11

6.1K 495 8
                                    


Cikin shirinta ta isa side d'in Anwar. A falo ta sameshi zaune yana waya lokaci d'aya kuma yana danne danne a laptop d'inshi.
"Eehh, na tura masa yanzu. Kaje ka karbo kayan akai site, Nura ka lura kar a samu matsala."
Yana gama fad'an haka ya kashe wayan ya dubeta fuskarsa ba yabo ba fallasa. Da wani yanga ta isa gurinshi ta kamo hannunshi.
"Ina kwana Baban Nana?"
"Lafiya." Ya bata amsa a tak'aice.
"Kazo muci abinci."
Zama sukayi a kan dinning tayi serving nashi dankali da kwai d'in data soya.
"Ya baki yanka onion akai ba?" Ya tambayeta bayan ya caki d'aya da fork ya kai baki.
"Wallahi mantawa nayi ganin na makara. Tea zaka sha ko Quarker Oats?"
"Had'a min Lipton kawai ki saka mini lemon tsami don dankalin yasha mai."
"Yanzu hakan yasha mai?" Ta tambayeshi lokacin da take zuba nata a plate.
Har ta gama cin nata ta had'a mishi Lipton din bai k'arisa nashi ba. Sai danne-danne kawai yake da wayarshi yana sipping tea din, wani lokacin kuma su had'a ido da Nazifa tana washe mishi hakwara.
"Na k'oshi." Anwar ya fad'a bayan ya mik'e tsaye.
"Baka cinye ba."
"Bana son over feeding da safe."
"Shikenan. Ammm... ya maganarmu?" Nazifa ta fad'a tana kifta idanu cike da fargaban amsan da zai bata.
"Na me fa?"
"Maganar mu na jiya mana Baban Nana, ka tuna?"
"Idan bazaki fad'a min ba zan tafi, don banida lokacin tunawa."
Kyarr ta mishi da ido kamar mai nemo kalmomin da zata yi amfani dasu.
Ganin bata da niyyan magana yasa ya zuge zip na jakar laptop nashi ya kwashi phones d'insa yace,
"Na tafi. Na ajiye miki kud'i a bedroom. Ko akwai wani abu da kike buk'ata?"
"Babu nikam. Dama kan maganar aurenka ne kace zaka yi tunani."
Tsura mata ido yayi yana murmushi yayinda yake ganin wautarta a fili.
"Ka fasa ko?"
"A'a, ban fasa ba. Don bakin alk'alami ya riga da ya bushe. Ba yanda za'ayi anje anyi tambaya har an saka rana nazo nace na fasa. Haba Nazy, ai sai a d'auki iyayena k'ananan mutane. Its impossible. Kiyi hakuri Kinji?"
Tun da taji kalmarsa ta farko ta durk'ushe a gurin tana kuka. Yanzu shikenan dole sai anyi auren nan? Tayi rashin kunyan tayi lalla6in amma duk a banza? Yanzu ya zata yi??
Sosai ta bashi tausayi da kuma dariya amma ya gimtse, ya ajiye Abun hannunsa ya d'agota suka zauna a kujera.
"Nazifa ki saurareni da kyau."
"Ni babu abunda zaka fad'a min Anwar, cuta ce ka riga da mini."
Tashi tayi zata tafi ya rik'o hannunta ya zaunar da ita kan cinyarshi yace,
"Look at me. Nazifa." Ya juyo da fuskarta, ta danna masa harara.
"Ba fa rabuwa nace zanyi dake ba Nazifa. Aure kawai zan k'ara kamar yadda kema na auroki after Adama. Kar ki manta ni mijin mace hud'u ne, Aure kuma Sunnah ce ta Annabi Muhammad SAW. Abunda kike tunani game da Sa'adatu ba haka yake ba, idan kika zauna da ita zaki san cewa ita mutumiyar kirki ce kuma bata da mugun nufi akanku iyalina. In ma Karimatu na da mugun hali ba shi zai sa itama a jefeta da irin halin ba, so Halin karimatu daban, na Sa'adatu ma daban. Kina jina?"
Shiru tayi tana hawaye yayinda tunda ya fara magana take k'ok'arin barin cinyarshi yana rik'ota ya k'i barinta ta tafi.
"K'addara ta riga fata, kisa a ranki wannan aure yana daga cikin k'addarata wacce tun kafin inzo duniya an rubuta zanyi. Wannan rashin kunya da kike min kuma bai dace ba, keda zaki lalla6ani, iyee, ki riritani in amaryar ma tazo ki nuna mata cewa har yanzu kece fa ta gaban goshi Nazy na, amma sai kika biyewa zugin k'awaye. Haba Nazifa, ba haka ma sanki ba fa. Ina 'yar tu6ul tu6ul d'ina?"
Daga ita harshi dariya suka saka. Tana tuno auren kuma ta k'ara shan murr.
Ya jawota jikinshi tare da kwantar da ita kan kirjinshi yana share mata hawaye yace,
"Ki kwantar da hankalinki matata. Babu wata halitta da zata rabamu ko ta rage son da nake miki. Bana son inga kina damuwa akan abu d'an kad'an."
  Tana son masa tsiya amma kalamansa sun d'an shigeta, don haka ta rufe bakinta bata ce komai ba, ba kuma don ta rasa abun fad'a ba. Kallonta yake yi wanda Seconds kad'an idanunshi suka fara canja launi yana lumshesu. Ai kuwa tana ganin haka ta karanceshi tayi wuff ta mik'e tsaye ba tare da wahala ba don ya sassauta rik'on da ya mata sakamakon kasalan dake shigarshi a hankali.
"Zaka yi latti fa Baban Nana." Ta 6ata fuska taci gaba..
"... cikina na murd'awa wallahi. Washhh."
Shima mik'ewan yayi fuskarshi da d'an nuna damuwa duk da yasan k'arya take yi.
"Sorry, kije kisha magani ki kwanta. Kinji?"
Gyad'a mishi kai tayi tana cije le6e.
Sai daya kaita d'akinta ya kawo mata magani tace atafau ita bazata sha ba. Bai tilasta mata ba ya tafi bayan ta kwanta.
    Palourn Adama ya shiga ta gaishe shi, Ya amsa tace,
"Baban Nana ina son zuwa gidanmu da yara wuni in zan samu."
"Ki bari sai next week saturday. Gobe monday suna da makaranta tashin safe zai muku wuya. Kinji?"
"Naji."
"Ba komai ko?"
"Umm." Ta fad'a kan ta shige d'akinta a ranta tana jin haushin hanata zuwa da yayi, sai kace shine mai shirya mata yaran ko mai tashinsu. Tukunna ma ina ruwanshi??

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now