20

6K 796 12
                                    


Sannu kawai ta musu tayi shigewarta falo, Adama kuwa murna ta koma ciki don ta d'auka Umman zata zauna a tsakar gidan ne.
Daga cikin d'akin Umma ta kwalawa Adama kira tace tazo ta kar6i kunun aya a kaiwa Anwar.
"Aunty bana shan kunun aya." Cewar Anwar lokacin da Adama ta mik'e zata je d'auko masa.
"Yau zaka fara sha, Adama zo ki kai mishi. Baka ta6a sha bane shiyasa baka san dad'insa ba."
Adama da ke murmushi kasa-kasa don murnan za'a tilastashi taje ta d'auko babban gora da glass cup ta ajiye masa a gabansa, kana ta kwashe plate d'in da yaci abinci ya kai gurin wanke-wanke.
"Ke kizo ki shanye kunun Ayan, sai in ce ni na sha." Ya fad'a a hankali yana mik'a mata bottle d'in.
"K'arya ba kyau Yaya Anwar, ko ka manta dukan da ka mini ranar da na maka k'aryan cewa nayi haddana?" Mak'e kafad'a tayi alamar A'a.
Hararan da ya saba aika mata ya watso mata had'e da jan tsuka.
Shi ba wai baya son kunun ayan bane, duk randa ya sha sai ya kwana biyu da ciwon mara ga wani feelings da zai dinga damunsa duk inda yaga budurwa tazo wucewa ta gabansa.
Shahada yayi kawai ya zuba a cup ya fara sha don yasan dole yau ayi sallan Asuba babu shi. In bai yi k'arya ba duk kunun ayan da yake sha baiji mai dad'I da gard'in wannan ba.
"Aunty kunun ayan nan yayi dad'I wallahi. Ai kawai ki fara sana'arsa." Ya fadawa Aunty Maijidda cikin zolaya.
Lek'owa tayi daga palour tana cewa,
"Wannan ba ni nayi ba, Adama ce tayi. Ai k'anwartaka ba dai iya sarrafa abinci ba."
Adama murmushi tayi ta sunkuyar da kai jin an yabeta.
"G10 shima za'a baki don ba wani dad'in da yayi. Abu duk kinbi kin maka sugar ga yana tsayamin a makwogaro." Cewar Anwar kasa-kasa yanda Umma baza ta ji ba.
"Uhm." Kawai tace dashi kanta a k'asa.
Dai-dai nan k'annenta suka dawo daga Islamiyya kowa sai ya tsugunna har k'asa ya gaishe da Anwar yana nodding musu kai cike da jin girma.
Yana gama shanye kunun ayansa ya musu sallama ya tafi don an fara kiran sallan maghrib.
Bayan fitanshi ne Umma ta kira Adama tana tambayanta ko ya fad'a mata wani abu?. Adama ta fad'a mata duk yanda suka yi Umma na murmushi, sannan tace.
"Ke dai abunda zan k'ara fad'a miki shine: kici gaba da kare mutuncinki a duk inda kika tsinci kanki, sannan rashin kunya ba naki bane."
"Insha Allahu Umma bazan ta6a yin abunda zaku yi Allah wadai dashi ba. Kuma nima ai bazan masa abunda zai sa ya ta6a lafiyar jikina ba." Adama ta fad'a da d'an murmushi a fuskarta. Umman ma murmushi tayi tana cewa a ranta, yaro-yaro ne, ko da yake bata ta6a soyayya ba shiyasa ta kasa gane wanda Anwar yake mata.
"Sannan ki daina wannan halinki na shigewa d'aki in yazo nan, gudunshi da kike yi zai sa ya cigaba da miki abunda bakya so, amma idan kina fitowa zaku saba har ya dawo yana miki dariya."
Adama dai 'Uhm" kawai tace don bata tunanin akwai ranar da Anwar zai kalleta da idon rahama ba na mugunta ba.

