23

5.3K 388 2
                                    


"In tafi ne Yaya?" Ta tambayeshi ganin bai k'ara cewa komai ba tsawon mintuna biyu da suka wuce.
"Gobe zaki je bikin ne?" Shima ya tambayeta cikin sanyin murya kamar bashi ya mata fad'a d'azu ba.
"Ehh, zanje gobe."
"K'arfe nawa?"
"Yaya wani abu ne?" Ta tambayeshi cike da mamakin tambayoyinsa.
"Ki bani amsa mana."
"11:00am bayan an d'aura aure."
"Ki shirya zan zo in d'aukeki. Fice min a mota."
Tana gani ya cilla kan titi bayan ta fice masa daga motar, ta6e baki tayi ranta bai so ya kai ta gobe ba. Ko dai ta fasa zuwan ne?

Washe gari haka ya zo ya d'auketa kamar yanda ya fad'a. Da za'a kai Amarya ya hanata shiga kowanne mota na 'yan kai Amarya, dolenta ta hak'ura ta shiga tashi ita da Hajar da ta mak'ale mata tun zuwanta.
Bayan sun isa gidan Amarya ne yace Adama ta shige cikin gidan zai yi magana da Hajar. A sanyaye ta bar gurin tana ganin wannan raini ne, ita ko Hajar murna kamar ta taka kan jariri, sai washe hak'ora take kamar sokuwa.
Tambayarta yayi dalilin da yasa take shige mishi, ita ko ba sanya ta bayyana masa sirrin zuciyarta wanda tunda ta fara magana yake ganin wautarta a fili. Duniya tazo k'arshe, 'yar k'aramar yarinya da ita wai shi zata tsayar ta kalleshi cikin ido tace tana sonshi?
A nitse ya fad'a mata ta daina shige mishi, din shi baya sonta kuma baya son raini. Sannan yace mata yana da matar da zai aura.
"Don Allah Yayan Adama wallahi ina sonk....."
"Ki rik'e sauran mutuncinki da k'imarki ta mace." Ya fad'a cikin ruwan sanyi yana k'okarin shiga mota.
Yana barin gurin ta shige gidan da gudu tana hawaye. Ana tambayarta lafiya tace bata jin dad'I ne zata koma gida, jakarta ta kar6a ta musu sallama kan anjima in taji sauk'I zata dawo.
Adama kuwa dad'I kasheta don ta tabbata Anwar ya yarfata ne, amma haka ta danne murnanta ta yiwa Hajar in sannu da jiki, yayinda Hajar d'in ta danna mata harara ta fice. Har aka gama bikin bata dawo ba.
Anwar kuwa haka yaci gaba da dakon soyayyar Adama. Sannu-sannu itama ta fara jinshi a ranta dalilin ya daina hantararta, kuma itama tana iya bakin k'ok'arinta ganin bata yi masa laifi ba. A haka shak'uwa tsaftatacciya ta shiga tsakaninsu inda Iyayensu suka zuba musu ido suna jiran har sai d'ayansu ya kawo maganar gurin manya.
Duk da irin sauyawan halayenshi game da Adama bai furta mata so ba wanda shi kanshi ya rasa dalilin meyasa.
Ganin har kusan wata biyu da sasantawarsu amma babu labari yasa Babanshi ya kirashi ya tambayeshi shin ko ya sami matar aure? Yace Adama yake so. A ranar 'yan uwa biyun sunyi murna kwarai da gaske inda suka tsayar da biki wata hudu masu zuwa.
Adama bata tashi jin labari ba sai bayan kwana uku da zancen. Sosai ta kad'u ta kuma tsorita. Kwata-kwata bata ta6a tsammanin abu makamancin haka zai faru ba. Tasan dai a yanzu bata k'in Anwar kuma bata sonshi soyayya na aure. Soyayyar da take tunanin take mishi na 'yan uwantaka ne. Ina ita ina Anwar? Wani irin rayuwar aure zata yi da mutumin da ko mafarkin hakan bata ta6a yi ba? Anya Iyayenta sun mata adalci da basu tambayi ra'ayinta ba? Sai dai bata nuna musu bata so ba ganin yanda suke ta saka mata albarka farinciki fal a fuskarsu, tabbas zata iya jure zama da yayanta muddin zata dinga ganin iyayenta cikin farinciki. Kuma bayan mugunta da son girma irin na yayanta ita kanta shaida ce bashi da wani mummunan hali, ko da bata samu irin mijin da take so ba zata hak'ura da Yayanta.

Shi ko Anwar ta wani 6angare bai ji dad'in shigar sauri da Iyayensu suka musu ba, yaso a ce ya furtawa Admy kalmar so kafin taji maganar aurensu. Yasan dole taji abun banbarakwai, namiji da suna Hajara. Gidan Ango Musa yayi niyyar zuwa neman shawara don ya tabbatarwa kansa sani Admy zata k'ullaceshi duk da bata nunawa Iyayensu cewa babu batun soyayya tsakaninsu ba.

Gidan Musa da ke nan cikin Bauchin Anwar ya sauk'a, a bakin kof'ar gidan ya ajiye babur d'inshi yayi locking d'inta.
Wayarshi ya ciro ya kira Musa yace gashi a k'ofar gida. Minti d'aya Musa ya fito suka shiga gidan Anwar yana bashi labarin abunda ya faru.
"Moses meke damunka ne na ganka sukuku haka? Ina Surayya Amarya?" Anwar ya fad'a yana kallon abokin nashi da yayi tagumi ya zuba mishi ido.
"Tana bacci. Mu ci abinci sai muyi maganar a natse." Musa ya bashi amsa kana ya fita zuwa kitchen ya d'auko musu abinci da drinks.
"Ni a koshe nake, kai dai ka gama sai muyi maganar."
"Baza kaci girkina ba? Ko ka manta irin yanda kake rok'ona na girka mana Indomie a Uni?"
Da mamaki Anwar ya dubeshi yace,
"Surayya bata da lafiya ne ka girka abincin da kanka?"
"Lafiyarta kalau. Kaci abinci kai kam."
Haka Musa yaci abincinsa don Anwar cewa yayi ya k'oshi. Kofar gidan suka fita Musa ya fito musu da carpet suka zauna a k'arkashin bishiyar Nim.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now