40

5.9K 523 32
                                    


Sai a lokacin su Adama suka hangota suka nufi gurinta cike da tausayi, don sun ji duk abunda ya faru, takanas har gida wata makwabciyarsu tazo ta zayyane musu komai.
Kafin su isa gurinta suka tsinkayo muryan Anwar cikin k'araji yana cewa,
"Wallahi duk matar da ta isa wajenta sai ta bita."
Ai kamar an dasasu suka tsaya a in da suke, kowacce jikinta yayi sanyi, zuciyarsu cike sa tausayin Nazifa.
"Ku 6ace mini da gani yanzun nan." Sum-sum Sa'adatu da Adama suka wuce part d'insu don babu damar musu da Anwar da ya rikid'a zuwa Zaki.
Nazifa na ganin haka tasan cewa lallai itama yau asirinta zai tonu muddin Anwar ya koreta daga gidansa, ina zata je? Gidan iyayenta da ta wofintar don ta samu daula ko kuma duniya zata shiga?
Ganin bata motsa daga in da take ba yasa Anwar d'aukan akwatunanta ya nufota yana doka mata kallon tsana.
Nazifa na ganin haka ta k'ara gigicewa ta fashe da sabon kuka tana yarfe hannu. Kafin ya iso ta fara cewa,
"Ka rufamin asiri don Allah Baban Laila, wallahi sharrin shaid'an yasa na fita ba da izininka ba. Wallahi bazan k'ara ko da tari ba muddin baka yarje min ba. Ka tausayamin, ka tausayawa maraicina. Na tuba Baban Laila. Ka rufa mini asiri yanda Allah ya rufa maka naka. Na shiga ukuna."
Wuceta yayi tana magiya tana binsa amma ko kulata bai yi ba, sai ta ya je bakin gate ya ajiye akwatunan ya kalleta yace,
"Ni na baki dama tun zuwanki gidannan kike min abunda ranki yake so, a tarihi babu macen da ta ta6a d'aga mini murya ko ta mini rashin kunya sai ke. Duk rashin hankalinki nayi hakurin shanyesu amma yanzu kin kaini bango, akan wasu 'yan iska kika tsallake umarnina da na gindaya miki. Me zasu baki ko me zasu miki? Bazan miki dogon bayani ba, dama na fad'a miki Duk ranar da kika fita ba tare da Izinina ba a bakin aurenki, don haka Ni Anwar na sakeki saki d'aya takardarki na cikin kayanki da duk abunda zaki buk'ata. Zan aiko miki da sauran kayanki har gida saboda bana buk'atar k'ara kallon fuskarki Nazifa."
Nan ya kira Maigadi ya fitar da akwatinan ya tara mata Keke Napep ya sakasu ciki.
Nazifa tunda taji maganar saki komai na jikinta ya daina aiki, tunaninta ya tsaya cakk! Har aka saka mata kayanta cikin Napep bata sani ba sai ji tayi Anwar na cewa,
"Na baki minti biyu ki fice mini a gida, idan na dawo na sameki anan baza kiji da dad'i ba." Yana fada'an hakan ya juya ya shiga falonshi zuciyarshi na suya.
"Hajiya mai Napep d'in yana jiranki." Cewar Maigadi cike da tsoro don yasan halinta sarai na rashin mutunci.
Sai dai Nazifa bata ce komai ba asalima ji tayi kuka ya zo mata, lalle yau Ruwa ya daki Babban Zakara. Haka tana ji tana gani ta saka k'afa ta fita daga gidan da take ik'irarin nata ne, gidan da take jinshi kamar Aljannarta, gidan da yasa ta banzatar da tushenta ta daina ziyartarsu. A yau an mata koran kare a gidan da take ganin babu abunda zai rabata dashi sai mutuwa, a yau Ungulu zata koma gidanta na Tsamiya. Tana shiga mai Napep ya kunna inji yana cewa
"Ina zamu je Hajiya?"
Cikin kuka tace,
"Tasha."

Minti goma ya kaisu tasha, sai a lokacin ta fara tunanin me zata bashi ita da bata fito da ko sisi ba, shiru ta yi tana tunanin mafita, ganin Mai Napep tsaye kusa da ita da alama kud'inshi yake jira yasa ta bud'e akwatinta tana d'an duddubawa gudun kar ya mata rashin mutunci a bainar jama'a.
A can k'asan kayanta taci karo da Kud'i da akalla zasu yi dubu ashirin, da ATM card d'inta da duk tarkacen da zata buk'ata, can k'asansu kuma Takarda ce fara a nannad'e. Wasu sabbin hawaye taji sun gangaro kan kuncinta tayi saurin gogewa ta dauki D'ari biyar ta bashi kana ta rufe akwatin ta kutsa cikin tasha neman motar garinsu. Shatan mota guda ta d'auka suka harba titi lokacin biyar saura mintuna.

