07

6.5K 482 5
                                    

Nazifa ta jinjina kai tana auna maganganunsu duka. Duk so da k'aunar da ka nunawa d'a namiji watarana sai ya cusa maka bakin ciki ta hanyoyi da dama, amma anya maganar Hindy gaskiya ce kuwa cewa "da tsohuwar zuma ake magani? Zuwanta gidan Anwar ta dusashe tauraruwar Adama duk dama cewa dama ba haskawan take ba. To itama anya hakan bazai faru gareta ba ganin gwanda Adama sau dubu akanta? Duk k'azantar Adama akwai abun mora a tattare da ita, amma Ita fa? Da ita da fanko basu da banbanci. Tasan tabbas Anwar ya k'ara aure za'a daina labarinta, don ko a yanzu Adama ta fita daraja a idonshi balle kuma gaba ai sai kora. Ya ma zama dole ta tashi ta nemi mafita.
Nannauyan ajiyan zuciya ta sauk'e tana mai duban su Rocky da suma zuba mata na mujiyan sukayi,
"Don Allah ya zanyi? Gurinku fa nazo ku bani shawara amma kun tsare ni da ido. Kuna k'ara tsoritani wallahi". Ta k'arishe maganan tana d'aura hannayenta biyu kan k'uncinta.
"Ki d'aga mishi hankali kawai, bala'in yau daban na gobe daban har sai ya hakura da auren, kuma kiyi barazanar kashe amaryan a ranar da aka kawota, may be ya tsorita ya fasa auren". Inji Hindy.
Rocky kuma tace;
"Ina uwar gidanki? Ko ince akuyarki, don marabansu kad'an ne".
"Tana gida, amma ni gani nakeyi kamar murna ma takeyi da auren, wallahi ko a jikinta. Mijinki zai k'ara aure don tsabar rashin sanin ciwon kai ko uffan ta kasa furtawa in banda sunkuyar da Kai na munfurcin da takeyi.
"Ko baki ji shawaran da na baki bane? Cewar Hindy tana kallon Nazifa.
"Hindy, ko giyar wake nasha bazan fara wannan ba don wallahi Anwar zai aikata korani gida, da zarar ya lura zan d'aga mishi hankali zai iya rabuwa dani, nifa yanzu lalla6awa nake yi a gidan don banida power. Kuma ni tsoronshi ma nake ji, kar watarana ya narka min dukan da zan kasa tashi. Ya daina yayina ai yanzu"
Hawaye ne suka gangaro mata tasa hannu ta share tana tsinewa ranar da ta had'u da rugujewar farin cikinta da walwalarta.
Sosai ta basu tausayi musamman Rocky. Shiru suka yi suna tunanin hanyar da zai sa Anwar fasa aure. Nan ma basu san wacece zai aura ba.
"Kunyi shiru". Nazifa ta fad'a tana yarfe hannu.
Rocky tace;
"Ki had'a kai da uwargidan ku masa bore, idan ke d'aya ce zai iya koranki, amma in kun had'u ku biyu kuka masa zafi dole yasan yanda zai yi".
Haka dai suka yita bata shawarwari ko ince hudubar shaid'an har kusan azahar sannan ta koma gida. Ta samu Laraba ta share mata d'aki harda goge-goge.
Wayarta ta d'auka da niyyan yin kira taji babu kud'I. Drawer da take ajiye 'yan canjunanta ta bud'e ta zaro 2k, amma tana mamakin saurin k'arewansu don bata cika wasa da kud'I yanzu ba. Bata kawo tunanin komai a ranta ba ta fita ta bawa maigadi ya siyo mata kati.
Bayan ta loda ne ta danna calling d'in aminiyarta Zee, bugu d'aya ta d'auka ta fara zuba mata kirari;
"Kaji manyan mata Amaryar Anwar Bankudi. Ki shige gaba mu biki a baya sarauniyar jarumin jarumai, 6auna mai tafiyar k'asaita....."
"Sannu Zee" Nazifa ta dakatar da ita don ganin abun nata ba mai k'arewa bane.
Bayan sun gaisa ne Zee ke cewa
"Yanzu kam kin 6arar dani Nazifa, gaba d'aya kin canja min sai kace ba dake muka taso mukayi yawon d'akin samari ba. 'Dan sinadaran da nake miki oda ma kin daina siya kwana biyu, ko dai kin canja dealer ne?"
Ta6e baki tayi kamar Zee d'in na gabanta tace
"Ni duk ba wannan ba Zee, magana nake so muyi yanzu".
"Tooo, ki bani minti 5 don yanzu ina tare da kostoma ne. Zan miki filashin in mun gama".
Kashe wayar tayi tana duban screen d'in wayar, hotonta ne da Anwar lokacin sunje umrah k'asa mai tsarki. Tana matuk'ar son pic d'in don a wancan lokacin ji take yi babu abunda zai sa Anwar d'inta ya gujeta ko ya juya mata baya.
Ta fashe da kuka tana girgiza kai.
Wayarta ce ta fara ringing, sai da ta bari ya tsinke ta share hawayen fuskarta kana tayi calling back.
"Ina jinki" cewar zee bayan ta zauna kan katifar dake yashe a d'akinta.
"Zee, Anwar d'ina zai k'ara aure kwanan nan wallahi".
"Kutumesu babban b*** uba. Anwar d'in? Shi d'in banza. Kina zaune ke kuma sokuwa? Tukunna ma ya aka yi kika bari har hakan ta faru? Ai dama nasan za'a rina, tunda kika gujeni kika daina huld'a da maganina dole kuwa mijinki ya k'ara aure. Ke kinsan daga ina nake oda kuwa? Har China da India ina da kostomomi. Jar uba".

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now