24

5.3K 392 1
                                    


"Ya kake ganin zanyi?" Anwar ya fad'a bayan ya gama koro bayani.
Musa ya gyara zama ya zuba tagumi yana kallonshi a ranshi yana cewa 'baka da damuwa'.
"Kaje ka sameta ku sasanta kawai. Me abun 6oye-6oye tunda tana da labarin kai zaka aureta. Abunda nasha fad'a maka shi zan maimaita; kaje ku fahimci juna kabar wannan shegen girman kan naka. Nikam wallahi mamaki kake bani. Wannan wani irin ra'ayine? Idan kuma baza ka iya ba ka fasa auren kawai, dama auren babu komai cikinshi sai wahala." Sauk'e tagumin yayi ya jingina da bishiya ya mik'ar da kafafunsa.
"Nasan akwai abunda yake damunka Musa. Ka fad'a min, menene?" Anwar ya tambayi abokin nashi cikin damuwa lura da yanayinshi tunda ya zo.
"Kasan komai na rayuwata Anwar, idan zan 6oye wani sirrina to kai dole ne ka sani. Ka zama d'an uwana shak'ikina. Banida kamar ka Anwar..."
"Stop all this and tell me whats going on." Anwar ya katseshi don gaba d'aya kalamansa sun rikitashi, baya son yaga Musa cikin damuwa a cewarsa he had had enough.
"Na rasa gane me yasa komai a rayuwa yake zuwa min ba dad'I. Sanin kanka ne yanda nasha wahala wajen Matan ubana. Haka na taso abun tausayawa dalilin uwa da na rasa. Ban samu 'yancin kaina ba sai da Mahaifina ya rasu ina secondary school na shiga d'awainiya da kaina. Ba sai na tsaya tuno maka da dukkan abunda ya faru ba har nauyin karatuna da Babanka ya d'auke min na gama Jami'a."
Share kwallan daya taru a idonshi yayi, ya kawar da kanshi daga kallon da Anwar ke mishi kana yaci gaba..
"Na taso ne a wata rayuwa da babu kulawa babu tausayawa, ban san wani abu wai shi soyayyar 'yan uwa ba both dangin Mahaifiyata da na Mahaifina. Zan iya cewa duk duniya kai kad'ai ne ka jani a jiki kake tausaya min kake sona. Ka tuna lokacin da muke karatu nace da kai mace ce babu abunda zai hanani aurenka?"
Jaddada kai Anwar yayi yace
"You were mad a lokacin." Yana murmushin yak'e.
Anwar yaji tausayin abokin nashi don yasan ba k'aramin abu ne ya sakashi tuno wannan tarihin ba.
Dariya musa yayi yace,
"I was so stupid da nake tsammanin akwai wani halitta da zai soni bayan kai. Na nemi mata da niyyar ta maye mini gurbin iyayena da na rasa, ta maye mini gurbin 'yan uwa da na rasa masu sona, ta shafe memoryn kad'aici da nayi a baya, ta nuna mini so tamkar rayuwarta. A haka na shiga na fita na samu Surayya. Kasan irin soyayyar da muka yiwa juna, wanda a tunanina idan muka yi aure har goyani zata yi in na buk'aci hakan. Ashe duk Imagination ne wanda yake a rubuce Impossible."
Juyowa Musa yayi gefen Anwar yana dariya kamar bashi ke bayar da labarin rayuwarsa mai d'aci ba.
"Kasan me? Surayya bata damu dani ba, kasuwancinta kad'ai ta saka a gaba. Yau wata d'aya har da sati uku da aurena amma banji dad'I full na rana d'aya ba. Koyaushe gidana cike da mata 'yan kasuwa da masu d'auka mata tallah. Koda na dawo daga office na shige d'aki wallahi baza ta biyoni ba sai ta gama harkokinta da su, abinci mai kyau gagarana yake yi Anwar. Daga indomie, d'an wake sai taliya, ko kuma ta siyo mana masa a nan makwabta duk da sunan wai ta gaji. Wata rana haka zata fita kasuwa sarin kaya ba tare da ta fad'a min ba, sai dai in dawo in bud'e gidan in shiga zaman jiranta. To sati biyu da ya wuce nayi mata magana kan abubuwan da take mini, bud'ar bakinta cewa tayi ina mata hassada da samun kud'in da take yi."
Nuna kanshi yayi da yatsa saitin k'irjinshi yana murmushin takaici yace.
"Wai ni nake mata hassada, Anwar ni nake mata hassada, matar tawa zan yiwa hassada? Can you believe it?. Abunda ya faru a ranar babu dad'in fad'a. Ta koma gidansu bayan kwana biyu aka mana sulhu, na nemi ta bar kasuwancin tunda ban gaza ta ko'ina ba. Iyayenta suka ce in barta da sana'arta saboda sun mata fad'a zata canja. Haka ta dawo da alk'awarin ta daina mayar da gidana kasuwa. Ashe aikin banza nayi wai an danne bodari ta ka."

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now