Nazifa bata isa gida ba sai 12 na dare, Allah ya taimaketa drivern dattijon kirki ne magana wannan baya mata in bai kama dole ba. Har k'ofar gida ya ajiyeta ya tsaya jiran a bud'e mata kar ya tafi ta shiga wani halin.
Tafi minti biyar tana kwankwasawa ba'a bud'e ba, su kuma cikin gidan gaba d'aya sun tashi a tsorice don sun d'auka samarin da Ma'u K'anwarta ta yiwa rashin mutuncine suka zo d'aukan fansa.
"Ki kwala musu kira mana." Dattijon ya fad'a yana gyara tsayuwarsa.
Nan ta shiga kiransu tana cewa su bud'e mata. Da kyar Ma'u ta fito da torchlight a hannunta tana haska bakin k'ofar.
"Waye ne?" Ta fad'a a tsorice don in ba k'arya kunnenta suka mata ba muryan Nazifa ta jiyo.
"Nice Nazifa, Nazifanku. Kizo ki bud'emin." Nazifa ta bata amsa daga waje.
Da gudu Ma'u ta koma d'akinsu tana fad'awa Mamansu muryan waye ta jiyo.
"Muje in ji. Don bana tunanin Nazifa ce da tsakar daren nan, watakila 'yan iskan yaran nan ne suka biyoki."
A haka suka k'ara zuwa bakin k'ofar suka tambaya, Nazifa kamar ta yi kuka ta shaida musu itace. Nan suka bud'e mata ta shigo da kayanta bakinsu a bud'e suna mamakin ganinta a wannan talatainin daren.
Ta bud'e akwatinta ta ciro kud'in Mai Mota a yanda suka tsadance ta fita ta kai masa. Kar6a yayi ya shiga motarsa yana cewa,
"Sai gani na biyu. Mu kwana lafiya."
Da haka ya tashi motarshi ya 6ace cikin duhun dare.
A can k'uryan d'akin Mamanta tayi masauk'i ta ajiye akwatinanta a lungu d'aya har lokacin bata ce dasu k'ala ba, su ma babu wanda ya mata magana sai bin ta da ido kawai suke.
Bakin gado ta zauna ta dafe kanta nan da nan abubuwan da suka faru ya dawo mata sabo k'al ta fashe da kuka. Mamanta da ke tsaye a kanta tana jimamin halin da 'yartata da dawo ciki ta kori k'annen falo kana ta zauna kusa da Nazifa.
"Me ya faru Nazifa? Wani abun suka miki?"
"Ya sakeni Mama, ya koreni a gidansa. Ya rabu dani." Nazifa ta fad'a tana kuka mai tsuma zuciya.
"Ya isa haka nan. Kiyi shiru gobe zamu yi maganan, yanzu dare yayi ki kwanta ki huta gajiyan hanya kinji?" Maman ta fad'a cikin dakewa don mummunan labarin da Nazifa ta kawo mata ya daki zuciyarta.
"Mama ki yafemin yanke alak'ar da nayi daku, Mama alhakin hakan shi ke bibiyata. Na wofintar da ke da k'annena akan daular da bani da tabbacin mutuwa a cikinta. Mama ki yafemin don Allah, ki yafemin." Ta fad'a tana rungume Maman wacce itama kukan ta fara, duk yanda take jin haushin sharesu da Nazifan ta yi bata k'i a ce ta dauwama a gidanta na aure ba. Ba za taso a sako mata 'yarta ba ko da kuwa abunda tayi yafi haka.
Da kyar ta lallashi Nazifa tayi shiru sannan suka kwanta kowa da tunanin da yake yi a zuciyarshi.
Nazifa dai gata a d'akin da babu POP ba A.C balle makeken gado mai d'auke da katifa mai taushi, da kyar baccin wahala ya kwasheta anan kan gadon Mamanta.

Su Adama sun yi matuk'ar girgiza ganin tafiyan Nazifa, musamman Sa'adatu da take son k'aryata zancen K'abilansu na cewar Bahaushe baya rik'e aure. A ranan kwana suka yi sukuku har Anwar na tambayar Sa'adatu me ya sameta tace babu. Shi kanshi jinshi yake yi incomplete tamkar ya rasa wani shashe ne na jikinsa, amma babu yanda ya iya, rabuwa da Nazifa shine samun kwanciyar hankalinshi.
(Duk zaman da kike da ita ki sani a yau aka ce bata nan sai kinji wani iri, ko yankar naman junanku kuke yi kuna soyawa watarana sai kinyi kewarta saboda sabo turken wawa. Idan sun rabu karki nuna jindadinki a fili in kina jin dadin ko shi yana nunawa, don baki san ainihin abunda yake ji a zuciyarshi a wannan lokacin ba sannan baki da tabbacin kema hakan bazai faru dake ba. Ki kula. Allah ya barmu da mazajenmu ya bamu hakurin zama tare.)

Ina masoyan Nazifa? Ya kamata ku tayata kokawa, rabuwa da gidan miji ba wasa ba wallahi.

#MK
#MumFateey

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now