09

6.2K 492 11
                                    

Washe gari ya kama girkin Nazifa amma har ya fita aiki bata je ta kar6i k'udin cefene ba kamar yanda suka saba a al'adan gidan, hasalima ko fitowa bata yiba har Adama ta tura yara school ta kammala abincin rana.
Adama taji kamar ta lek'a Nazifa amma wata zuciyar ta haneta tace 'yunwar cikinta ma zai fito da ita'.
Ai kuwa yara na dawowa daga school 12:30 ta fito itama.
Fuskarta a kumbure yayinda lokaci d'aya ta d'an rame kamar ba ita ba.
Direct kitchen ta nufa ta d'ebi Rice nd Stew da Adama ta girka kana ta koma d'akinta ba tareda ta kula kowa ba. Adama na ganin haka tayi kwafa.
K'arfe 8 da 'yan mintuna na dare Nazifa ta fito kai tsaye ta wuce kitchen don d'iban abinci. Wayam taga babu warmers d'in da ake zuba abinci.
Falon Adama ta shiga ta d'aga labule tace
"Adama ina abincina?"
Shiru Adama tayi yayinda ita da 'yayanta suke cin tuwo miyar taushe. Sosai k'amshin miyan ya daki hancin Nazifa. Ranta ya 6aci da shareta da Adama tayi amma ta dake tace;
"Maman Laila dake fa nakeyi".
"Hala kin manta yau girkinki ne ko?" Adama ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba.
"Ehh na sani, amma ai kinsan bana girki in mun sami sa6ani da maigidan, ke kike girkawa kuma kinayi dani".
"Hakane, nima sa6ani na samu da maigidan shiyasa na daina yin girkin gida, illah inyi daidai cikina dana 'yayana, kema zaki iya dafa naki ba dole sai kinyi da maigidan ba".
Bak'in ciki ne ya turnuk'e Nazifa wai yau ita Adama ke fad'awa haka? Ga yunwa kuma tana ji, ga abincin ya bata sha'awa tasan tabbas Adama da yawa tayi abincin. Hala itama ta fara kilewa ne.
"Naji, yanzu dai a bani na daren tunda kinga lokaci ya k'ure bazan iya d'aura tuwo ba". Cewar Nazifa bayan ta gyara tsayuwarta a bakin k'ofar.
Nana tayi karaff tace
"Ki dafa indomie ko taliya".
Harara Nazifa ta watsa mata, tayi gum da bakinta don ba wuya yanzu ta lakad'a mata duka kuma mamanta baza ta kwaceta ba.
Tsaki Nazifa taja ta juya tayi kitchen ganin cewa Adama ba kulata zata yi ba. Wai tukunna ma Yaushe Adama ta fara kilewa ne? Da Alama raini ya fara shiga tsakaninsu kuma zata yi maganinta, ta k'ara wani tsakin.
Ko da ta shiga kitchen d'in kasa dafa komai tayi don ita wannan miyar taushenne ya shiga ranta, miyar taushen Adama ai ba abun ya wuceka bane. Tayi tsaki yafi sau sittin har ta gaji ta d'aura ruwa don dafa indomie.
"Anty Nazy wai ga tuwo inji Mama". Cewar Laila tana mik'a mata plate cike da tuwon.
Juyowa tayi ta kar6i kwanon, ta kashe gas cooker dama bata saka indomie d'in ba.
Sai data gama cinyewa ta lashe kwanon ta dawo hayyacinta anan kuma ta fara jin haushin kanta, uban meyasa ma ta kar6a?

Daga ranar ta fara girkinta Ita kad'ai, in ta gama ta shige dashi d'aki koda ran girkinta ne. Kuma bata kula kowa.
Adama ganin haka yasa itama ta kama kanta bata kulata don ita hakan ma yafi mata. A cewarta in ta biyewa Nazifa zata kaita ta barota.
Anwar duk yana ganin take takensu yayi shiru ya zuba musu ido, don sun d'auki abun da zafi. Gwanda ma Adama in ranar girkinta ne tanayi dashi kuma in ya buk'aceta bata mishi musu, sai dai a ranar girkin Nazifa bazata yi abinci dashi ba kuma koya nemeta bata kulashi, dama kafin ma ya dawo ta kulle d'akinta da lock d'in jikin k'ofa ta yanda key bazai bud'e ba.

Yau ta kama saturday anje anyi tambaya har ansa rana 1month 3weeks masu zuwa za'ayi biki.
Sosai baffanun Anwar suka yaba da karamcin da dangin Sa'adatu suka nuna musu, duk da cewa su K'ABILA ne, musamman mahaifinta daya kasance mutum mai daraja da datalinko a garin nasu.

Ranar da daddare ya kama girkin Nazifa ce, sai da ya dawo ya kintsa, dama already yaci abincinshi a restaurant kana ya kirasu a waya kan suzo falonshi.
Adama ce ta fara zuwa ta zauna can nesa dashi kana ta gaisheshi.
Shiru shiru har kusan 5mins babu alamar Nazifa. Tashi yayi ya zagaya ta bayan d'akinta ya bud'e window ya kira sunanta cikin 6acin rai.
A tsorice ta juya tana kallon window don ta d'auka aljani ne.
"Wallahi kika k'ara minti 2 baki zo ba sai na nuna miki 6acin raina, ko baki ji ba?
"Naji ai" ta fad'a cikin tsiwa, amma ta tsorita ainun.

5mins later

"Kamar yanda na fad'a muku zan k'ara aure , to yau Allah ya nufa Anje anyi tambaya har an bayar, and an saka rana 1month 3weeks nan gaba Insha Allah. So abunda yasa nake fad'a muku komai dangane da auren nan shine: Bana son ace na munafurceku na 6oye muku wani abu, ko kuce yanzu bana sonku nafi sonta. Da sauran gutsuri tsominku na mata.
"Na nawa kuma munafurci kam? Cewar Nazifa k'asa k'asa amma Anwar yaji abunda ta fad'a Sarai. Bai kulata ba yaci gaba
"Sunanta Sa'adatu, k'awar Karimatu ce matar Musa."
"Me kace?"
Cewar Nazifa jiki na kyarma ta mik'e tana nuna Anwar da yatsa..
"Kana nufin itama.... daga.. daga kudu take?"
"Kwarai da gaske." Ya tabbatar mata.
Wannan karon Adama ce ta fara fita tana k'ok'arin danne hawayen da suke son wanke mata fuska. Ido ya bita dashi har ta fice.
A sukwane Nazifa tayo kanshi, tana isa ta zube a k'asa ta rik'e kafafunsa.
"Don girman Allah Baban Laila, don darajar Annabi karka auro mana 'yar kudu! *MATAR K'ABILAH* Anwar? Ka dubi girman iyayenka ka fasa auran 'yar kudu. Wallahi na yarda ka auri biyu akaina hausa ko fulani amma banda MATAR K'ABILAH! Baban Nana dai, wayyo Baban Nana! Yau na shiga uku na lalace k'arshena yazo a gidan nan."

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now