29

6K 441 19
                                    


Ana d'aura aure ranar Juma'a aka d'auko Amarya zuwa Bauchi gidanta ita da Adama da yake Anwar ya k'aura wani gida da ya saya nan kusa da gidan Musa. Dalili kuwa gidanshi na farko na zaman mace d'aya ne.
Nazifa shaye-shayen magungunan da tayi Allah kad'ai ya sani, wai duk akan burge Anwar. Tun kafin biki take fama da ciwon mara, ga wani wawan feelings da ke damunta kamar ta kai kanta.
Duk yanda take ji na ciwon bata daddara ba, don ranar da aka yi bud'an kai Zee ta kawo mata wani sinadari wanda ake had'awa da kankana da nonon Rak'umi.
Rabashi suka yi tare kowa gora d'aya, suka shanye har da gyatsa. Washe gari biki ya k'are dangin Amarya suka koma da safe, da yamma ciwon mara ya tasa Nazifa a gaba. Tun tana daurewa har tazo tana muk'urk'usu hannu dafe da mara, hawaye kuma na sintiri a fuskarta.
Gidan shiru 'yan biki duk an watse, Adama kuma na can d'akinta tare da 'yayanta.
Nazifa ganin zata mutu yasa ta d'auko waya ta kira Anwar.
"Yaya Anwar kazo gida, zan mutu wallahi. Cikina...cikina da marata.. wayyo don Allah kazo." Ta fad'a cikin sheshshek'ar kuka.
A kid'ime ya bar abunda yake yi ya shiga mota ya nufi gida. Direct d'akin Nazifa ya shiga ya sameta ta k'udundune akan gado. Tana jin shigowarsa ta mik'e da sauri ta je ta rungumeshi tana kuka."
"Me ya sameki Nazy, ina yake miki ciwo?" Ya fad'a a gaggauce Gaba d'aya ya daburce.
"Cikina ne da marata ke ciwo." Ta samu daman bashi amsa bayan ya zaunar da ita kan gado.
"Ko dai period d'inki ne?"
Girgiza masa kai tayi tana kallonsa idanunta na zubar da hawaye, ita kad'ai tasan ya take ji amma sai taji kunyar sanar dashi.
Tambayan duniyan nan ya mata amma tace ba period bane ciwon mara ne. Yace su tafi asibiti, nan ma tace a'a, ita baza taje asibiti ba.
Kanshi a kulle ya fito daga d'akin ganin ciwon ya d'an lafa. Waje ya fita gurin abokinshi Musa da suka taho tare, yana fita yaga Musa na fitowa daga nashi gidan rai a 6ace. Yana ganin Anwar ya nufoshi da sauri yana cewa,
"Me ya sameta hala?"
"Wai ciwon mara, kuma na tambayeta ko period ne tace a'a."
"To mu tafi hospital mana. Ka fito da ita muje aga likita" Musa ya fad'a yana k'okarin shiga mota.
"Tace baza taje ba. Na rasa gane me yake damunta. Lafiya fa take d'azu." Anwar ya fad'a yana jingine da motar hannunsa d'aya akan k'eyarsa, fuskarsa kuma damuwa faal.
Shiru suka yi na 'yan mintoci kana Musa ya dubeshi da murmushi yace,
"Idan kasha Kunun Aya wani irin ciwon mara kake fama dashi?"
Da mamaki Anwar ya dubeshi kana yace;
"Kai anya kuwa? It can't be!."
"Kaje ka tambayeta. In abunda nake tunanine better ka turo yara gidana sai ku fara amarcinku tun yanzu."
A sanyaye Anwar ya nufi gidansa, yana shiga ya samu Adama da 'yayanta a cikin gida sunyi cirko-cirko suna kallon d'akin Nazifa da sautin kuka ke fitowa. Da sauri ya kalli Adama yace,
"Kuje gidan Musa ke da yara, ina zuwa." Ya fad'a a gaggauce yayin da ya nufi d'akin Nazifa da saurinshi.
  Da saurinshi ya shiga d'akin Nazifa ya tarar da ita a falo tana durk'ushe a k'asa. Isa gurinta yayi ya d'agota yana shak'ar k'amshin jikinta wani abu na mintsilarshi.
"Me kika sha?" Tambayar da ya fara mata kenan, Nazifa tayi saurin had'iye kukanta ta d'ago da fuskarta tana kallonshi, zuciyarta kuma na dukan uku-uku cike da firgita. 'Muk'ut' ta had'iye wani yawu mai kauri ta fara in-ina.
"Wani abu kika sha ko?" Ya k'ara tambayarta yana nazarinta.
"Wallahi Zee ne....Zee ta bani wani abu. Ni banma san na menene ba, ashe maganine." Ta fad'a tana kyallara fiki-fikin idanunta.
'Magani' ya nanata a ranshi yana kallon k'asa.
Sarai yasan mata na shan wasu magunguna wanda illolinsu sun fi amfaninsu yawa. A iya zaman da yayi da Adama bai ta6a ganin tana shan irin abubuwan nan ba, kuma Masha Allah yana jinta yanda ya kamata, matsalarshi da ita shine; rashin tsafta. So Nazifan ma zai hanata don ba zai so wani abu ya sameta ba.
D'ago fuskarsa yayi yana kallon Nazifa da ta had'a gumi itama shi d'in take kallo.
"So, me maganin cutarki? Ya fad'a yana murmushi.
Sadda kai tayi k'asa cike da jin nauyinshi tana murza yatsun k'afanta a tiles d'in falon. Duk da ta saba arangama da maza bata ta6a ganin wanda take jin kunya kuma take ganin kwarjininsa ba irin Anwar. Duk iya shegenta da felek'enta yau babu shi.
Daga ita har shi abunda suke ji a jikinsu lokacin zai yi wuyar fassarawa.
D'agata yayi cid'ok kamar Baby yace,
"Akwai magani a d'aki. Muje in baki."

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now