45: Sayayya

6.8K 951 42
                                    


Wayar hannunta ne ya fara ringing ta kalli gefen da Jamila take, kana ta kara wayar a kunnenta bakinta k'unshe da sallama. Bai amsa ba yace,
"Kina ina Rayuwata?"
D'an murmushi mai sanyin sauti ta yi tace,
"Muna cikin gari."
"Ki fad'a min in da kuke, yanzu gani nan zuwa."
"Ga Jamila zata gwada maka in da muka nufa."
Nan ta bawa Jamila wayar ta ta fad'a mishi gurin da zai samesu. Har suka isa *Kwaiseh Boutique* Anwar na waya da Adama yana jaddada mata kyawun da ta yi.
Basu fi minti biyar da shiga ba Anwar ya iso, tun daga nesa kallon Adama yake yana d'aga mata gira, fuskarsa gwanar kyau kuwa, cike take da annuri.
Isarsa gurin da suka zauna yasa hannu ya mik'ar da ita tsaye yana juyata. Adama kunya kamar ya kasheta, sai nonnok'ewa ta ke yi. Jamila da ke gefe ta fara musu video tana cewa,
"Wannan har IG zai je."
Janta yayi gefe, ya matso da fuskarsa dai-dai nata, hancinsu na gogar na juna yayin da hannayensa ke mak'ale a k'ugunta. Cikin rad'a ya fara cewa,
"Kamar in maidaki ciki haka nake ji, ina kishin mazan da suka kallemin ke a hanya. Kin k'ara birkitani Hayateey, kin yi kyau, you look perfect. Wai shin me sirrin?"
Shiru ta yi don gaba d'aya a takure take, ji take kamar idanun mutanen duniya kaff yana kansu ne. Sannan kalamansa na tsumata. Tana son nuna mishi farincikinta, ta mishi iso cikin sabuwar duniyar da ta samu kanta a ciki, amma wannan kunya da take damunta shi ke hanata rawan gaban hantsi.
Jin takun mutum a gefensu yasa ta yi saurin jan jikinta daga gareshi tana kallon gurin, shi kuma, ita ya kafawa ido yana kallo kamar za'a sace mishi ita da zarar ya kawar da kanshi.
"Mr nd Mrs Bankud'i muna muku barka da zuwa. Sunana Kwaiseh Maryama owner na wannan gurin." Ta fad'a tana aika musu murmushi.
Adama ta amsa itama d'auke da fara'a a fuskarta. Tace,
"Yauwa, mun gode."
Anwar ya k'ara da,
"Sannunki"
Jamila ya hango bayan matar tana danne-danne a waya, ya kirata tazo,
"Me kuka zo yi anan?"
"Dama Adda ne tace zata canja wardrobe, shine na rakota."
Juyowa yayi gefenshi ya kalli Adama wacce ke kallon Jamila, matsowa kusa da ita yayi, yace,
"Da ni kika nema in miki rakiya, nasan kayan da suka fi dacewa da ke Hayateey, ni nasan kayan da zasu zauna a jikin kyakkyawar halittarki."
Kad'a ido tayi, ta juyo da dubanta gareshi cikin yanayin da bata ma san tayi shi ba, a gun Anwar ganin hakan yayi matsayin 'ka tara yawunka'.
"Haka ne?" Ya ji ta fad'a da sanyin murya.
Gyaran murya Jamila tayi, tana kallon Adama irin 'kiyi shiru' d'in nan. Da hakan Adama ta yi shiru, tana kallon matar da ta gabatar da kanta a matsayin Kwaiseh tana magana da masu tayata aiki.
Anwar ya kama hannun Adama suka nufi wani sashe na kayan mata zalla bisa jagorancin Kwaiseh Maryama. Kujerun da suke gurin aka nuna musu suka zauna, bai bari ta zauna nesa dashi ba, ya jawota kusa dashi. Anan aka fara kawo musu kaya kala-kala kama daga English wears, Arabian wears da Atamfa masu tsananin kyau da tsada. Kowanne ya d'auka sai ya auna a ranshi irin kyawun da zai mata, Jamila ma ba'a barta a baya ba, tana tayashi za6e.
"Abban laila, ina da laces da Atampa a gida wanda ba'a d'inka ba, ina ganin kar a d'auki wasu." Cewar Adama yayin da Anwar ke ajiye wani lace a gefenshi.
"Ok, amma dai idan naga wani wanda ya mini kyau zan d'auka." Ya bata amsa yana kallon kwayar idonta.
K'asa ta yi da nata idanun tana motsa lips d'inta. Mayar da hankalinshi yayi kan abunda ya ke yi.
Shopping d'in da aka yi a ranar Naira ta yi kuka da idonta, sai da aka gama aka yi lissafin kud'i Jamila ta fara zare ido, ware kayan aka yi a gefe, aka tattara sauran na gabansu zuwa muhallinsu, anan Anwar ya dubi Jamila yace,
"Jeki d'auki abunda kike so."
Tana jin haka ta kutsa ciki har da 'yar tsallenta.
"Ina gurin under wears da Night gowns?" Anwar ya tambayi Kwaiseh.
"Yalla6ai bari a kawosu ku za6a." Ta bashi amsa cike da jindad'in yau shagonta ya yi manyan bak'i.
