19

5.5K 419 2
                                    


Shiru tayi, Anwar ya matso daff da ita ya mata rumfa da tsayinshi. Jikinta ne ya fara kakkarwa tana jiran inda zata ji sauk'an duka,
"Don Allah kayi hakuri." Tayi saurin fad'a kanta a k'asa idanunta taff da kwalla.
"Baki bani amsa ba." Yace da ita yana hard'e hannayensa a k'irji.
"Abincin gidane." Ta bashi amsa tana matsawa nesa dashi.
Fita yayi daga kitchen d'in yana murmushi don yana jin dad'in yanda take tsoronshi.
Kujerar tsugunno ya samu ya zauna yana fuskantar kitchen d'in ta yanda zai na monitoring kowanne movements d'inta.
Adama gaba d'aya ta kasa sakewa saboda duk lokacin da ta kalli inda yake sai sun had'a ido, a haka ta kammala abincin a cikin 10mins dama ta kusa gamawa ta kashe gas.
Shi kuwa yana nan zaune bai ce da ita uffan ba sa'I-sa'I yana latsa wayarsa Nokia Guduma mai Camera wacce ake yayi a wannan lokacin.
Bayan ta gama kwashewa ne ta rasa yanda zata yi ta masa tayin abincin, kar ta masa tayi ya disgata; kar kuma tak'I yi ta jawowa kanta laifi.
"Yaya a kawo abinci ne." Tace dashi cikin sanyin murya.
Lumshe ido yayi kana ya bud'e ya cigaba da danne-dannensa kamar bai ji abunda tace ba.
"Yaya a kawo maka abincin ne?" Wannan karon ta fad'a ranta a d'an 6ace sanin sarai ya ji maganarta ta farko.
"Me kuka dafa?"
"Tuwon shinkafa miyar ku6ewa d'anye."
"Saka mini loma uku in gani ko zan iya cin jagwalgwalenki." Ya fad'I haka alhali nan k'amshin girkin kad'ai ya tayar masa da yunwa.
A plate ta sako ta kawo gabansa ta ajiye.
"Haka ake serving abinci a garinku? Babu stool d'in ajiye plate, babu spoon, babu ruwan wanke hannu? And ohh God, babu ruwan sha."
Ya fad'a yana kallon fuskarta wacce take cike da mamakin k'arfin hali irin na bawan Allah nan.
"Kin mini shiru kina kallona da k'attin idanunki masu saka mutum mafarkin tsoro."
"Uhm Yaya kenan, yanzu dai na kawo maka abincin wanda ko gama mik'ewa banyi ba, kuma dai baka ga naje na zauna ban kawo maka duk abunda kake son ba." Tana fad'in haka ta bar gurin don ba k'aramin d'anyen kai tayi ba wajen fad'a masa wad'annan kalmomi.
Shi kuwa kallon mamaki ya bita dashi yana tunanin wani irin kalan rainashi zata yi muddin ya kuskura ya furta mata kalmar so!.
Cigaba da latsa wayar yayi wanda hankalinshi baya ma kanta, gaba d'aya tunaninshi ya tafi ta yanda zai 6ullowa Adama da maganar soyayya ba tare da girmanshi ya fad'I ba. (Da k'okarinka Anwar).
Haka ta kawo masa komai ta jera kamar yanda ya buk'ata tayi hanyar tafiya falo.
" 'Yar Fari ina zaki je?"
"Palour." Ta bashi amsa a tak'ace.
"Ki dawo ki zauna a nan. Idan na tashi buk'atan wani abu fa?"
"Yaya sai ka kwala min kira, ai anan palour zan zauna."
"Ban iya magana da k'arfi ba, Oya zauna anan ki jirani."
"Idan dai zamu rabu lafiya ai shikenan." Ta fad'a k'asa-k'asa tana jawo plastic chair.
"Ni kike zagi?".
Zaro idanu tayi kwal waje tana kyaftasu,
"Yaya ni? Yaushe na zageka? Wallahi ban zageka ba."
"Gunguni ba zagi bane? Wato don kinga yau tunda nazo ban saki kuka ba yasa kika fara rainani. Barin gama cin abincin zaki gane ba'a sabo dani."
Spoon ya d'auka yana hararanta ya yanko loma ya kai bakinshi, d'an zaro ido yayi yana kad'a kai don baiyi zaton zaiji girkin haka ba, 100% yayi masa dad'I. Wata lomar ya yanko yana gyara daidaituwar miyan.
"G10 za'a baki in har competition akeyi, don gaskiya ko F9 aka baki an miki mutunci."
Tana shiru abunta don kar ta bud'e baki ta k'arawa kanta laifi, sai dai tasan wannan zance yake yi don babu wani mahaluk'in da ya ta6a cin girkinta ya kushe sai ma yabo ko kyauta da yake biyo baya, musamman Abokan Babanta.
Bata yi ko da tari ba har ya gama cin abincin yace ta k'ara masa, ta k'ara masa tana mamakin yanda yake cin abincin G10, yana cikin kwasar girki Ummanta ta shigo.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now