38

5.6K 478 54
                                    


Washe gari Adama ta kyar ta tashi ta shirya yara zuwa school, dalilin zazza6in da ciwon kan da ta kwana dashi bai barta ba har lokacin, sai kusan k'arfe takwas na safe ta samu ta gama breakfast. Abdallah da yazo tun 7 shi ya taimaka mata da wasu abubuwan, don yanda ya ga fuskarta a kumbure, da ya tambayeta tace bata da lafiya ba k'aramin tausayi ta bashi ba. A hanyarshi ta dawowa ya tsaya a wani Chemist ya saya mata magani sannan ya shigo gida.
"Aunty Adama ga magani kisha kafin Ya Anwar d'in ya tashi ya kai ki Asibiti."
"Da ka barshi ma kawai Abdallah, zan samu sauki insha Allah."
"Kin hana in kaiki Asibiti saboda Ya Anwar bai baki izinin fita ba, shin maganin ma sai ya tashi ya baki izini kafin ki sha?" Abdallah ya fad'a ranshi a 6ace saboda yana ganin kamar Yayansa baya kula da ita.
  "A'a, kasan ni bana son shan magani ne, amma dai bani in sha tunda ka siyo d'in." Ta fad'a tana murmushin k'arfin hali.
Bai yarda ya tafi ba sai da ta sha maganin a gabanshi. Ya kira mai musu wanke-wanke da shara ta tattare mata kitchen d'in ta gyara, ta fita da sauran can in da suke wankewa. Abdallah sai da ya tilasta Adama ta shiga d'aki ta kwanta wai tayi baccin awa biyu. Ita dai binshi kawai take da murmushi don yanda ya tak'arkare yana fad'a kamar yaje ya doki Yayansa wai baya kula da ita. Tana kwanciya kuwa baccin ya sureta.

Tun Asuba Amarya da Angonta suka tashi suka yi sallah, karatu suka yi na 15mins, kana suka koma bacci bisa jagorancin Anwar. Sa'adatu tana ganin yayi bacci ta tashi a hankali ta sauka k'asa, shara da goge-goge ta fara sannan ta shiga kitchen ta d'ora musu karyawa. Bakwai na safe ta gama ta zuba a kula ta jera bisa Dinning Table sannan ta fita daga side d'in zuwa nata.
Acan tayi wanka da make up ta kara komawa side d'in Anwar ta tasheshi yayi wanka sannan suka fara karyawa.
"Yau kuma Adama doya da kwai zallah ta yi?" Anwar ya fad'a bayan ya kai lomarshi ta farko.
"A'a, yau nice nayi girki." Sa'adatu ta bashi amsa tana murmushi.
"Ohh, Ok. Yayi dad'i Amarsu. Ashe ke d'in ma ba baya ba wajen iya girki. Kinga in Adama zata yi doya da kwai tana mini sauce na Hanta ko Jan Nama ta saka doyan a ciki, ko tare take dafawa ne ohoo? Bansan dai ya take yi ba, amma zansa ta koya miki don yafi mini dad'in ci."
Muk'ut Sa'adatu ta had'iye yawu mai d'aci, can k'asan zuciyarta ba ta ji dad'i ba. Ai bai kamata a karon farko na girkinta ya nuna ba haka yake so ba. Wai har cewa yake matarsa zata koya mata girki?
Shi ko gogan ko a jikinsa yaci gaba da cin abincinsa.
Tayi d'an murmushi yak'e tace,
"Ya kamata in koyi wannan sauce d'in kam Habibi."
Ya gyad'a mata kai.
Gurin had'a Tea ma sai da ya sa ta kawo masa lemon tsami ya matse a ciki wai saboda yaci maik'o, ai tun aurenshi da Adama in tayi abinci mai maik'o tana saka mishi lemon tsami a Tea ko Juice.
Da suka gama ya jata falo yana nuna mata abu a Laptop amma hankalinta baya gurin, yana can tana tunanin hanyar da zata bi ta koyi wannan sauce d'in gurin Adama har ma yafi nata dad'i. 'Dolene in koyi sauce d'in don girkina ya fi k'ayatar da kai.' (Anya hakan zai faru Sa'adatu?) Ta fad'a a zuciyarta kana ta maida hankali kan laptop din.
(Kunji fa Sauce ta kudiri aniyar koya! Ke fa da kishiya ta miki fintikau ta kowanne fanni amma kina zaune guri d'aya kina cewa ba ya miki adalci. Ta yaya zai miki adalci ba ya jin zam-zam? Kar ku manta fa shi namiji kamar yaro yake, duk in da ake mishi abunda yake so nan zai tare. Wallahi duk son da yake miki sai kin ga ba dai-dai ba muddin kika kasa kula dashi da abunda yake so. Ki kula!)

Adama tunda ta kwanta ita ce bata farka ba sai 11am, a hankali ta mik'e tana kallon yanda gadonta ya jik'e da ruwan nono jagab. Ta ji dadin jikinta don babu ciwon kan, ba zazza6i, ga nonon mai sun daina zafi da zogi. Fanka ta kunna ta k'ure power don zanin gadon ya bushe kana ta shiga bandaki ta kama ruwa ta fito falo. Ko'ina tsab daga falon har kitchen wanda tasan umurnin Abdallah ne. A gurguje ta d'ora abincin rana shinkafa da wake, bata gama ba yara suka shigo da sallama wanda muryan Imam ta fi ta kowa k'arfi dalilin shi yau Lailah ta bashi labarin abunda Aunty Sa'adatu ta koya musu.
Abdallah da ya dawo dasu ya shigo ya mata ya jiki ya fita. Anan ta zubawa yara abinci suka ci.

Sa'adatu da rana ta girka musu Tuwo miyar Ugwu wanda yasha kayan had'i. Sai da ta yi wanka ta canja shiga sannan ta koma side d'in Anwar ta zauna jiranshi ya dawo su ci abinci. Sai bayan sallah Azahar ya dawo, ta taimaka mishi yayi wanka suka wuce Dinning cin Abinci.
Yana ganin tuwo ya fara mata signa irin 'kamar kinsan abunda nake so' d'innan. Dad'i taji sosai ta bud'e kulan miya ta zuba musu a wani karamin bowl. Da hannunta ta bashi a baki har santi yake yi yana had'awa da yatsunta in muguntar ta motsa.
Sai da ya koshi itama taci nata yana ta yabon girkin.
"Ki ajiye tuwon nan in akwai saura, gobe da safe ki mini d'umame dashi."
"To Habibi. An gama."
Bayan sun gama ta tattara kwanukan zuwa kitchen murna fal a ranta, in Adama ta fita a Sauce itama kuma ta fita a miyar ugwu. (Kar ki kushe abunda yake so don kishiyarki ce ta yi, ki tayashi yabawa in kuma kishin ya motsa baza ki iya ba, kawai ki yi murmushi ki kauda hankalinshi. Daga nan kema ki tashi tsaye kiyi wani abun da kika kware a kai. Note: Ban da munafurci, ban da hassada, ban da had'a guri, ke dai ki bi hanya tsaftatacciya wajen ganin kin fita matsayi a zuciyarsa. Ki kula.)

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now