Nan aka shiga gabatar musu yana d'aukan kalan da yake so, gurin za6en Night gowns, ba Adama ba har Kwaiseh mai shagon sai da ya basu kunya, zagewa yayi yana d'aukan shara-shara, wanda rariya ta fisu sutura yana mannawa jikin Adama, idan ya masa kyau sai yayi murmushi a ajiye a gefe. Nan ma sai da aka 6ata wani lokacin sannan aka gama.
"Kuna da kayan kwalliya-kwalliya haka? Irin wanda suke gyara fuskarsu dashi kamar wannan." Ya fad'a yana nuna fuskar Adama.
"Anan bamu dashi, amma ga shago na gaba akwai in da zaku sami duk abunda kuke buk'ata." Kwaiseh ta amsa mishi.
Bayan an gama lissafin kud'in kayan duka tare da na Jamila, Anwar ya biya, nan masu aikin gurin suka kwashi kayayyakin zuwa motarsu. Anan Kwaiseh ta musu jagora zuwa *Miss Hafsy Cosmetics*
A bakin k'ofar shiga shagon ta musu sallama tana cewa,
"Oga, Madam, sai mun k'ara ganinku. Thank you" Ta koma shagonta.
Shigansu ke da wuya, mamallakiyar gurin ta taso da fara'arta ta tar6esu suka gaisa.
Wannan karon Jamila ne ta yi magana tace,
"Aunty Cici, kayan kwalliya za'a had'a mata kit guda. Komai da komai ake buk'ata, sannan ki duba wani cream da soap zai fi dacewa da kalar fatarta?"
Anan Anwar ya dubi Adama da ke k'arewa shagon kallo yace,
"Naji ana kiran sallar Asr, zan fita in yi, kafin nan kun gama za6en sai mu wuce gida. Ga card sai ki biya in kun gama. Kin ga yanda na yi d'azu ba?"
Mik'a hannu ta yi ta kar6a tace,
"Ehh, na gani. Sai ka dawo." A hankali ta k'ara da "Nagode"
Murmusawa yayi kana ya sa kai ya fita, bin bayanshi da kallo tana yaba tsarin halittarsa ta jarumta da takunshi cikin nitsuwa da izza.
Jawota cikin shagon Jamila ta yi, da taimakon Miss Hafsy aka za6i kayan kwalliya kalar fatar Adama.
"Jamila ina zan kai uban kayan shafe-shafen nan?" Ta fad'i haka a lokacin da ake lissafin kud'insu. Bayan sun biya suka fito Jamila na cewa,
"Ai ba k'aramin dad'i naji ba da Ya Anwar yazo aka yi shopping d'innan dashi. May be da mu kad'ai ne tuni mun gama, har mun tsufa a gida."
Bata kula ta ba suka isa mota ta ajiye kit d'in a baya kana suka tsaya jiran Anwar.
Tafe suka hangoshi yana waya, hannunshi d'aya rik'e da wani package k'arami, yana gama wayar ya bud'e motarshi ya saka tare da rufe marfin. Hangosu yayi a in da suke tsaye, ya iso yana cewa,
"Sa'adatu ta gaisheki, sannan yara na tambayanki."
Murmushi Adama ta yi tace,
"Ina amsawa, fatan dai yaran basu dameta ba?"
Hannayenshi ya saka a aljihun wandonshi, ya d'an d'aga kai sama kafin ya sauk'e kan Adama yace,
"In kin koma ki tambayeta. Amma bana jin zasu takurata."
Kad'a kai Adama ta yi cikin yarda da kalamansa. Bata tunanin Sa'adatu na da matsala tunda ita da kanta tana jansu d'akinta.
"Ya Anwar, dama kai muke jira zamu koma gida." Inji Jamila.
"Da waye zaki koma?" Ya tambayeta yana d'an had'e fuska.
"Dama gidanki zaki koma ne Adda?" Ta mayar da tambayan ga Adama.
"Kamar mun yi da kai sai da daddare zaka zo mu tafi. Ko dai ka canja mind d'inka ne?" Ta tambayeshi tana tsoron kar ya hanata komawa gidansu. Fuskarta ta marairaice tana kifta masa ido alamar tausayi.
"Naji, shikenan. Zan zo da dare na d'aukeki." Ya fad'a daga k'arshe. Juyawa yayi zuwa motarshi ya jingina a jiki yana kallonta, tamkar kar ya rabu da ita yake ji.
Dariya Jamila ta yi tana k'okarin bud'e motar tace,
"Soyayya manya."
Hararanta Adama ta yi, ta shiga motar itama tana jin kewar mijinta. Bata k'i ace su koma gida ba, sai dai tasan ko sun koma yanzu Sa'adatu ce zata tar6eshi. Ta gabanshi suka zo suka wuce suka harba Titi. Daga nan basu wuce ko'ina ba sai gida.
A gajiye suka zube a falon Umma, Jamila ta kwala kiran mai aiki ta kawo musu ruwa da abinci.
"Ke nifa sai nayi sallah kafin in ci abinci." Adama ta fad'a tana mik'ewa. Dai dai nan Umma ta shigo rik'e da yusuf yana lasan Ice Cream.
"Canjin d'iya aka mini?" Cewar Umma tana ajiye Yusuf kan kujera da shima Mamanshi yake kallo.
A kunyace Adama ta fara tafiya zata bar falon, Umma ta tsayar da ita tana yaba gyaran da jikinta ya samu.
"Don Allah a ci gaba da irin hakan, zuciyata zata ji dad'i."
"Umma, nima dai yanzu zan dinga gyaran."
"To Allah yasa, ya kuma sa a d'ore."
Adama ta amsa da Ameen. Da haka ta wuce d'akin Jamila ta barta anan falo tana bawa Umma labarin fitarsu, tana yi tana cin abinci don yunwar da ta kwaso.

