17

6.1K 439 3
                                    


TUNA BAYA....

Alh. Muh'd da Alh. Umar Bankud'I 'yan uwan juna ne uwa d'aya uba d'aya. Su kad'ai iyayensu suka haifa Baban Anwar ne babba. Sunyi karatun Arabi da Boko har matakin degree, Alh. Muh'd yaci gaba da karatunshi ta fannin Islamic Studies har ya kai matakin Professor, shi kuma Alh. Umar ya kama siyasa gadan-gadan, a harkarsa ta siyasa duk kujerar da ya nema Allah na taimakonshi ya samu, saboda ya rik'e gaskiya kuma talakawa na sonshi.
Akwai wani lokaci da Alh. Umar ya kaiwa Yayan nashi ziyara yake ce mishi,
"Yaya, tunani nayi wanda in hakan ya faru ba k'aramin fad'ad'a zuriyarmu zata yi ba."
"Wani tunani kenan d'an uwana?"
"Me zai hana mu had'a Adama aure da d'aya daga cikin 'yayanka maza wanda tasu tazo d'aya."
"Nima na jima da wannan tunanin kuma naji dad'I da ka kawota a yanzu. Kaga Saifullahi ya girmeta sosai tunda yanzu har matsa mishi nake yi kan ya fito da matar aure, kaima shaida ne, mutum ya gama karatun har aiki ya samu me yake jira?"
Tsaki Baba ya ja don burinshi a yanzu bai wuce ace Saifullahi yayi aure ba. Ya nisa ya cigaba da magana.
"Anwar ne zaiyi dai-dai da ita kaga yanzu tana SS 1, shi kuma ya kusa gama Jami'a. Ko ya ka gani?"
"Hakan yayi dai-dai. Sai dai jiya Saifullahi ya je mini da magana ya samu matar Aure nace sai nayi bincike. Yanzu kam shima zai huta da gorinka."
Dariya suka saka Baba yana hamdala. Anan suka tsayar da maganan cewa zasu had'a Anwar da Adama Aure. Sai dai basu bayyanawa kowa ba sai matansu.

