawara, sai dai bai nuna ba. Ya kalli Adama wacce yanzu fuskarta fayau, ba alamar 6acin rai tattare da ita yace,
"Zaku ita tafiya."
Kamar dama jira take yi ta tashi da sauri ta nufi k'ofa.
"Adama, nace ko zaki had'amu a cikin breakfast d'inki na gobe?" Ta tsinkayi muryan Anwar a dodon kunnenta.
Wani mololon bak'in cikine ya turnuk'eta yazo mata har wuya ya tsaya anan. Hawaye ne ya sauk'o mata tayi k'arfin halin cewa To, kana ta fita daga falon.
Dariyan takaici Nazifa ta yi, tana gwada ina ma ita aka cewa tayi karyawan dasu! Wallahi sai dai yunwa ya kashesu amma baza ta yi ba.
Anwar ya tashi yana kallon Nazifa da take zauna kamar an dasata a gurin, bata da niyyan tafiya.
"Ke fa? Baza ki tafi bane?"
"Dama ina son magana da kai."
"A yau d'in?" Ya tambayeta yana d'aga Sa'adatu daga zaune.
"Ehh mana." Nazifa ta bashi amsa cikin tsiwa.
Hannunshi ya zagaye a kunkumin Sa'adatu suka fara tafiya yana cewa,
"Ki jirani. Idan Allah yayi na fito sai mu yi maganan ko?." Bai ko waigowa ya haura sama da Amaryasa yayin da Nazifa ke kiransa tana maganganu marasa dad'i.
Tafi minti 30 zaune a gurin tana hawaye, kamar ta haura sama ta buga musu, sai dai tana shakka don tasan tun d'azu darajar Sa'adatun take ci kamar yanda Anwar ya fad'a. A yanzu kam in ta kaurara haukarta zata ci na jaki ne daga gunsa.
Jiki a sa6ule ta baro side d'in ta yi nata gurin, tana tunanin ko me Anwar yanzu yake yi da Sa'adatu. Ohoo..

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now