10

6.2K 480 5
                                    


  Shiru yayi yana kallonta, don shikam da farko yanda ta sukwano ta bashi tsoro, ya zata hannu zata sakar masa, kawai dakewa yayi yana jiran abunda zai faru ya koya mata hankali.
  "Mtsw, sake min k'afa". Ya fad'a yana k'ok'arin kwatar k'afanshi da ta rik'e gamgam kamar me neman gafara.
K'in sakewa tayi tana shar6an kuka tana mishi magiya.
  Sunfi minti 12 a haka tak'i barinshi. Ganin ba kyaleshi zatayi ba kuma ya gaji da addabar da yake masa yasa yace
  "Ok.. ok naji, zanyi tunani akai".
  Aiko da sauri ta sakeshi tana washe hak'ora kamar wanda yace ya fasa.
  "Don Allah Baban Nana ka fasa, wallahi matan k'abilan nan babu abunda suka iya sai asiri da makirci. Munafukai ne na kan gaba wajen tarwatsa aure wallahi".Ta goge hawayenta da d'ankwalinta wanda ya cire tun d'azu. Kana taci gaba
  "Yanzu ka duba Musa, fisabilillahi ya zama tamkar rak'umi da akala. Ka duba yanda shegiya matsiyaciyar nan Karimatu yanda take juyashi kamar waina. Ni bana son ka zama mijin tace don haka ka rufawa kanka asiri ka bar waccar Sa'adan. Kaji Baban Nana?"
  Shikam tsayawa yayi kawai yana kallonta yana tabbatar da maganan mutane da suke cewa 'mace kan iya komai akan kishi'. Yaushe rabon da Nazifa ta lallasheshi ko ta kirashi Baban Nana? Wai shi zata yiwa wayo, tana fad'a mishi illar matan kudu? Wai me ta dauk'eshi ne? Yaro ko Jahili?
  Murmushi kawai yayi irin kina fooling kanki d'innan.
  "Naji, kya Iya tafiya d'akinki don ni bacci nake ji".
Da sauri tace
  "A'a, yau anan zan kwana sweety".
  "Bana buk'ata, ki tafi room d'inki".
  Sosai ya ja mata ajii amma ina ta kafe lallai yau a d'akinshi zata kwana tunda girkinta ne.
  "Ka bani minti 10, yanzu zan dawo".
Kai ya gyad'a mata don yana mamakin saurin canjawanta. Tabbas yayi missing d'inta, kusan watansu 6 rabon da su had'a makwanci. Ya rasa dalilinta na haka, ya mata magiya ya gama jarabarsa amma bata bashi hak'k'inshi.
  Tana isa d'akinta ta watsa wanka, wani drawer ta bud'e ta d'auko wani garin magani wanda ta yarda dashi tun da. Kad'a shi tayi da madara. Lokaci d'aya ta kafa kai ta shanye tass a tsaye harda gyatsa.
  Humra ta shafa a jikinta tabi da musk ta lailaye kana ta zura rigar baccinta ta doshi sashen Maigida Takobi. Buhun k'aya ba'a cikaka a danna.

Wanka ta samu yakeyi don haka ta zauna a bakin gado tana jirashinshi. A hankali take bin room din da kallo wanda da alama baya samun kulawa kamar da.
  Bata ji fitowanshi ba sai ganinshi tayi tsaye a bakin mirrow yana goge kanshi da k'aramin towel.
  A hankali ta isa gurinshi ta kar6i towel d'in tana goge masa kan da sauran jikinshi. Bayan ta gama ta jawo mishi chair din mirrow ta mai alamar ya zauna, zama yayi kana ta d'auko lotion ta fara shafa mishi. Salon yanda take shafe jikinshi yayi matukar sanyashi kasala gami da jin buk'ata.
  "Wani kaya zaka saka?"
  Muryanta ya dawo dashi daga tunanin da yake.
  "Just kiyi baccinki, zan d'auka da kaina".
  "Wai har yanzu jan ajin bai k'are bane?". Ta fada yayinda ta zauna kan cinyarshi suna fuskantar juna.
Kawar da kanshi yayi gefe yana cije le6e. Wani shu'umin murmushi tayi kana ta juyo da fuskarsa da hannayenta lokaci d'aya ta fara bashi hot kiss.

50mins later

Anwar ya sau'ko daga kan gado ya nufi toilet yana wasi wasin abunda yake zato game da Nazifa.
  Ita kuma tana can kan gado ta lullu6a da lallausan bargo tana baccin wahala da gajiya. Gefen fuskarta ga hawaye daya bushe.
Koda ya fito ko ta kanta bai bi ba ya kwanta had'e da kashe bedside lamp.
Yaja tsaki yafi sha biyar kafin yayi addu'ar bacci, ya jawo bargo had'e da sa pillow tsakaninshi da Nazifa, a cewarshi bata yi wankan janaba ba.

Washe gari Adama ta fito don yin karyawa da mamakinta taga Nazifa na juye soyayyan dankali a food flask d'in Anwar, sai banko mata harara take yi tana taunar chewing gum kas kas kas.
  Babu wacce ta yi magana wa y'ar uwarta kowacce ta kama aikin gabanta, Nazifa na gama aikinta ta bar Adama wacce ta d'aura d'umamen tuwo.
  A dinning table Nazifa ta ajiyewa Anwar abincin kana ta shiga bedroom d'inshi ta tashe shi ya shiga wanka.  Room d'inta ta koma ta shige wanka itama tana fatan magiyarta na jiya yayi aiki a kan Anwar.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now