Update

3.8K 258 26
                                    

Nazifa ji tayi zuciyarta ta kara bugawa a karo na ba adadi tun zuwan Anwar gidansu a safiyar yau.
Jikinta babu kuzari ta mike a hankali tana takawa har ta fita tsakar gida inda ta iske Anwar kan tabarma yana u wayarsa ta zauna can nesa dashi Mamanta kuma ta shige falo ta basu guri. A karo na biyu ta kara gaishe shi,
     "Ina kwana?"
     "Lafiya." Ya fada ba tare da ya d'ago kai daga abunda yake yi ba.
     Shiru sukayi dukansu na yan dakikai, Nazifa da kanta ke kasa ta dago ido ta kalli Anwar da shi kuma wayarsa yake kallo fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sunkuyar da kanta tayi zuciyar ta na cigaba da lugude, dan ita kadai tasan me takeji a zuciyarta, tsoro, fargaba, zulumi da d'an digon fatan Anwar zuwa yayi domin ya maida ta d'akinta kamar yanda Abdallah yake hasashe.
     "Nasan bani da wata k'ima, daraja ko kuma idon da zan kalleka na baka hakurin abubuwan da nayi maka, da karya dokokinka da nayi a rayuwar aurenmu. Ba sai nayi tone-tone ba, ni karan kaina na san ban kyauta maka ba, matarka da 'yayanka ban yi kyakkyawan zama dasu ba, a wasu lokutan kuma na zaluncesu."
   Dago jajayen idanunta tayi da suka cika da hawaye kana suka fara zubowa ta cigaba.
     "Amma duk tarin laifukana zan nemi gafararka tunda Allah ya sa munyi ido hudu kai. Ka yafemin Baban Laila kamar yadda kake so Allah ya yafe maka, Adama da 'yayanta idan ka koma kace suma ina neman gafararsu."    
  Muryarta ne ya fara sarkewa ta rufe bakinta da hanunta hade da sunkuyar da kanta, jikinta na girgiza alamar kukan yaci karfinta.
     "Ki shirya zaki koma gidanki." Abunda kadai ya iya fada mata kenan ya tashi ya saka takalminsa sannan k'ara da cewa.
  "Kira min Abdallah." Yasa kai ya fice daga gidan.
     Nazifa gunki ta zama na sakwanni tsabar kad'uwa da furucin Anwar, shin kunnenta ya jiyo mata daidai kuwa? Anya ba aljani ne yayi siffar Anwar yazo yana wasa da hankalinta ba? Wai tukunna ma me yace? Kamar cewa yayi ta shirya ta koma gidanta!! Ita Nazifan zata koma gidan Anwar ko wata Nazifan yake nufi?

     Fitowar Abdallah daga falon mamanta shi yayi sanadin farkawarta daga duniyar tunanin da ta shige. A firgice ta dube shi tana k'okarin tuno sak'on da Anwar ya bata akan ta fad'a mishi.
     "Ashe yaya ya fada miki ki kirani baki fadamin ba gashi yana ta min fada a waya." Fita yayi waje ba tare da ya ji me zata ce masa ba dan gudun Kar ya had'u da wani fad'an.
  Bayan fitan Abdallah waje ya tarar da Anwar a cikin mota har ya tayar da ita yana k'okarin mata wuta, da sauri ya shiga motan suka bar unguwan zuwa gidan baffan Nazifa.

