46: Sauk'e Nauyi

7.1K 982 49
                                    


*Dedicated to All our Parents. Allah ya biyaku da Aljannah ya bamu damar faranta muku, ya kuma sa mu muku hidima a tsufanku.*

"Umma, kin aika kirana." Fad'ar Adama yayin da take zama a kan gado kusa da ita.
"Ehh, bani minti biyu in gama tura sak'o." Cewar Umman tana danna Laptop dake kan cinyarta, idanunta sake da Gilashin k'ara kwarin gani.
Minti kad'an da haka ta ajiye Laptop d'in a gefe, ta zare gilashin tana kallon Adama cikin kulawa, lokaci d'aya fuskarta ya canja zuwa kalar tausayi. Hannun Adama ta kamo ta rufe cikin nata tana bubbuga saman a hankali. Magana take son yi amma ta rasa harshenta, dalilin wani abu da ya tokare mata makoshi, tana ganin da ta bud'e baki zata iya yin kuka gaban 'yarta
"Umma wani abu ya faru, ko laifi na miki? Adama ta tambayeta tana matsowa kusa da ita fuskarta cike da damuwa. Bata son abunda zai ta6a mata Ummanta.
"Babu komai, babu abunda kika min." Had'iye abun ta yi sannan ta kalli Adama ta ce,
"Kina jina?"
"Ina ji. Ina jinki Ummana"
"Don Allah ki canja halayyarki ta baya, ba haka kike ba tun tashinki Adama. Ganinki cikin rashin kula ba k'aramin ciwo nake ji a zuciyata ba, na miki fad'a na miki nasiha amma bakya d'auka, koyaushe kina min alk'awarin zaki gyara. Ke mutum ce mai son tsafta Adama, kina da k'ok'arin gyara jikinki da muhallinki, ban san me ya sameki ko ya faru da ke kika canja dabi'unki ba, kuma a yanzu bana son sanin wannan dalilin Adama. Fatana da rokona d'aya a gareki, Don Allah kar ki koma rayuwarki ta baya, kar ki cuci kanki da ta 'yayanki Adama. Ki min alk'awari na k'arshe har cikin zuciyarki zaki daina Adama." Hawayen da ya zubo mata ta yi saurin gogewa don bata son tayar da hankalin 'yartata.
Adama da ta sauk'ar da kanta k'asa tun lokacin da mahaifiyarta ta fara magana ta d'ago kai, idanunta na tsiyayar hawaye. Hannunta da ke cikin na Umma ta ciro a hankali ta mayar da nata sama ta rik'esu, bata damu ta share hawayen da suke tsiyaya a idanunta ba, haushi da takaicin kanta take ji na watsar tarbiyyar da Ummanta ta bata tun tasowarta, lalle ta kasance mara dogaro da godewa Allah da ta bari maganar mutum d'aya ya tarwatsa rayuwarta ta jindad'i, ya kuma yi k'okarin canja halayyarta har ya shafi 'yayanta. Shin da har yanzu bata ankara ba haka zata cigaba da zama a matsayin k'azama mara kula da kanta da 'Yayanta? Shin ta yiwa Mahaifiyarta da 'Yayanta adalci kuwa?
"Umma ki yafe min watsar da koyarwarki da nayi. Umma na miki alk'awarin baza ki k'ara kamani da laifi makamancin haka ba. Nasan nayi kuskure a rayuwata, amma yanzu zan gyara Umma, bazan k'ara bari wani abu ya canja dabi'ata ya mantar da ni wacece ni ba. I promise Umma." Ta k'arishe maganan tana kissing hannun Ummanta da ke cikin nata, lokaci d'aya ta ware hannayensu ta rungumi Mahaifiyarta wanda a daa ta dade bata yi hakan ba, sai yau ta gane cewa ta yi kewar d'umin mahaifiyarta, duk girmanta har yanzu tana jin kanta tamkar jaririya a gaban Ummanta.
Umma da ke k'okarin 6oye hawayenta ta barsu suka zuba a karo a na biyu, ta fara shafa kan Adama tana jin tausayinta a zuciyarta, tare da wannan soyayyar dake tsakanin Uwa da D'anta. Sun jima a haka kafin Umman ta fara k'okarin d'agata daga kafad'arta.
"Ya isa haka. Tashi in baki albishir." Ta fad'a tana goge hawayen fuskarta.
Adama da take jin kyiwar rabuwa da jikin Mahaifiyarta ta nok'e kafad'a alamar baza ta tashi ba. Jin kanta take kamar Laila ko ma Yusuf a yanzu da take jikin Ummanta.
"Idan baki tashi ba zan fasa baki albishir d'in." Umma ta yi warning d'inta cikin wasa.
Tashi ta yi, tana goge fuskarta tana murmushi had'e da d'an dariya kad'an, zuciyarta cike da k'aunar mahaifiyarta.
"Kuka ba naki bane Adama. Ki godewa Allah kin canja tun kafin tafiya ta yi nisa. Albishirinki!"
"Goro Ummana." Adama ta fad'a tana dariya had'e da d'an zare ido don bata san wani albishir za'a mata ba.
Hannu Umma ta tura k'asan pillow ta ciro Key guda biyu tana ajiyewa kan cinyar Adama.
"Kyauta ce daga Daddynku, wannan na mota ne, wannan kuma na gida wanda yanzu haka akwai 'yan haya a ciki." Ta fad'a tana nuna mata keys d'in da yatsa.
Adama rufe bakinta ta yi da dukan tafukan hannayenta tana hawayen jin dad'i.
"Umma...." sai kuma ta yi shiru, k'ara hugging d'inta tayi tana cewa,
"Nagode Umma, Allah ya biyaku da Aljanna, yasa mu muku hidima idan tsufa ta kawo."
"Ameen, Ameen." Ta fad'a.
Adama ta yi breaking hug d'in tana jujjuya Keys d'in a hannunta cike da murna.
Bata san lokacin da Umma ta tashi ta bud'e wardrobe ta ciro wani kit karami ba, a tsakiyarsu ta ajiye tana budewa da tace,
"Ga ajiyarki nan."
Set na Sarkokin Gold ne manya-manya guda uku, sai wasu k'anana masu kyau guda hudu.
"Manyan naki ne, k'ananan na su Nana. Ban baki su ba saboda nasan baza ki kula dasu ba, shiyasa a duk lokacin da na saya miki sai na 6oye a gurina."
Cikin mamaki ta ajiye Keys d'in ta d'auko sark'ok'in idanunta taff da hawaye.
"Umma..duka.."
Bata ida ba Jamila ta shigo idanunta kan sark'ok'in baki bud'e.
"Umma, wannan na waye?" Ta tambaya tana d'aura wani kan wuyanta tana kallon kanta a madubin d'akin.
"Na Addarki." Ta bata amsa tana kallon Adama da take rike da na su Nana da Laila tana kallo.
"Umma gaskiya ban yarda ba. Nima a saya min irinsu, nawa basu kai wannan kud'i ba."
Dariya su Adama suka yi suna jin surutun Jamila na cewa lallai itama sai an saya mata irinsu.
(Nima fitowa nayi a d'akin don gaskiya I'm jealous. :D)

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now