12

6.2K 471 5
                                    

1Month Later...

Shirye-shirye ake gudanarwa a kowanne sashe, kama daga gidansu Amarya da na Ango.
Abubuwa sun faru harda k'aura zuwa sabon gidansu.
Tangamemen gida ne na gani na fada wanda dama Anwar ya dad'e da fara ginawa.
Kana shigowa zaka fara arba da part din maigidan wanda upstair ne.
Palour biyu ne, na farkon wanda yake babban gaske wanda fad'in tsaruwanshi ma 6ata lokaci ne. A cikin palourn akwai d'akuna biyu sai stairs da zai haura dakai sama. Can saman ma falo ne babba amma bai kai na kasan ba. An k'awata shi shima ba laifi. Bedrooms 3 ne cikin palourn saman kowanne da kayan d'akinshi set, sai Study Room.
Ta Palour k'asa akwai k'ofa da zai sadaka da cikin gidan. Bari mu dawo baya.
Daga part din Maigida wanda yake gefen dama zaka hango wani dogon lungu mai flowers gefe da gefenshi. Ta nan zaka bi ya sadaka da cikin gida. Part uku ne daban-daban, wanda yanayin tsarinsu duk d'aya ne, palour babba wanda ya cinye saitin kujeru 2 da Dinning Area. Sai 3bedrooms da kitchen mai had'e da d'an store.
Ta bayan ginin d'akunan kuma Lambune da aka Shuka bishiyoyi har da abun marmari sai kuma Traditional Kitchen wanda yake d'an babba.
Ana washe garin zasu kauro Anwar ya kawo su Adama kan kowacce ta za6i inda ya mata. Adama ta za6i na farkon wanda yake ta hannun dama.
Nazifa kam ruwan ido tayi ta yi k'arshe ta za6i na tsakiyan, aka barwa Amarya na k'arshen gefen hagu.

*OYO STATE*

"Kudirat, kawo min hijabina. Fast fast."
"Which one sister?"
"Kowanne, just hijab."
Tana saka takalmi ta zura hijab d'in da kudirat ta kawo mata, ta dubi Mamanta wacce ke yanka ganyen Ugwu ta fara magana cikin Yarensu,
"Mama zan tafi, yau ma sai Aunty Mansura ta yi mini fad'a."
"A dawo lafiya, Allah ya tsareki daga ido mara kyau."
"Ameen Mama. Nagode."
A wajen gidansu ta tarar da Babanta cikin mutane da alama yau ma gardama yake rabawa. Har k'asa ta tsugunna tace mishi zata tafi. Hannu kawai ya d'aga mata don hankalinshi na kan matar dake magana tana kuka, ta dubi sauran mutanen tace,
"I greet you My Elders."
Da sauri ta bar gurin don bata son tayi latti.
Tana isa ta duba Agogon hannunta 4:37pm. Ajiyar zuciya ta sauk'e kana ta tura gate d'in ta shiga gidan.
Yan mata 5 ne zazzaune kan fararen kujerun roba, yayin da wata mace wacce zata yi kimanin 45yrs zaune itama kan kujera tana fuskantarsu da d'an stool a gabanta mai d'auke da wasu littafai.
Matar ce ta fara ganinta da yake ita ke fuskantar gate.
"Latti latti comer." Matar ta fad'a tana aikawa Sa'adatu harara.
A hankali ta isa gurinta ta durk'usa ta gaisheta.
"Aunty Mansura wasu friends d'ina suka kawo min visit, to basu tafi ba sai yanzu. Ayi hak'uri"
"Kije ki zauna. Punishment d'inki yau shine wanke toilet d'insu Abdul Hakem."
Dariya Sa'adatu ta yi har da toshe hanci. Sauran ma suka dara. Cikinsu ta shiga ta zauna kan sit d'inta, kana ta zuba idonta da hankalinta kan Aunty Mansura.
"Sa'adatu kafin ki zo munyi magana kan yanda ake wanke Undies d'in Ogah. So da yake ba wani dogon sharhi bane yasa kika yi missing. Zamu cigaba da next Babinmu in yaso in miki bayani daga baya."
Gyad'a kai sukayi suna sauraronta.
(Ni Maman Fateey daga gefe na zaro ido cikin mamaki, undies d'in ma sai an koya musu yanda za'a wanke??)
Kamar tasan me yake raina tacigaba da magana,
"Abunda yasa Matan Arewa ke tsoron kishi da mu kenan, saboda mu a kowanne fanni na tattalin miji da kuma biyayya mun kwarance babu inda Maigida zaiyi kuka da mu. Kuma bama saurin fushi, jiji da kai ko raina ga mazajenmu. Duk wani abu da muka san zai sasu farin ciki muna yinshi muddin bai kyaucewa shari'a ba. Mutumin da zai kawoki gidanshi, ya ciyar da ke, ya tufatar da ke, ya biya miki dukkan buk'atunki na yau da kullum ta hanyar guminshi, ya so ki, ya so 'yayanki da danginki, kuma Aljannarki na k'arkashin k'afarshi....".
Kallonsu Aunty Mansura tayi d'aya bayan d'aya tana jin d'adin yanda kowannensu ya tsumu da magananta kana taci gaba..
"... Shin wani mutum zaki daraja ki mutunta bayan Iyayenki in ba wannan bawan Allah ba?? Shin da me zaki saka masa akan tarin hidimominsa akanki?? Wani abu zaki masa ki nuna jin dad'inki gareshi? Wad'annan abubuwa sune: First HAKURI, LADABI DA BIYAYYA, SADAUKARWA, MUTUNTAWA, JURIYA DA TAIMAKO.
"Abu na biyu da zamu yi magana akai shine: GODIYA GA MIJI.
Ko daga tasowanku a gida kuna ganin example yanda iyayenku ke godiya ga Babanku. Namiji baya jin dad'in ya kawo abu na ci, sutura ko na amfanin gida ki kar6e babu godiya. Ba fa ke kika nemo masa kud'in ba. Yess duk da cewa hak'ki ne akansa ya sauke ana so ke kuma ki nuna masa jindad'inki ta hanyar masa godiya da kuma kalamai masu dad'I, fuskarki kuma koyaushe ta kasance cikin murmushi."
"Sa'adatu ke da Maryam ku fito ku gwada mana yanda akeyi."
Sa'adatu tayi sauri tace,
"Nine Miji."
"Noo, kece Mata. Maryam Miji." Cewar Anty Mansura.
Gwalo Maryam tayiwa Sa'adatu. Tayi d'an nisa da ita ta fara taku kamar Namiji har da wani fuskewa. Dariya sauran suka saka, Aunty Mansura ta kallesu da kattin idanunta suka k'unshe dariyar sunayi a hankali.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now