25

5.4K 390 4
                                    


"Wani abun kuma take maka?" Anwar ya tambayeshi zuciyarsa na tafasa kamar ta k'one.
"Change da na samu shine matan baza su iso ba sai na fita office, kafin na dawo sun tattara sun tafi. Zan dawo in samu gidana kaca-kaca, Surayya kuma tana gado tana bacci cikin kwanciyar hankali, ban isa na tasheta ba coz da fad'a zamu k'are cewa na takura mata na hanata bacci. Na rasa gane zaman aurena take yi ko zaman kasuwancinta.
Cikin kwana biyun nan har na saba da hakan. Bata mini breakfast da lunch, sai dare take girki. So abunda yafi damuna guda d'aya ne; rashin bani hakk'ina da take yi. Idan zata k'i dafa mini abinci zan iya saya a waje, amma hak'kina fa? Matan banza take so in fara bi? Ko kuwa in zauna da cuta a jikina?" Musa ya k'arishe maganar da guntun kwalla a cikin idanunsa.
Anwar ne ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yana jin tsanar matan abokinshi a ransa. Da yana da iko babu abunda zai hanashi ya mata d'an banzan duka ko zata yi hankali.
"Wani mataki ka d'auka? Ko kuma duk abunda take mata ka zuba mata ido ne?"
"Ya kake so in yi? Na kai k'aranta gurin iyayenta wanda su kad'ai ne zasu taka mata birki, so kaga outcome d'in. Maimakon abu yayi sauk'I sai ma ta sake wasu sabin halaye na daban. Na mata nasiha, na mata fad'a har barazanar rabuwa da ita nayi naga bata damu ba. Haka Allah yaso ya k'addara rayuwata Anwar, babu abunda zanyi da ya wuce hakuri da addu'a. Wata rana sai labari Insha Allah."
Shiru suka yi kowa da abunda yake tunani. Anwar yace zai je ya mata magana ko zata nitsu, Musa yace ya barta kawai har ranar da tayi hankali da kanta, don yana tsoron a k'ara mata magana ta kunno da wasu sabbin rashin mutuncin.

Tun daga ranar Anwar ya k'ara kuncewa da lamarin mata. Adama jira take Anwar ya zo ya mata bayani ya aka yi haka ta faru? Amma sai ta ji shiru, tun tana saka rai har ta hakura ta cire tsammani. Saboda tasan daga ita har Shi babu soyayyan aure a ransu, amma idan suka fahimci juna zaman auren zai zo da sauk'I.

Shi kuwa a nasa 6angaren cewa yayi soyayyar da Musa da Surayya suka nunawa juna a waje shi ya jawo musu matsala a gidan aurensu, to sun gama cinye Love d'in a waje. Anwar ya d'auki alwashin ba zai nunawa Adama komai ba har sai ta shiga gidanshi.
Tun daga lokacin ya rage zuwa gidansu, kuma ko ya je tsakaninsa da ita gaisuwa. Delicious abincinta da yake ci ma ya daina, saboda da baya jimawa zai musu sallama ya tafi.
Duk halin da ake ciki Iyayensu sam basu lura ba, shirye-shiryen biki kawai suka saka a gaba cikin jindad'in k'ara had'ewan kan 'yayannasu.

Ana saura mako biyu biki Anwar ya je gidansu Admy yasa aka kirata.
A falon Babanta suka zauna, tun da ta gaisheshi suka yi shiru dukansu, kanta a k'asa tana wasa da zoben Azurfan da ke yatsanta, yayinda shi kuwa gogan wayarsa yake latsawa. K'aran TV ne ke tashi a hankali wanda Jamila 'yar rakiya ke kallon Cartoon a Tashar MBC3.
Gyaran murya ya fara kana ya ajiye wayar a gefensa, tattaro dukkan natsuwarsa yayi ya sauk'e ajiyar zuciya, ya zuba mata ido.
"Akwai abunda zaku yi ne?" Ya tambayeta.
Sai da ta d'auki 10secs kana ta bud'e baki.
"Na meye fa?" Ita ma ta mayar masa da tambaya.
Sarai ta gane in da ya dosa amma ta nuna bata gane ba don ya bata haushi ainun, idan ma ba sonta yake yi ba ai ya kamata ya fahimtar da ita kan abunda yake shirin faruwa.
Shiru suka yi dukkansu kowa zuciyarsa ba dad'I, don shi gani yake yi jan aji take masa, alamar raini na hanya.
"Wasu irin programs ake yi a bikin aure?'
Shiru tayi, sai da ya k'ara nanatawa sannan tace,
"Su walima da sauransu." Kanta a k'asa amma yanayin yanda take magana zai tabbatar maka fuskarta babu walwala.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now