Anwar kuwa a ranar ya gane kurensa, don tunanin Adama yake tayi har ya jawo masa ciwon maran, sai da ya kwana biyu abun ya lafa, kana ya cigaba da zuwa gidan koyaushe da yamma da niyyar tunkaranta da abunda ke ranshi. Sai dai da yaje zai rasa 'yan kalmomin da ya haddace saboda wani irin kwarjini da take masa da cika ido, haka zai zauna ta saka masa daddad'an abincinta yaci ya tafi. Tashi salon soyayyar kenan.

BAYAN SATI BIYU
Anwar ne zaune saman motan Musa abokinshi na k'ut-da-k'ut, yayinda Musan ke tsaye yana jingina da motar.
"Tsoronta kake ji kenan?" Musa ya fad'a yana dariya bayan Anwar ya gama bashi labarin halin da yake ciki.
"Kai wani sa'in wawa ne, ya za'ayi inji tsoronta kuma? K'anwata ce fa, kawai bana son raini ne." Anwar ya bashi amsa yana daga faffad'an shoulder d'inshi.
"To ka hakura kawai don in dai raini kake gujewa kanka kar ka kuskura ka aureta."
"Ban gane ba." Anwar ya tambayi Musa cikin rashin fahimta.
Musa ya d'ale kan motan ya fuskanci Anwar da ya k'agu ya bashi amsa.
"Aboki cewa kayi baka son raini just akan furta cewa kana sonta, so ya kake tunani zaku yi rayuwar aure da wannan stupid thing d'in a ranka. Be realistic mana, imagine anyi auren, haka zaku cigaba da zama ko dai zaka canja? In har zaka canja after aure, to ka canja tun yanzu and win her heart, you are not her brother anymore, kai masoyi ne mai neman soyayyarta da yardarta. Keep girma da girman kai aside and be her friend."
Shiru suka yi Anwar na aikin tunani yayin da Musa ya ciro wayarsa daga aljihunshi yana buga game, lokaci-lokaci yana kallon abokin nashi ta wutsiyar ido yana murmushi, mamaki yake yi wai baya son raini, to ya za'ayi rayuwar auren? Sometimes Anwar jin kanshi yake yi kamar uban kowa, ya fada a ranshi.
Anwar kuwa yafi minti goma yana aikin tunanin maganar Musa, gaskiya lokaci yayi da zai sauk'e wannan girman kan ya ajiye gefe ya tunkari love of his life.
Murmushi yayi yana tuno had'uwarsu a jiya.
Ya je da yamma kamar kullum ya samu tana soya dankalin hausa, shine man gyad'an ya tsitto a hannunta, ta fasa ihun da yasa taku uku ya kaishi kitchen d'in cikin tashin hankali. Yana tambayarta me ya faru amma ina sai tsalle take yi rik'e da hannunta. Umma da ke falo itama ta fito a rud'e tana tambayar lafiya, Anwar yace shima bai sani ba kamar zai yi kuka, ji yake yi da yana da iko da ya dawo da abunda ya sata kukan jikinshi. Sai da Umma ta tsawata mata ta nitsu tana kukan a hankali ta fad'a musu abunda ya faru, ana dubawa aka ga ko tashi gurin bai yi ba, sai dai yayi jaa abunka da farar mace. Tsaki Umma ta ja, ta fita tana mita wai dole ta k'arisa suyan, Anwar ne ya kar6i suyan ya k'arisa yana mata sannu, har ranshi yaji haushin Umma da ta nuna halin ko-in-kula da Admynshi (sabon sunan da ya rad'a mata).
"Sannu Admy." Anwar ya fad'a a karo na ashirin da biyu tun shigowanshi kitchen d'in. Ita kuma sakaliyar tana gefe tana kumburo baki.

"Namiji a soyayya wawa ne, wani kuma soko ne...." Anwar ya dawo daga kogin tunanin da ya afka jiyo muryan Musa na wak'a.
"Na yarda, wanda aka kusa aurenshi kuma rak'umi ne ai." Dariya suka saka, kana suka cigaba da hiransu Musa na bashi shawara har dare yayi kowa yayi hanyar gidansu.

Don't forget to vote and comment please. Hakan shi zai k'ara min kwarin guiwa cigaba da kawo muku #MK akan lokaci. Thanks

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now