30

7.2K 590 45
                                    


Tana cikin kukan Anwar ya shigo fuska ba yabo ba fallasa. Isa bakin gadon yayi yana kallonta sai a lokacin yaji tausayinta a ranshi.
"To ki bar kukan mana haka ya isa."
K'in kulashi tayi tana mai cigaba da kukanta. Sai da ya d'au lokaci yana rarrashi sannan tayi shiru ya taimaka mata zuwa toilet. A can ma daru ta dinga mishi, sai da ya daka mata tsawa ta shiga hankalinta ya mata abunda ya dace suka fito.
Bayan ta kimtsa ne ta fara sallar maghrib wanda Anwar ne ya tilasta mata tayi, don cewa tayi wai baza ta iya ba.
Kiran sallah Isha da ake yi yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga, mamaki yake yi na halayyar Nazifa akan addininta. Yana lura lokacin da suke toilet wankan da tayi sai da ya gyara mata, nan ma tana kumbure-kumbure ta yarda ta gyara, to gashi yanzu sallan nata ma taci gyara ba kad'an ba. Tashi yayi ya fita zuwa masallaci don bin jam'I. Bayan an idar ya fito shi da Musa wanda da alama ya rigashi zuwa masallacin.
A hanyarsu na dawowa gida Musa ke cewa,
"Ango, Ango yau kayi laifi amma ni nasha masifa, Surayya na ta bambami wai ka kori yara har da uwarsu."
Murmusawa Anwar yayi don shi bai ga abun tashin hankali anan ba.
"Adaman ne bata gane abunda nake nufi ba, ina nufin ta kai yaran ne kawai. Amma ai ta dawo har ta d'aura abinci, dama tana d'an son zaman ne shiyasa ta fake da cewa na koresu. Mata dai duk yanda ka musu baza kayi gwaninta ba."
"Shiyasa ban ma tsaya mata bayani ba na bar mata gidan na taho Masallaci. Ina Amarya? Naga alamar kamar ba sai mun maka rakiya ba." Musa ya k'arishe maganan yana kyakyatawa da dariya.
Anwar bai kulashi ba in banda murmushi da yake yi har suka iso gida. Anan ma hira suka ta6a kana Musa ya shige gidanshi Anwar kuma ya shiga motar ya bar unguwan.

Takwas dai-dai na daren Surayya ta dawo da su Nana, tana son zama tayi gulma ba sararin hakan don Musa yana gida yana jiranta ta d'aura musu abinci, bata so ba haka ta yiwa Adama sallama ta tafi.
Adama ta tambayi yaranta ko zasu ci abinci? Da sauri suka amsa, ehh zasu ci. Ta zubo musu Tuwo da miyan waken da tayi, a falonta kan sabon carpet ta ajiye musu suka hau ci. Suna gamawa tace su tafi d'akinsu su kwanta.

Tara saura kwata ya dawo da ledoji a hannunsa, d'akin Adama ya fara shiga ya mik'a mata nata kan ya wuce d'akin Nazifa da sauran.
Awa 1 da haka ya kira Adama a waya kan ta zo falonshi yana son ganinta. Hijabinta kawai ta zurma ta fito, a bakin falon tayi sallama ya amsa kana ta shiga ta zauna kan kujera.
Shiru tayi kanta a k'asa tana murza 'yan yatsunta a hankali. Anwar ne ya fara magana da godewa Allah kana ya fara nasiha kan zaman lafiya da kuma su had'a kansu d.s.
Adama mamakine ya cikata kan in Nazifan take! Don shigowanta Anwar din kad'ai ta gani a 2sitter. D'ago kanta tayi ta hango Nazifa a lafe jikin Anwar kamar ta shige cikinshi. Nazifa na ganin Adama ta d'ago kanta ta k'ara shigewa jikinshi tana yiwa Adama wani shu'umin murmushi. Murmushin Adama ma ta miyar mata har ana ganin alamar hakorinta. Kawar da kai Nazifa tayi don ba haka taso ba.
Yana gama nasiharsa ya tambayi Adama batun kwana, nawa-nawa za'a sa?
"Duk yanda kasa yayi." Ta bashi amsa kanta a kasa.
"Sweety a sa kwana hudu-hudu." Inji Nazifa tun kafin a tambayeta.
Shiru yayi kamar ba zai amsa ba don mak'aleshi da tayi a gaban Adama bai mishi dad'I ba. Tun kafin Adama ta shigo yace ta matsa amma tak'I wai sanyi take ji. Sannan ko 'yar kunyar nan ta Amare bai ga alamar tana dashi ba.
"Kwana hud'u yayi yawa, ina laifin biyu? Haka ya miki Adama?" Anwar ya k'ara tambayanta.
"Yayi. Allah ya za6a mana mafi alkhairi ya bada zaman lafiya." Ta fad'a tana murmushi wanda ke konawa Nazifa rai.
"Ameen Ameen." Anwar ya amsa da jindad'I a fuskarsa.
"Kefa Nazifa? Ya juyo yana k'ok'arin rabata da jikinshi.
Shiru tayi tana tura baki, fuskarta da alaman tayi fushi don meyasa ba'a bi shawaranta ba? K'ara nanata tambayarshi yayi sannan tace,
"Ba kun gama magana ba? Ni ai nawa ido ne."
"Ban gane nufinki ba." Anwar ya fad'a ranshi a d'an 6ace.
"Ai baza ka gane ba." Nazifa ta mayar mishi da amsa ta tashi ta shige bedroom d'inshi tana d'ingishi. Da mamaki yabi bayanta da kallo don bai ta6a zaton tana da raini haka ba.
Ganin haka yasa Adama ta mishi sallama ta fice tana 'kad'an ka gani'.

Washe gari Adama ce ta tashi tayi karyawa na d'umamen tuwo. Amarya da Ango suna can suna baccin huta gajiya, basu tashi ba sai kusan sha d'aya na rana. Akan Dinning Table suka ga Breakfast d'insu wanda har ruwan tea Adama ta tafasa musu, Nazifa cewa tayi baza taci tuwo ba, dole Anwar ya fita ya mata Take Away shi kuma yaci tuwonsa, don baya garajen girkin Adama ya wucesa. Kwana bakwai yayi a d'akin Amarya kan ya dawo d'akin Adama kamar yanda Addini ya tanadar. Sai dai da ya dawo bai nemi biyan buk'atarsa ba gurin Adama har ya gama kwana biyunshi ya koma d'akin Nazifa.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now