Adama na idar da sallah Jamila ta shigo d'auke da Yusuf a hannunta, mik'a hannunshi yayi gurinta alamar ta k'ar6eshi.
"Sai yanzu ka tuna dani Yusuf? Baka san nayi kewarka ba ko? Zo nan Babyna." Ta fad'a lokacin da take ajiyeshi kan cinyarta.
Tura kanshi yake a k'irjinta alamar yana neman Nono, salati tayi ta kwalawa Jamila kira da ke toilet tana alwala.
"D'aukeshi ki kai wa Umma, ya tuno da nono. D'aukeshi don Allah tun kafin ya fara min kuka."
Da kyar Jamila ta kwaceshi a hannun Adama, ta mik'ashi gurin Umma yana kuka yana zillo.
Bayan Adama taci abinci Jamila ta jawo make up kit d'in, ta ciro abubuwan da ke ciki tana gwadawa Adama sunansu da amfaninsu.
"Ni fa abubuwan nan sun yi yawa a fuska d'aya, haba!" Adama ta fad'a.
Da kyarr ta lalla6ata da kalamai sannan ta maida hankali aka fara nuna mata amfaninsu da aikinsu a fuska.
An gwada kwalliya sau biyar kafin Adama ta fara koyan zana gira da shafa Foundation. Sune basu tashi a gurin ba sai magrib, gaba d'aya Adama ta gaji tana son hutawa. Suna sallah Umma ta aika kiranta, kafin ta je Anwar ya kirata, yana fad'a mata zai zo bayan Isha su tafi.

Please Don't forget to vote. Hakan kad'ai zai sa in san kuna jindad'in Matar K'abila. Thank you.😍

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now