Adama itace 'ya ta fari gun iyayenta sai k'annenta biyar, Muh'd, Samira, Jamila, Suraj sai autansu Al-Ameen.
Tayi makarantan primary har O'level d'inta, anan Babanta ya katse mata karatun kan cewa sai tayi aure in mijinta ya yarda sai ta tafi Uni, ga dai result ta samu amma haka ta hakura ta zauna tana fatan Allah Ya za6a mata mafi Alkhairi. Amma tasan da wuya tayi aure a wannan lokacin saboda bata kula samari, kuma ko da an aiko cewa ana kiranta a waje bata fita kuma cikin iyayenta babu mai tilasta mata kan ta fitan. Ita a tunaninta Mazaje na gari sun k'are, irin mijin da take fatan samu har yau bata ji irin labarinsa ba balle yazo hanyarta.
Sukan had'u jefi-jefi da Anwar wanda ko numfashi mai k'arfi bata yi a gabansa saboda baya mata da dad'I, duk cikin danginsu yafi saka mata ido sa6anin sauran 'yan uwanta da yake wasa dasu, sai dai su d'in ma suna kofsa masa zasu gane kurensu. Ita kuma a duk lokacin da suka hadu sai ya sata kuka saboda sunaye da ya rad'a mata, Lukuta, 'Yar Fari Wauta, ko Mai Idon Agogo. Duk cikin sunayen nan babu wanda yake mata dad'I sai ma ya sata 6ata mata rai. Shiyasa a duk lokacin da tasan yana gida bata zuwa gidansu, in kuma gidansu yazo bata fita har ya gama hiranshi da Mamanta ya tafi.
Bayan gama skul d'inta da 3months, Adama ce tsaye sanye da riga da siket na atamfa wanda yayi bala'in yiwa dogon kuma duma-duman jikinta kyau, bata yi wani kwalliya mai yawa ba illa kwallin da ta sakawa manya kuma fararen idanunta da suka k'ara haska doguwar fuskarta mai d'auke da dogon hanci. Daurin d'ankwali tayi irin karkatacce na gefen nan wanda ya bawa k'ananan kitson kalaba da aka mata damar zubowa gefe da gefe da kuma a kafad'unta. Gabanta k'annenta ne biyu yara k'anana da baza su wuce 4 to 5yrs ba suna knelling gaba d'aya sun had'a gumi suna rok'anta ta barsu su tafi sun gaji.
"Jamila ki d'aga hannunki da kyau, kai kuma Suraj ka rufe idonka. Yau sai nayi maganinku. Dani kuke wasa." Tace dasu da d'an mitsitsin bakinta kamar na yara.
Farar kujeran roba ta jawo ta zauna rik'e da bulalan Nim a hannunta tana nuna su dashi cikin warning in sun bud'e ido.
A haka Anwar ya bud'e gate ya shigo da babur d'inshi ya samesu. Harara yake danna mata tun kafin yayi parking tana ganinshi kuwa ta cewa yaran su tashi su shiga gida wanda k'aran bud'e gate yasa suka bud'e ido ganin ko wayene.
Da gudu suka isa gurinshi suna mishi oyoyo sai warin zufa da wahala ke tashi a jikinsu. Alawa ya ciro ya basu suka kar6a suna godiya yace su shige gida a musu wanka. Adama dake tsaye tana mazari dalilin tsayar da ita da yayi da hannu ta gaisheshi.
"Ke sokuwa ce da zaki saka k'ananan yaran nan knelling cikin rana ba ko tausayi? Tukun ma me suka miki?"
"Wanka za'a musu shine suke ta guduwa sunk'I suje a musu, kuma wallahi don sunga Umma bata nan ne."
"Yanzu saboda wankan ne zaki saka su knelling? Oya kema kiyi irin nasu. Now."
Hakuri ta fara bashi yace atafau sai ta yi. Dolenta tayi tana matsar kwallah.
"Your hands up and close that clock-like eyes."
"Don Allah Yaya Anw...."
"Do as I said."
Kunce d'anwalinta tayi ta warware ta yafashi a kanta kana ta rufe hammatanta don d'inkin Stella ne a jikinta.
Shi abun ma dariya ya bashi to mai zai gani a hammata. D'auko Newspaper yayi a jikin Babur d'inshi ya jawo plastic chair ya zauna yana karatunshi. Sa'I-sa'I yana lek'enta ta saman jaridar wanda ya rasa gane dalilin yin hakan.
Idonta a rufe amma hakan bai hanata zubar hawaye ba tana jin tsanarshi cikin zuciyarta. Ohh ashe haka yaran suke ji game da ita?
"Ki sauk'e hannayenki." Ta tsinkayi muryanshi na bata umarni.
Shi kuwa bai ma san lokacin da bakinshi ya furta hakan ba, a tunananinshi zuciyarsa ce ta fara magana.
Sauk'ewa tayi a hankali tana yarfesu saboda tsamin da suka fara suna mata ciwo. Share hawayenta tayi ta sukuyar da kanta k'asa tana murza 'yan yatsunta.
"Look at me 'yar lukuta."
Cinno baki tayi sama ta bud'e idon tana kallonsa wanda yake aika mata da murmushi.
"Wato kinfi k'arfin ki bani hakuri ko?"
"To ba tun d'azu na fara baka hakurin ka tsayar dani ba."
"To daga nan kin k'ara attempting ne?"
Shiru tayi tana kallon gefe ranta a 6ace.
"Ok, hands up and close your eyes again."
Kuka ta fashe dashi tana cewa,
"Kayi hakuri don Allah. Kayi hakuri ka barni in tafi. Na baka hakurin don Allah"
Tausayinta yaji ya tsirgeshi lokaci d'aya da wani abu daya kasa tantance ko menene. Gaba d'aya sai ya fara jin haushin kanshi a karo na farko da irin kukan da yake sakata duk ranar da suka had'u.
"Ki tashi ki tafi." Ya fada a sanyaye kamar ya bata hakuri amma jin kanshi bazai barshi ba, yana ganin girmanshi zai fad'I.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now