06

6.9K 520 7
                                    


Adama da safe ta tashi tayi break fast, Bayan sun gama ci ta yiwa yaranta wanka ta turasu gidan kakaninsu Iyayen Anwar, don jiya sun aiko cewa yaran su je musu weekend.
A falo ta ajiyewa Nazifa nata karyawan kana ta ajiyewa Anwar nashi kan dinning table. Zata fita kenan ya fito daga room d'inshi yana zuba k'amshi k'ananan kaya ne jikansa wannan karon.
Ta gaishe shi ya amsa yana kallon mahaukaciyar shigar da tayi. Rigan atamfa, d'ankwalin material da zanin lace, kuma kowanne kalan shi daban. Fita tayi ya kad'a kai ya hau dinning table don karya kumallo.
Bayan ya gama kai tsaye ya wuce d'akin Nazifa.
Bacci ya sameta takeyi ta bararraje watakila ko sallah Asuba bata yi ba.
K'afarta ya buga
"Nazifa, Nazifa"
Ta farka tana hamma kamar mayunwaciyar zakanya. Tsaki taja ganin Anwar ne tsaye a kanta. Ko k'ara kallonshi batayi ba ta shige toilet ta barshi nan.
Murmushi kawai yayi ya fice.

Nazifa na fitowa daga toilet tayi sallarta, ko addu'a babu ta tashi ta wuce falo. Abincinta ta gani wanda Adama ta ajiye mata ta fara ci ba ko bismillah.
Sai da tayi nakk, ta fit0 da kwanon zuwa tsakar gida.
Mai musu shara da wanke-wanke ta hango tana tattara kwanuka ta mik'a mata na hannunta tace;
"Gashi Laraba, idan kin gama aikinki zaki share min d'akina, kinji?"
Shiru Laraba tayi don ba yau ne na farko da Nazifa ke sata sharan d'akinta ba kuma baya cikin aikinta da suke biyanta.
"To" kawai ta furta mata kana ta kar6i kwanon ta kai gurin wanke-wanken.
Da harara Nazifa tabi bayanta kan ta shige d'akin Adama don samun mafita. Don ita har yanzu bata daddara ba. Kuma ta d'au alwashin muddin tana numfashi k'arya ne Anwar ya mata kishiya.
Bata jima a room d'in ba ta fito, fuskarta babu alamun nasara. Gyalenta ta zara ta fice zuwa gidan wasu k'awayenta 'yan zaman kansu, babu wanda yasan daga ina suke kuma me suke yi.

Su biyu ne kawai a gidan Hindatu wacce tayiwa kanta lak'abi da Hindy sai Ruk'ayya ana kiranta Rocky.
Nazifa ta kasance mace mai son tara k'awaye birjik, bayan aurensu da Anwar ta dinga bin matan unguwan a cewarta tana son tafi Adama jama'a da k'awaye. Sai dai ba daga nan take ba, wai an danne bodari ta ka.
Halinta in ba mai hakuri ba babu mai jurewa. Tana da son kai, ga mak'o da kwadayi, idan musu ya had'aka da ita dole kayi shiru don d'aga murya zatayi tana surutai marasa kan gado. Tana da nuna isa, wai ita matar mai k'udi. Kuma addini ba wai ya dameta bane. Muddin zata ci ta k'oshi kuma taji Bank accnt d'inta da tsoka bata da damuwa. Wannan kad'an kenan daga halin Nazifa.
Babu sallama ta kutsa kai cikin gidan sanin ko tayi ba amsawa zasuyi ba.
A falo ta tarar da Rocky tana danne-danne a waya, a yatsine ta kalli Nazifa tace
"Idonki kenan?"
"Ke dai bari, Anwar ya saka min dokan fita, ashe munafuki yasan me yakeyi".
Ta k'arishe maganar fuskarta zallan 6acin rai, har hawaye na taruwa a idonta.
Dai dai nan Hindy ta fito daga d'aki tana wani kwarkwasa, bayanta kuma wata shegiyar Hajia ce wanda da ganin suturun jikinta kasan kud'I sun zauna. Matar tace;
"Hindy don Allah karki manta dani, Ina jiran call d'inki".
"Ok, A huta gajiya hajiya". Cewar Hindy wacce har ta samu guri ta zauna a d'aya daga cikin kujerun da suke falon.
A marairaice hajiyar ta kalleta tace
"Babu ko rakiya ne?"
"Next time please, kema kinsan a gajiye nake".
Ganin Hindy na basar da ita kuma ga hararan da Rocky ke aika mata yasa Hajiyar ta fice tana cewa;
"I will be expecting your call".
Nazifa ce ta maida dubanta kan Hindy tace
"Wacece kuma wannan matar? Ko itama yayarki ce?"
"Nazifa kiyi abunda ya kawoki ki tafi, sanin kanki ne bana son yawan tambaya. Uwata ce".
"Kiyi hakuri Hindy, ai ban san Mamanki bace wallahi. Gashi ko gaisawa bamu yi ba tunda kince bakya son Ina kula bak'inki mata. Allah sarki Ke ko ai mahaifiya ta wuce haka, yau rakiyan ma sai ta rok'a Hindy? Kuma kice wai kin gaji, d'an nan da bakin gate.....".
Dariyar da Rocky takeyi yasa Nazifa yin shiru tana kallonta irin me abun dariya anan? Daga nasiha kawai?
Hindy ta 6ata fuska sosai tace
"Ya isheki haka Nazifa...." taja tsaki.
"....Tukunna ma uban me ya kawoki da sassafen nan?"
Inda sabo Nazifa ta saba da wulakancin k'awayen nata musamman Hindy mai gaya mata maganganu d'atata babu ko sakayawa, sai dai dole take basarwa don tana son kasancewa tare dasu, dalilin a gurinsu take ganin latest fashion tana kwaikwaya Kuma suna bata shawarwarin banza sakk irin yanda take so.
Nazifa cikin sanyin murya tace;
"Hmm, ku tayani jaje, Anwar ne zai k'ara aure." Ta karishe maganan tana Jan majina idanunta fal da hawaye.
Kallonta sukayi shek'ek'e kana Rocky tace;
"To, menene don zai k'ara auren?"
"Kishiya fa za'a min Rocky, wacce a yanzu ita zata zama amarya 'yar gaban goshi. Wanda idan nayi wasa ma sai ta fitar dani a gidan, kishiya fa Rocky, Kishiya!!"
Rocky ce ta girgiza kai tace
"Dama haka mutane suke, da sunga kana sonsu sai su so bak'anta maka, kuma sukan manta duk irin d'awainiya da tarin son da ka nuna musu ada, sai ki dau hak'uri."
Hindy ta dubi Rocky tace;
"Wani lokaci kuma condition ne ke sa mutum canja shek'a babu yanda ya iya, kuma ai da tsohuwar zuma ake magani sweet Rocky nah".
Ta k'arishe maganar tare da kanne mata ido.
Nazifa kallonsu tayi don bata gane in da maganarsu ta dosa ba duk da ta gane wasu kalmomin.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now