Baffa Tukur k'ani ne ga baban Nazifa kuma shi ya bada aurenta. Mutum ne mai wadata kuma ko da bayan mutuwar Yayansa yana taimakawa Iyalansa In buk'atar hakan ya tashi. Shine ya bada auren Nazifa ya kuma kawo musu kayan abinci da aka ci a biki. Ya kuma aikawa mamanta kud'i yace ta sayawa Nazifa kayan d'aki. A kofar gidan sukayi parking Anwar ya aika Abdallah cikin gidan a musu iso.
  Bayan Abdallah ya fito daga gidan Anwar ya shiga, a falp ya Iske Baffa Tukur a zaune. Bayan sun gaisa Anwar ya kara dukar da kanshi yana cewa.
  "Baffa nazo ne don na koma da Nazifa gidana."
  "Masha Allah, Masha Allah. Hakan yayi kyau. Bayan ta dawo mai d'akina ke fad'amin Nazifa ta dawo gida, sannan daga baya mamanta tazo nan take fad'amin wai aure ya mutu. Abu bai yi dad'i ba sam, Kunyi saki d'aya ko?"
  Gyad'a Kai Anwar yayi kansa na k'asa kamar mara gaskiya.
  "Eh, hakane Baffa. Abubuwa da yawa sun faru sai daga baya nagane harda laifina, ina mai baku hakurin abunda na aikata cikin fushi. In Allah ya yarda hakan bazai kara faruwa ba, sharrin shaidan ne da kuma saurin yanke hukunci cikin fushi." Anwar ya karashe, yana kara dukar da kansa alamar bada hak'uri.
  "Kaddara bata wuce fata Mallam Anwar, haka Allah ya k'addara muku zai faru. Nan gaba sai ayi dogon nazari da kuma sanya hakuri a zuciya kafin a yanke hukuci, ban ji dad'in abun ba sam."
Sosai Baffa Tukur ya masa fad'a had'e da nasiha shi kuwa Anwar kansa na k'asa yana gyada kai yana k'ara bada hak'uri, daga baya sukayi sallama ya fito daga gidan.
  A waje ya iske Abdallah suka k'arasa zuwa gidajen baffanun Nazifa. Su ma nasihar suka mishi sosai kana ya bada hak'uri tare da alkwarin k'ara hak'uri a zamansu. Basu samu suka gama ba sai kusan sha daya saura na hantsi.
  Komawa gidansu Nazifa sukayi suka samu har ta gama shirya kayanta tsaf. Zaune a falo Nazifa ce da mamanta wacce take mata fad'a sosai kan zaman aure da kuma hakuri da biyayya ga miji. A haka Abdallah ya samesu ya yiwa maman magana kan cewa Anwar na son yi mata sallama. A tsakar gida ta iske shi, ya kara bada hakuri, ita ma ta k'ara nasiharta sannan ya fito da bandir biyu na dari biyar-biyar ya mika mata. Da kyar ta amsa kana ta saka mishi albarka ta koma falon in da tabar Nazifa zaune tun shigowansu Anwar.
  "Nazifa ki rike mijinki, ki kuma koyi hakuri da abokan zamanki. Abunda yafaru ya isheki ishara kan rayuwa, yau kece cikin daula gobe kuma in Allah yaso sai ya maisheki cikin takauci. Ke ba yarinya bace, kin san me kyau kin san marar kyau, ki zaman abun koyi ga kannenki tunda gasu nan sun gama tasowa miji na fitowa za'a aurar dasu. Ki rik'e mijinki Nazifi sannan ki zauna a gidanki lafiya babu ruwanki da tashin hankali ko fitina. Allah ya miki albarka kuma Allah kawar da sharrin shaid'an tsakaninku ya kuma kyautata zaman ku." Ameen Ameen kawai Nazifa ke fad'a tana jin wani farin ciki mara misaltuwa na ratsa zuciyarta. A ranar da ta bar gidan Anwar In aka ce mata zata koma gidanshi zata k'aryata. Amma wai yau gashi nan zata koma gidan da take tunanin ta barshi kenan har abada.
Wani farin cikine ya k'ara lullu6eta da ta tuna cewa da Sa'adatu kad'ai zata yi kishi dalili kuwa Adama bata ma Kai a kirata da mace ba balle har a yi kishi da ita. A ranta kuma ta kudurta in biyayya ne tak'amar Matan K'abilu to itama zata ara ta yafawa kanta ko da zuciyarta bata so ba, idan kissa da kisisina ce makaminsu itama zata gwada. Wani gefe na zuciyarta kuma na cike da fargaban lahanin da ta yiwa kanta, tayi nadamar lalata abunta, abun alfaharin kowacce d'iya mace. Ta yi alk'awarin fantsamawa neman magani har sai ta warke daga cutar da ya dad'e yana addabarta. Kuma tayi alkawarin rama abunda Hajja Uwa ta mata komin Daren dad'ewa. Daga nan ne zata nunawa Sa'adatu cewa Mijinta Anwar nata ne ita d'aya, gidan Anwar nata ne ita kad'ai sannan ko da Kirsa Sai ta dawo da soyayyarta da kimarta a gurinshi, Alkawari ta d'auka sai ta sato zuciyarshi. Wani murmushin mugunta tayi tuno da irin shigo shigo ba zurfin da zata musu har hakanta ya Cimma ruwa. Ai ba'a ce kishi babu kyau ba, to itama zata yi amfani da wannan damar ta mallake mijinta ya dawo sai abunda ta fad'a za'ayi a gidan. Nazifa Kwata-kwata bata ma tunanin  Adama domin bata ko cikin lissafinta. Ni Maman Fateey nace akwai aiki Jaja jurr a gaba domin zaman kishi yanzu za'a fara domin babu abunda aka yi. 

Wahoho
K'ak'ak'arak'ak'a
Shin ya kuke ganin Haduwar Nazifa da Adama zai kasance? Shin wannan zama na fahimtar juna tsakanin Adama da Sa'adatu zai d'ore kuwa? Shin Anwar har cikin zuciyarsa yake son dawo da Nazifa? Shin wani irin zaman kishi za'ayi a wannan gida na Anwar a daidai lokacin da kowacce matarsa ta tashi hani'an ganin ta zama tauraruwarsa? Shin Nazifa zata cimma d'aruruwan burikanta kuwa?
Domin jin amsoshin dukkan tambayanku Zaku samu a MATAR KABILA part 2 wanda an gama rubutawa a yanzu zaku samu complete.
Domin samun cigaban wannan labari na zaman kishi tsakanin matan Anwar sai ku turo N200 ta Bank (5139579011 fcmb Suwaiba Muhammad)
Zaku iya tuntubata ta numberna 09023713064 a Telegram ko Whatsapp domin nuna shaidarku ta biyan kudi ni kuma in tura muku Insha Allah.

Ina mata 'yan kasuwa? Masu sari ko siya da siyarwa? Ga dama ta samu💃🏻💃🏻 momeekareto collection kamfani ne da ke kawo kaya daga qasashe daban2 masu kyau da inganci a farashi me rahusa👌🏼😍 ku shiga link dinnan na group https://chat.whatsapp.com/J561UaMK20rJ5hKY9bHS3

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now